FULANIN BIRNI

1.9K 87 11
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU 

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 🔟

Sannu sannu k'awancen raihan da yusuf yafara tsawo yakan zo yajata suje yawon shan ice cream da hutawa .
Har ranshi yake jinta but yabar abun kan cewa dan tana Fulani ce haka yake jinsu kamar jininsa. Hakama raihan tad'auke shi kamar Abdul yayanta.
    Yau ma kamar Kullum tare suke da faruk sunje wani park , tayi shigar black and red d'in atampa gown ce da akayiwa akaiki da stones sai d'an k'aramun kyalenta data yafa d'an kwalin kuwa dashi tayi ribbon ta tufke kanta se wata red bag da ratsin black.
    Tayi matuk'ar kyau se wani kallo yake jifanta dashi.

     Tuni faruk yad'ago abokin nashi akan raihan kawai ya kyaleshi ne yana son ganin iya gudun ruwanshi akanta.
     Zaune suke kan grasses suna kallo a laptop d'in shi , sukaji anyi sallama bai d'ago ba dan yagane muryarta.      
    Raihan ce ta amsa sallama " bismillah mana kizauna kinyi tsaye kamar wata bak'uwa".  
    Faruk ya karbi zancen da cewa "ai shine kiyiwa kanki guri kam nan gurin ba bak'onki" .
    Harar shi tayi "ni ba gurinku nazo ba bare amin abinda aka saba naga wata se wani shan k'amshi take dama anmaida wuk'ar " idonta k'yam akan yusuf.
    Sarai yasan shitake jefawa magana amma yayi kamar babu ta agurin Idan ma yatanka ta zataji sanyi ne , raihan ce tace.
"Yusuf bakagan Amira bane kosai mun baku guri faruk muje daga can".
    
        Haushi yacika yusuf yarasa bakin magana sai binta da ido yake gira ta d'aga mishi suka bar gun itada faruk.
     Suna wucewa yajuyo kan Amira fuskar nan ba annuri " keee yanuna ta da yatsa lafiya mekike yi nan kokuma maitar ce ta taso ki agaba kika biyoni".
    "Murmushi tayi mai ban tausayi.
"Magana d'aya takawo ni gurinka".

       "Tambaya nake waccan waye nidai nasan ba families d'inku take ba sannan kuna yawo tare" 
    Kallon banza yabita dashi "kijini dakyau sunanta Raihana Adam itace kalata seem trip d'ina saboda haka ita zan aura kingane".

   "Yusuf takira sunan shi kuka nason k'wace mata kasani dani keda ikon zuciyata da tuni narabata da soyyarka nasani jarabawa ce daga Allah wadda kaima Baka wuce taba, Annabi yace kaso mutum dan Allah ka k'ishi dan Allah yusuf bakada wani dalili dazaisa kace baka sona, ko kana so kace min saboda ni ba yarenku bace , ko kuma raihan tafini kyau ne tafini ilimi kota fini kudi da usuli ne".
       "Of course tafiki gurare da dama raihan tafiki sanin duniyar gabadai ke inbanda soyayya mekika sani , in fact ni natsani mace low class raihan kuwa itace mace ta farko dana fara had'uwa da ita kyawuna da kudina ajina da muk'amina basu rud'eta ba bantaba kula mace ba bankuma tab'a tunanin cewa akwai wadda zan furtawa koda 3 word's ne ban bar mata wani Abu a zuciyar taba".

     "Zama ka fad'a anzo gun wlh anzo agun, love gashi kagan wadda kake ra'ayi amma ita batada wannan feelings akanka nan gaba zaka had'u da wadda zaka cewa I love you tace I hate you "  
     Shak'o wuyanta yayi never wlh har abada koda matan duniya zasu taru kaina banga wacca ta isa nacewa I love her  ba niba d'an k'auye bane bakuma jaki bane irinki jaka" 
      Ranta yasoma baci da  iskancin sa saboda haka tace jakai dai kasan waye jaka bani ba"
   Atake ya wanketa da wani gigitaccen mari seda takai k'asa tareda sakin wani ihu atare raihan ta iso da faruk suna mishi kallon tambaya .

     Raihan batabi takanshi ba taje gurin Amira ta tada ita tsaye tana share mata hawaye suka koma gun da suke itada faruk.
   "Meya farune dukan ki yayi ne? Amira takasa magana se kuka take bawai kukan marinta da yayi ba bak'in cikin wulak'anshi take.
   "Ya Allah Kaine ka jarabeni da soyayyar bawanka Allah kabani ikon cinye jarabawar nan kasaka min da mafi alkhairi" 
Hawayen tausayi suka zubowa raihan ta dafa Amira " karki damu Amira kowani bawa datashi k'addara taki jarabawar mai sauk'i ce akan wani yanda zakiyi kicinye ta shine.
     Kikoma ga Allah kicigaba da kai mishi kukan ki baccin dare banaki bane k'iyamul lail zaki dage dayi kina fadawa Allah damuwar ki

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now