Bakinta sake tana al'ajabin wannan mutumin lallai wai matar sa kwafa tai, tamaida wayarta jaka ta fito downstairs taga Mama sallama tamata akan ta tafi makaranta
Allah ya kiyaye hanya, ki kula Autar mama.Tom Mama saina dawo
Yadda take tafiyar ta kullum haka take yanzu ma haka, tanayi tana tuno Ahmad Insta da muryar sa afili tace ka had'u.
Karyar kwanarta keda wuya wadda zata sadaka da makarantar taga Malaman abakin gate kowa sa k'atuwar bulala a hannu cikinta ne ya d'uri ruwa ita ko bulala batason gani bare Kuma ace ta hau jikinta.
Agogon hannun ta ta duba, sauran 4 minutes afara taran makara ai da sauri ta saita tafiyar ta tafara da sauri amma ta maze irin d'in nan, haka ta shiga cikin makaranta hankalinta bai kwanta ba saidatajita a aji, sannan tasaki ajiyar zuciya.
Ko zama batai ba, akafara Deedoh yau zakushata shine kika gudu ran nan?, Ido ta zaro tace banson gulma yama manta inajin, ku nama gudu haka kawai za'arunga mun tambaya kamar naci bashi ko a kotu sai haka, NI nama kusa daina zuwa aure zanyi na huta.
Dariya suka saka amma a hankali, saboda tun lokacin data fara magana yana tsaye Ita bata ganshi ba.
In baku labari na had'u da wani shima, nan ta zayyonomusu abinda yace, ku amma guy d'in ya had'u irin na aure ne.
Mukuma ba irin na aure ba koh?, da sauri ta juyo a tsaye yake da bulala a hannun sa, Malam ina yini" lafiya lou magananniya.
Guri tasamu ta zauna tace yau zakasha tambaya Wallahi, muje zuwa dai. Shi kallon ta yake yi yana murmushi shi kad'ai yasan mai yake saqawa a zuciyar sa.
Yauwa yau ba karatu zamuyi ba, filin tambaya da amsa saboda haka kowacce tai tambayarta zan amsamata daidai gwargwado, kun gane? Eh su kace
Haka kowacce tafara tambaya akan karatun su, wata akan abinda yashige mata gaba na al'amra daidai yana amsawa
Malam inada tambaya? Deedoh ce tai magana, mik'ewa tai tace Malam ya ake wankan janaba ni bantaba yi ba, Kuma naji kusan kullum saikace Gusulul Janabati, shiyasa nakeson sani kuma inaso nafara yi tunda gaskiya bantaba yiba?
Ido ya zaro yace Firdausi ai bawai ina nufin kuyi ba, a'a ku iya kafin ta same ku, kuma kusan menene yake kawota Idan kayi d'aya daga cikin abinda yake wajabta wankan ta dole kayi.
To Malam mene yake wajabta wankan, Kuma meyasa sai nan gaba zamuyi?
Tana magana idonta a k'asa, shi mamaki take bashi lallai yarinyar nan, zaiyi maganin ta
Bayani yafara mata, yace Yanzu danaji kince gayen ya had'u, idan azuciyar ki kikaci gaba da kiyasta hallitarsa dole zakiji wani abu to anan ma wataqil wanka yakamaki tsarki dai zakiyi...amma fa idan abin yai yawa zakiyi wanka dan abinda zai fito daga jikin ki yafi k'arfin tsarki.
Cigaba yayi Tuntana ji harta dawo kwanyarta tafara rufewa yana gani tafara rife Ido shikuma yak'i yadena jin ba alamar tsayawa tace Malam nafa gane ka barshi haka dan Allah .
Ai bawaike nakewa ba duka yan ajin, suma su fuskanci me ake nufi da haka, to ai sun fuskanta
Shiru yayi dariyarsa yasha azuciyar sa ganin tamakasa d'aga Ido ta dubeshi
Yana sane yace, yan aji kuna raina malaman Islamiyya bansan mai yasaba, kodan bamiyun swaga kuma bama hawa motoci, bamu Iya turanci ba, ba yan gayu bane mu, shiyasa ma bakwa son kuji wani yace yana sonku?
Ai arziqi na Allah ne, kuma bayan haka, itama wayewa haka, da yamma kawai muke zuwa bakuyin tunanin da safe muna wani abin plx ku canja, wato ku sai gayu sune mutane?
Nan yai musu nasiha afakaice kuma da Deedoh yake.
Nagama sauran ke Firdausi meyasa kika gudu daga tambaya?
Ido tafara mutsikawa tace Malam fitsari nakeji lokacin fa, kuma Kuma......
Kuma me?, ai saina zaneki Yau, rashin kunya koh?, Wallahi a'a ancema kada ka dakeni Wallahi tana magana idonta taf kwalla. Yar gata wayace kada na dakeki? Ya Ahmad mana.
Waye shi? duka ya tabbata akan ki kuwa. bulala uku ya tsulamata masu zafi yanayi yana dariya aikam tajita a jikin ta.
Kuka tasaka tana kare jikinta har ya gama, tunda tasa kanta a cinya bata d'ago ba harya fita hak'uri akafara bata haba Yar ficika kiyi haquri mana daga wannan d'an dukan.@ut@r h@jiy@
YOU ARE READING
KALLON KITSE.
Historical FictionStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...