FULANIN BIRNI

1.2K 84 9
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

©ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 6⃣8⃣

Yau ta kasance Monday, saboda haka tin da tayi sallar asubah bata koma bacci ba.

Kitchen tashiga ta had'a musu simple breakfast, ferfesun hanta, wanda yaji alaiyahu, sai kuma wainar kwai, da ruwan shayi.

K'arfe 7dai_dai tagama shirinta cikin uniform d'in ta masu kyau, takawo after dress ta d'ora sama.

Sauri_Sauri take tafita, tsabar missing school da tayi.

A falo tayi kicib'us dashi, 'yar k'aramar fad'uwar gaba tasa meta, sedai tayi k'ok'arin b'oye damuwar ta, tacigaba da tako kamar wata b'arauniya.

"Where are you going.?
Cak ta tsaya tana gab da bud'e k'ofa.

"School."

ta bashi amsa cikeda fargabada a zuciyar ta.

"Da izinin wa"?
"Hu tuna yak'are daga yau."
"Nace da izinin wa zaki fita?
Ranta ya soma b'aci akan hakan, ta juyo fuskarta wacca tayi kalar b'acin rai tace.

"Banice da alhakin neman izinin ka ba, wanda yabaka aurena shine yanemi izinin hakan, sannan kabayar tin wancan lokacin, so a yanzu babu buk'atar in sake neman izinin ka, saboda kasan da wannan zancen."

"Ba inda zakije" kallon sa tayi cikeda mamaki, tayi d'an k'aramin murmushi.

Bud'e k'ofar falon tayi tacigaba da tafiyar ta.

"Idan kika kuskura kika fita zaki gane bakida wayo" banza ta mishi ganin yana Neman b'ata mata lokaci.

Rasa tayi abinda zatayi bata tab'a hawan napep ba, amma yau zata fara, yau da ta taka wani babban matsayin da bakowa ke akai ba.

Da ace anbarta da zab'inta ta tabbatar shine wanda zai ja ragamar kaita school ba kyara bare bak'ar magana, sai akasin hakan yakasan ce kanta, auren mutum mafi k'arancin mutun ci a idonta.

Kuka ne yazo mata da k'arfi, narashi, narasha faruk da yanzu shine zai sakani a farin ciki, ina kake ne faruk, ina kashiga.

Tana cikin wannan yanayi taji horn a bayan ta.
Ko da ta juya ashe Nazifi ne d'an class d'in su, acikin motar su, tareda k'annen sa, bata da wani zab'in daya wuce ta bisu, muddin tana son isa makaranta cikin lokaci.

Saida suka fara ajiye wasu maza biyu a darud da'awa sannan suka bi ta play over zuwa khalipha international school.

Murna sosai a gun yesmin lokacin da ta hango bingyal.
Rungume juna sukayi suna cikeda farin ciki gamida k'ewar junan su.

K'arfe biyu suka tashi daga school, kai tsaye masallaci sukayi suka gabatarda sallah kana, suka wuce school shop , maltina kawai ta siya da madara, yesmin kuwa cornflakes tasiye.

K'arfe uku suka shiga lesson d'in, chemistry basu fito ba sai 3:40 suka shiga lab sharp_sharp suka fito.

Sallar asr suka bayar, cikeda gajiya kowacce ta kama hanyar gidansu.

Napep ta hau ya kaita har k'ofar gidan ta, ta sallameshi kana tashige ciki.

A inda ta barshi anan ta sameshi alamar baifita ko Ina ba sai abun sallah da carbi a hannun sa.

Batareda tsoro ko fargaba ba, ta nufi hanyar d'akin ta.

"Dakata"

Ta juyo tana kallon shi. "Lafiya?

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now