FULANIN BIRNI

1.8K 79 0
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE6⃣

Allah yajarabe laila da ciyon Mara saboda haka kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
   Kabiru kuwa tuni yacire rai da haihuwa yafi alak'anta shi dacewa shine da matsalar , ana haka Aisha tasamu ciki bata gayawa kowa ba seda yayi wata takwas tasame alh kabir tamishi bayani bai wani murna ba acewarshi inda sauran sukaje wannan ma can zaije.
     Itake kwantar mishi da hankali da bashi baki harya d'an nutsu suka duk'ufa da addua , Alhamdulillah tahaife d'anta namiji kyakkyawa kamar sauran aka rad'a mishi Yusuf.
      Yusuf yatashi hannun laila tana mugun ji dashi akanshi dakowa tana samun matsala ko uwar data haifeshi bata isa ba haka suke ta rigima da ita. 
      Yusuf yaga gata kala_ kala kowa sonshi yake baiwani samu kunyar d'an fari ba course yazo lokacin da ake bukatar shi.
      Yanada shekara biyu aka mishi kanne mata biyu twince zokuga murna gun alh kabir , Yusuf gabadai Yakoma hannun laila daga yaye shi Aisha tabada shi bak'aramun dadi taji ba hakama maigidanta hakan datayi yak'ara mata daraja da k'ima sosai a idon mijinta. 
     Wasu daga danginta sukan ga wautan ta wasu kuma suce tayi namijin k'ok'ari duba da yanda aka dad'e ana nema.

    Tawaye nada shekara daya laila tasamu ciki nanma anyi murna sosai Yusuf zai samu k'ani , haka tasankad'o babynta sak ita buzuwa , daga nan kuma bawanda yak'ara haihuwa acikinsu sosai Yusuf yakeji da k'anwarshi fatim ba abinda keraba shi da ita inba skull ba lokacin da zaije boarding skull ansha fama sosai hatta twins kuka suke soyayya mai k'arfi sukewa junan su.
    Haka yagama bafarawa institute ya wuce Malaysia karatu inda yake karantar sociology.
    Har yusuf ya girma  bashida uwa kamar laila dashi kad'ai take fira ko "yarta fatim bata samun walwala kamar yanda Yusuf yake samu.
daga bisani Yusuf yafahim ci mahaifiyar shi ta usuli , amma duk da haka yafi jin laila aranshi , duk yanda yake zaune tareda ummanshi baya iya sakewa itama kuwa bata wani sakewa dashi.
    Sosai siblings d'in shi ke tsoronshi fiyeda mahaifinsu duk da bawani zama suke dashi ba, indai Yusuf yabada order tabbas kowa zai yi obey ko anaso ko ba'a so , usaina da hasana suna state university suna karatun science.   

      Inda fatim ke polytechnic tana karantar low. 
    Yusuf yanada zuciya sosai kamar lion yake akwaishi da miskilanci ga rashin son jama'a, abokinshi d'aya faruk wanda suke tun childhood d'insu shima d'in dan taso tazo d'aya ne suke tare.
Mahaifin faruk d'an siyasa ne saboda haka dukan su da kud'in su faruk ya karanci likitanci bangaren mata saboda haka tin dawowar shi Malaysia dadynshi ya mallaka mishi babbar asibiti wadda tashafe bangaren mata kawai.
      Kowaci matsala ta mace indai taga Dr faruk tokuwa anwarke da bi'iznin Allah.
      Amira yar k'anwar laila ce hasalima agidan tasan shi daga nan kuma tafada tarkon sonshi.
    Amira 'yar baban gida ce tana cikin gata da soyayyar iyaye both kasancewarta mace tafarko agidan kuma ta k'arshe sedai maza dake binta su uku.
   Laila na matuk'ar sha'awar auren Yusuf da Smira sai dai bai bata fuskar hakan ba ita kanta tsoronshi take duk masifarta.
    Yakan yiwa kowa biyayya baya da k'arancin mutunci yakan bawa kowa girmanshi.
   Matsalar shi daya idan aka tab'ashi baya kyalewa ra'ayinshi kuwa bamai canzawa.

     Wannan kenan kad'an daga biography d'in Yusuf.

Sai kuma muje gaba Dan jin su  waye raihan da usulinsu

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now