KALLON KITSE. 6

1.6K 111 2
                                    

Feedoh dai tsabar haushi ko  online bata koma ba, tana zaune saidai ta tuno Ahmad Insta tsaki kawai take
   Shikuma daga can yana zaune dariya kamar ta kulle masa ciki, yanda yaga tayi yasan tanacan tana masifa ko ana bada labari
   Wayar sa ya janyo wadda ya ajiye ta, dialling number nata yayi, tana toilet tajiyo ringing d'in tazata Kwaiseh ce amma saitaga new number
   "Hello"
  "Hy ya kike Yar ficika shine kika gudu koh?
  Bangane ba a ina na gudu?, waye kai
   Daga d'aya b'angaren yace Ahmad ne, ai na d'auki number naki, naga kin sakata kekuma daga magana idan ya b'atawa yammatan rai tayi hak'uri bazan Kuma ba
   Baki ta zob'aro tace ai Kaine daga had'uwa sai maganar wani Akhbari ko Ishmawee, hala kana koyarwa ne?
  Eh inayi menene?
   Ba komai, amma banga alama kana teaching ba, tunda some of Malaman Islamiyya basa wani karatu few ne cikin su, amma kai gaka handsome Indai har pics naka kake sawa
   Gaka da ilimin ka da wayewa abin dad'i, ga ilimin addini da kake dashi, kaga kuwa yaushe zaka tsaya b'ata wa kanka lokaci kana koyarwa
   Huum, haka kuke gani, bamuda aikin yi tunda muna zuwa koyardaku?, kuma kuna bada kud'in wata ko term, amma baku tunanin da safe maimukeyi
   Munada abinyi taimaka muku muke, dariya tai tace nidai ban yadda kai Malami bane, Idan kai malamine ya akayi kake chat, ai su daga gafaka sai littafi
   Dariya sosai tabashi, Lallai kenan ke baki iya auren malami?
   Waih rufan asiri, Deedoh batama kula samari karatuna shine saurayi na
   A nan suka shan take sunata hira muryarsa mai dad'i, ga wani slight English dayake zubawa, kusan raina nata English d'in tayi amma bata nuna masa ba
    Basu fargaba saida sukaji kiran Sallah sannan sukai sallama, amma Ji sukai dama suyita hira
   Ido Deedoh tazaro ganin 2 hours suna magana, Lallai wannan to Waye shi?
  Batada ansa Illa,kwanciya da tayi, tana tuna muryarsa tayimata kama da ta MALAMIN FIQH amma wannan yes ne, shikuma NO ne
    Wasa wasa cikin kwana 2 sunyi sabo sosai, baiqara mata maganar wani FIQHU ba, labarai suke akan Korean series da Indian film yawancin duk film din data gani yagani, wani ma Ita a season 2 or 3 take amma shi yafice nan
    Sai hira akan wasu garuruwa da k'asashe, sosai sabo yashiga tsakanin su wanda Ita Feedoh batasan lokacin da sabon ya shiga ba
   Yau da akwai Islamiyya hakan yasaka ta duk wani iri, ga ZAHRA bata nan taje J TOWN Anee kuma ta dena zuwa saboda Exam
    2:00 tayi shirinta yadda tasaba, ta d'akko wayarta da Jakarta, tana cikin fesa turare taji vibrating nata, dakatawa tai ta ciro wayar
   A haf tasan shine, hakan yasa tai murmushi
"Hello yammatana doguwa hallitar Allah Yar ficika"
  Dariya tai tace kaganka, ya kike to feel fyn munata shirin makaranta
   Wacce makaranta kuma?, Islamiyya mana, ok time yayi fa. eh yayi
   Kuma yau Malam Ahmad garemu first gashi namasa laifi Kuma banson duka ko d'aya
   Ah aikam Idan kinyi laifi dole adakeki, dama nizan zaneki, naga ya zakiyi
   Lol Allah ni banson duka, amma fa shi baya duka Idan anyi laifi ma ba kullum yake dukaba gayen yanada kirki
   Dariya ya kyakyale da ita, yace ashe harda gayu cikin malaman?, haba dai shine kawai fa, shima ina ganin diploma ko NCE gareshi, shiyasa yake d'an wani ji da kai, amma wani gayu
   Yanada kyau sosai, ga fatarsa mai haske da d'an bakinsa abinda yasa zaka k'ara ganin kyau nasa tabon Sallah dayake dashi
  Lallai amma kunmasa kallon k'urilla, irin zano suffarsa haka?
  Haba dai kawai kasan Idan ka kalli mutum zaka Iya fad'i, kai bara nabarki haka kada ya dokarmun ke
  Huum ai Idan ya dakan kaima yaja maka, dan yaji zanyi nadena kula kowa tunda sunan ku d'aya
  Lalala to zanyi addu'a kada Allah yasa ya dokeki, Ki kamun yaji ai ba kanta ina zan ringa sauraron golden voice naki
   Maza ayi shiri atafi, agaidamun shi, kice mijinki na gaidashi
   Kai miji Kuma, eh mana, tsaya Malam bangane ba?
  A'a kije kawai mayi magana anjima, kafin tace wani abu ya datse layin shima da sauri ya fito ya hau machine nasa ya tafi yau shi kansa yaso yayi latt.

@ut@r h@jiy@

KALLON KITSE. Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang