FULANIN BIRNI

1K 65 5
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 5⃣5⃣

Hannun shi ta damk'e sosai idonta sunyi fari tas kamar madara, wani sinadarin kyau ke fita daga jikinta.

"Mijina hak'ik'a wannan cutar ba wacca zan warke bace, yakamata nida kai da sauran 'yan uwa mu yarda da wannan."

Ido kawai ya zura mata batareda yace uffan ba, hakan ya bata damar cigaba da maganar ta.

"Ina son inyi amfani da wannan damar danake da ita domin in kyautata gobe na, zanso inyi amfani da sauran kwanakin da suka ragemin inyi aiki wa addini na k'asata da kuma garina."

Seda ta nisa sannan tacigaba.

"Masallaci, makaranta, tsayarda masu neman tsayuwa da k'afafun su, taimakawa mata masu Neman sana'a marasa jari."

Rungumeta yayi sosai yana zuba mata albarka "Allah ya albarkaci rayuwar ki matata Allah yacika miki wannan burin naki, insha Allah ko bayan ranki namiki alkawarin cika wannan burin naki."

"Nagode mijina. Nagode sosai."

Dikkan wani Abu mai daraja nata tafidda shi, kama daga kan gwalagwalai, zinari, da dikkan manyan kayan da batayi amfani da su ba hakama kayan d'akin ta wanda basu cika amfani dashi ba.

Dikkan kud'in dake banking nata taciro su,
Daga k'auyen su tafara kebi acikin wani kauye mai suna nasara 'yar k'aramar islamiyya akayi mai d'auke da azuzuwa ukku sai gefe d'aya masallaci wanda iya killacewa akayi, kana ta zuba littafai wanda tasan za'a buk'ata.

Wata unguwa acikin sokoto wacca ake kira helele, kai bazaka ce acikin Gari kake ba basuda basuda maraba da k'auye.

Islamiyya babba akayi wacca taci sunan Raihana Tahfidhul Qur'an.

Acikin wata d'aya aka kammalla komai sati d'aya aka zuba malamai masu inganci. Atake akafara tururuwar shiga makarantar abunka da bati ba'abiyan ko sisi sedai addu'ar da ake zubawa wannan boyar Allah.

Sai kuma madaidaicin masallaci a unguwar more. Wanda Sheikh Amir bashir bello ke jagorantar shi. K'aramun yaro mai ilimin addini.

A gaskiya raihan tayi namijin k'ok'ari domin dikkan wata kadara tata da dikkan wani Abu nata mai muhimmanci ta sayarda shi domin cikar burinta, ba k'aramin kud'i ta kashe ba.

Tin Yusuf na hanata har yazo yana taimaka mata, a halin yanzu da kanshi yakafa wata k'ungiya mai sunan Raihan peoples project, adik bayan wata biyar suke d'ibar mata goma domin su tallafa musu.

"Keee ki shirya yaron nan zamuje gurin ammaty kema ki shirya muje tare" turo baki tayi "zan shirya shi ni ba inda zanje" a inda yake tsaye bai juyoba yabata amsa "Dake zamuje ki shirya" daga haka yasa kai ya barta zaune a gurin.

"Iyye kuji wannan d'an sarkin nizaka nunawa isa, ank'i ake gidan ammar tinda lailar qanwar uwata ce ko ta ubana, inada business da families d'in ku ne  ba inda zanje" ita kad'ai ke sambatun ta a parlor.

Black STR yard yasa ka tareda hula da takalmi dik kakar aikin ne, sai had'ad'den agogonsa hublot, rik'e yake da wayoyinsa biyu iPhone x tareda galaxy A3 yazuba su a aljihu yakawo tiraren smart collection, bayan yayi spraying jikinsa da Eksoda pink tareda had'ad'diyar humrar shi.

Wannan had'in tirarikan na matuk'ar sanya shi farin ciki sunbi jikinsa sosai shi isa ko bai saka ba zakiji wannan k'amshin na tashi ajikinsa.

Salim ma bingyal bata barshi haka ba seda ta ha'de shi da wani had'adden Jens blue tareda rigarsa black, ta taje mar sumar kanshi dayake basa cire mai sedai agyarata Kullum kyace kan mace ne.

Yasha tirare da had'ad'd'un takalminsa, tuni ya fito Yusuf sak, indai kaganshi bazaka ce d'an hausawa ne ba saboda kyanshi da yanayin shigarsa.

Raihan ma tafito cas da ita dikda tanajin jiki bai Janata cakarewa ba acikin wani Swiss lece red and black tasaka k'aramin hijabinta iya gwiwa, itama dai ba'a cewa komai had'uwar ba kad'an ba.

"Tabb! Narasa wayafi kyau tsakanin son da dadyn sa" Yusuf yayi murmushi "dik kinfimu yin kyau gaki nan kamar balarabiya" hararar shi tayi "nifa ina kishi ai wannan had'uwar seka sa su lolita da lainat suyita kallemin kai" dariya yayi yaja hannun ta yarik'e salim da d'ayan hannun sa.

Bingyal dake kallonsu ta tab'e baki a gurin matarsa kawai yakeda kirki.

Wayarta taciro ta musu photo har biyar ba wanda baiyi kyau ba kowanni da style d'in sa, batareda sun san tayi ba.

Da kanshi ya bud'e musu mota suka shiga, ta kallesa "mungode" ya latsa kumatun ta "my pleasure."

"Auta fa?
"Au bata fito bane? Bara na dubu ta."

Kan kujera yasameta tana kallo tana chatting da faruk.

Wayar ya fizge daga baya.

Dasauri ta juyo tana watsa mishi kallon raini.

"Malam lafiya?

" Ciyo" ya bata amsa.

"Allah yabaka lafiya, basai ka fad'a alamu sun nuna kana d'auke da ciyo."

D'aga hannu yayi zai mareta sai kuma yasauke.

"Malam kabani wayata tinda dai bakai kasiya min ita ba."

"Ank'i d'in kizo ki karb'a, ba kinada k'arfi ba?

Tsaki tayi ta juya zata hau kujera ya fizgo ta yajawo ta har k'ofa ya tura ya rufe ganbun parlor d'in.

Kiran da raihan ta kwala mata ne yasa ta fasa shuka mishi rashin kunyar data tanada domin shi.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now