KALLON KITSE. 10

1.4K 104 1
                                    

Shigar Deedoh gida batafi da minti goma ba, taje wajan Maman ta, zama tai a hankali tace mama ya gida?, lafiya lou Yar ficika ya karatun?

Lafiya lou Wallahi, mama dama wata magana nakeson gaya miki, Allah yasa kada kik'i.
Huum inaji indai har maganar mai amfanice maizaihana na karb'eta da hannu biyu. Tabbas kuwa mama Allah yasa maganar saurayi zatayi muma musha biki, dariya tai Mama tace ikon Allah saikace akanka take, banason gulma da sa Ido kaji.
Yaya Abdallah ne yace Mama Wallahi kekike sangartata, kalli wasu kaya datasa saikace gidan ta, kibari kije gidan ki saiki yi.
Zauna Malam bamuson magana, inajin ki Auta ta, kanta ta sunkuyar tafara magana a hankali, Ya Abdallah kuwa dariya ya kwashe da ita yace tab Deedoh da kunya Yau, lallai maganar nan taci gari, ja muje yammata nasan maganar saurayi ce.
Allah ya kyauta maka, ina ruwan ka ma, Feedoh ce tace Mama kyale shi, dama wani ne muka had'u da shi a Insta nan ta labartamata yadda sukayi dashi harkawo yanzu.
Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace, ikon Allah, bazance komai ba, Illa ki kare mutuncin ki da harshen ki, Kuma Allah ya kawo shi lafiya muna jiran sa, amma kina ganin bashida matsala?
Ya Abdallah ne yace, Mama tunda tace yace zaizo, abarshi yazo sai ayi tambaya a kansa, da komai nasa sanin halinsa kuwa, ko a zahiri yake Wallahi sanin ainihin halin mu sai mu kanmu.
Ba tangaran bane mu, ko kwarya da za'a kwankwansa aji nagartar mu, saidai muyi fatan Allah yasa nagari ne.
Ameen suka ce, nan sukai addu'a, sannan suka tashi. Waya tamasa taga yamasa yadda sukai da yayunta da Mamanta, murna fal cikin sa, da suka nuna murna su, akan haka, fargabarsa d'aya Allah yasa Idan ta ganshi bazata gujemasa ba.
Haka kwanaki suka ja, tsakanin ta da MALAMIN FIQH Ahmad kuwa, daga gaisuwa shikenan, amma wani lokacin saitaji tanson kallon sa, Malam Ahmad yayi ta ko'ina matsalan bazai Iya love ba, batace sai Don zata aura ba, amma Iya soyayya sai d'an boko, MALAMIN ISLAMIYYA ina, su sai k'ala rasulu, d'an kallon love enan da kalamai masu zafi basu Iya ba, itakam tanason love.
Da ace Malam Ahmad ba MALAMIN ISLAMIYYA bane, tabbas taga mijin aure, bakinsa mai kyau, amma Ita sometimes she hv a confection a kansa, skin nasa so soft, ga lips nasa maikyau pink blue foot nasa abin kallo ne garai garai 'yan yatsun hannun sa dogwaye, Wallahi da ace ba ustaz bane yayi 100%, amma ya b'aro shid'in ya sayyadi ne.
Lokuta da dama tana tunanin haka, kwanaki mafarkin sa tai tayi, da qyar ta yakice shiyasa batason kallon sa badan wai tanajin haushin sa ba ko wani abu, No takan shiga wani yanayi da shagala da tunanin sa, shiyasa batason kallon sa.
  ******** Bayan kwana biyu
                                  *********
Tun safe Deedoh akasaka house girls da masu bawa flowers ruwa suyi gyaran gida, Ita kanta saidata had'a alkama, kwai, nonon rak'umi da bagaruwa ta had'a ta gyara jikinta, ga wani turare na k'amshi datake sawa amma nayau yafi na ko yaushe.
Kayanta tun safen tayumusi turaren wuta aka fesa turare aka ajiye, komai yayi ready.
Abincin cika da snacks da had'in lemuka itada ZAHRA Bukar suke tayi, ZAHRA sai dariya take mata farin shigar love, yaudai za'aga real face na Ahmad Insta.
Waya yamata yakusa shigowa gari, nan fa murnarta ta k'aru, amma wani sashen na zuciyar ta yana mata wani iri tunanin MALAMIN FIQH take yi, da yadda kwanaki yai magana da English, sosai yake burgeta amma..... tsaki tai, tacigaba da ayyukanta.
Fad'uwar gaba, taji lokacin daya ke sanar da ita, cewar ya shigo gari nan da one hour zata jishi zaije wajan wani abokin sa. Sukuku tai harta fara tunanin dama batace yazo ba.
ZAHRA ce mai kwantar mata da hankali, tace ke insha Allah mijin aure ne, ba wasa alamransa insha Allah, ai daga gani ma zaiyi hankali.
Haka suka gama, wanka tai da sauri kwalliya ma kasayi tai, powder kawai tasaka kana ta d'akko super purple da takalmi da mayafi, ga sark'arta mai duwatsu purple, tai kyau matuk'a, ga k'amshi kota ina, lokacin ZAHRA ta tafi shiyasa Ita kad'ai takama hanya zuwa qasa.
   Waya yamata yazo fa, yana cikin compound nasu, Al ready dama taimasa kwatance, zuciyar tace taji ta kwace sak muryar Malam Ahmad, saidata dad'e sannan ta mik'e tsaye, idi taiwa waya akan yashiga da bak'on ta living room.
Gyara d'aurin d'ankwalinta tai, sannan taiwa Mama sallama ta fita.
A hankali ta qarasa hartaje saitin k'ofar shiga ciki, turaren Malam Ahmad taji, maisata nishad'i Rakaan na company'n Swiss Arabian, iska ta furzar taceto ko duk masu sunan Ahmad suna son wannan turaren? amma Kuma..... to ai turare bana mutum d'aya bane, haka tasakai ta shiga
  Yana kan kujera a zaune ya hakimce k'ananun kaya yasaka ga kansa yasha gyara agogon sa Rolex d'an yayi, ga azurfa mai adon blue dutse a d'anyatsansa, yana walwali. kansa a qasa, wayrsa yake dubawa, zuciyarsa kam fal take da fargabar ya Deedoh zata karb'eshi?
itama turaren tane Royally blue yaimasa sallama kafin nan siririyar muryar ta ta biyo baya.
A hankali takai kallon ta kansa shima daidai nan ya d'ago, Ido ta bud'e ina.... k'ara rife Ido tai ta bud'e still shine amma a tsaye.
Ihu tasaka ta juya a guje zata fita, kafin takai k'arshen wajan yayi ta maza yasaka k'afar sa ya tura k'ofar ta b'ame b'am.

@ut@r h@jiy@

KALLON KITSE. حيث تعيش القصص. اكتشف الآن