Sorry for Latt update sis, insha Allah nafara muku posting har saina kare Love u all....12
Kuka sosai tasakawa Maman ta. Feedoh is ok amma meya hadaku da yace haka me kikace masa?, Mama bance masa komi bafa ya zanyi yanxu Ina sonsa yatafi.
Kanta Maman ya shafo cikin taushin murya ta furta Feedoh ki nutsu indai yana sonki tsakani da Allah komi kikai masa a yanzu bazai guje kiba.
Nasan laifin kine amma kibashi lokaci zai dawo kiyita addua kuma dan itace jigo a rayuwar yanzu. Idan zabin kine wallahi Allah saiya dawo miki dashi, Idan kuma ba rabon ki bane sai Allah yakamiki wani daban.
Cikin kuka Feedoh tace Mama wallahi rabo nane kidena kawo kaddara a yanzu yana sona yasan wace ni....Nima nasan waye shi wallahi muna son juna.
Naji nadena fada yanzu ki tashi anyi kira saikiyi sallah ki kirashi a waya.
Tashi Feedoh tayi ta hau sama inda tai alwala kana ta hau kan praying mat tafara sallahr ta. Ta jima tana addua kafin ta shafa. Tunani tafara wai Malam Fiqh shine Ahmad how comes?, sosai Tafara tuno yanayin kallon sa a gareta da kuma yadda yake magana haka Ahmad yake komai saida ya dawo mata a ka, dan murmushi tayi tace koda almajiri ne kai I love u Only can't do without u....I can't break this pure love da muka gina kadawo inason ka a haka.
Wayar ta ta dauka inda tai dialing number tasa amma harta katse bai daga ba, kira tacigaba da yi amma still ba ai picking ba. OmG Ahmad kada kamin haka...dayan sim nasa tafara kira ko Allah zaisa ya dauka.
A bangaren Malam Fiqh kam yana fita gidan sa ya zarce ko parking baigama ba ya fito da sauri saikan gado haki yake yana ajiyar zuciya dama nasan bazaki soni ba, mesa zuciya bakimun adalci ba kinso wadda zata soni, gashi yanzu nafada tarkon wadda ta tsaneni ma...,Ya ubangiji ka kamin mafita Feedoh kisoni wallahi zanbaki duk dreams din da kikeyi duk yadda kike so na zama zan zama.
Yana cikin wannan tunanin yajiyo karan wayar sa, Dubawa yai hannun sa yasaka ya shafi sunan ta kafin ya furta I cant answer ur call Feedoh Ina tsoran jin kalaman da zaki gayan zuciyata bazata jure ba nasan baki sona basaikin bugo kin gayan ba.
Ganin baa dena kiran ba yasaka shi kashe wayar ma baki daya.
Inalilllahi shikenan tafaru ta kare yai zuciya inda take ko motsi kasa yi tayi anan ta kwanta har baccin wahala yatafi da ita mai cike da mafarkai kala kala.
Shima hakan ce tafaru bayan ya idar da sallah abinci dai babu Wanda ya saurara a ranar kowa zuciya ba dadi.
Su Auta fa sunata zuba idanun ganin Faeedoh online amma shiru har 12, zahra bukar ce tace ku Feedoh fa maybe akwai matsala amma bata kin hawa na kirata a kashe kuma....jiki da jini Jabo ce tayi wannan maganar da haka kowa ya sauka.
To fa su Feedoh anshiga taskun love gaba daya ta zama wata kalar tausayi Maman ta kwarai ta dage mata da nasiha dakuma bata adduoi akan komai yai zafi maganin sa Allah.
Malam Fiqh shima abin tausayi kullum idanun sa sunakan pics da previous chat din da sukai da feedoh wani yai murmushi wani kuma zuciyar sa tayi zafi.
Gashi baisan wa zai tunkara da wannan zancen ba....Abban sa hankalin sa ne sai tashi bare umman sa da bata son abinda zai tabamata Ahmad din ta.
Shirun dai shiyafi alkhairi hakan yai kuwa gashi ko online ma yadena ganin ta kenan canja number tayi saboda shi shiyasa ya kara shiga wani hali, makarantar ma kwanan sa biyu bai iya lekawa ba.
Yau kam tun Safe Feedoh take zaune a kan dining ta tasa abinci a gaba amma ko loma daya takasa kaiwa bakin ta. Malam Fiqh kawai take tunawa da komai nasa akan ta da kuma wayar da suke matsayin Ahmad har kawo ranar da yazo mata a fili.
Bataji shigowar Kowa ba sai jin hannu tayi a kafadar ta cikin slow ta dago kanta zahra ce...murmushi suka sakarwa juna.
Hmm Feedoh me yai zafi haka najima da shigowa amma ko alamun mutum bakiji ba saboda tunanin wani abu komai yai zafi maganin sa Allah what's the problem Qawata?.
Zahra dama inason kiran ki muyi magana dake, Ina Ahmad danace miki zaizo?, uhm. sai akai Yaya?, ba kowa bane face Malam Fiqh nan ta zayyanomata komai har tafiyar sa....zahra dai dan dariya tayi kafin tace ikon Allah amma abin da mamaki kodayake dama jikina yaban Malam Fiqh yana sonki but am not expected zaizo da haka. Feedoh idan har kin aure shi kinyi saa a rayuwa fatan Allah ya daidaita amma mene mafita yanzu?.
Kafin suce wani abu wayar Feedoh tafara tsiwa tana dubawa taga KITO ne cikin sayi ta amsa masa ba kamar da da take masa ihu aka ba.
Aa yammata yanajiki haka jikin ko garin?, Ya KITO ba labari Ina Ahmad danake baka labari?, naji mene?, Ya tafi ya barni kuma Ina son sa. Don't understand? KITO yace mata a bangaren sa, kamar ke ace yatafi kodai wani abu ya hadaku?, Ya KITO daga nace fa zanyi shawara shine yatafi yace dama yasan ba sonsa zan ba kuma wallahi Ina son sa.
Don't worry sis I will come insha Allah I will settle everything don't mind ur self u have me fa kuma u know am not lazy I will do all my best dan na dawo da sweetheart din sis dina.
But don't forget nima zahra a taimakan?, don't mind Ya KITO gata kusa ma wallahi nabaka ita kazo sai ayi maganar, ok amma kicire komai kisaki ranki yammatan Malam Fiqh...,dariya sukai tare kafin sukaci gaba da hiran su da zahra har Maman ta tafito takaramata fada sosai da nasiha.Auta ce

ČTEŠ
KALLON KITSE.
Historická literaturaStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...