FULANIN BIRNI

1.1K 65 3
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE  6⃣0⃣

Zaune yake kan k'afafunta kamar yanda yasaba tana shafa kanshi.

"Yusuf yakamata kanemi matar aure zamanka ahaka ba amfani, ko saboda salim ai."

"Karki damu ammaty ina gab da kawo miki wacca zan aura, zan matuk'ar baki mamaki."

Shiru tayi tana nazarin sa, daga bisani tace "Yusuf kabani dama in zab'a maka irin type d'in da kake so, nafi kowa saninka, nafi kowa sanin ra'ayinka."

"No ammaty kedai kiyimin addu'a kawai domin gab nake da zama Ango."

Yusuf wannan karan bazan barka haka ba dole ka auri Amira ina son wannan had'in. Acikin zuciyarta take wannan zancen.

Indomie yake dafawa salim tareda kwai, goye yake dashi, yanata zuba mishi surutu.

Atare suke ciki yabashi abaki shima yabashi.

"Abba ina momy taje bata dawo ba" murmushi yayi mishi "salim zata dawo tace seka ci abunci dayawa."

"Abba anti bingyal. Dafe kanshi yayi yace "tana skull yanzu. kabari na kaika gurin su usaina kaji."

Dayake bayada rigima yace "to"

Mai gadi ne keta zabga knocking amma bawanda ya kulashi, laila kam ba jinsa sab'anin ummi datake sama bazata jiyo shi ba.

Dadyn Yusuf ne da kanshi yasauko kasancewar yana jiyosa daga b'angarensa.

"Malam musa lafiya?
"Ranka yadad'e wani mutum ne ke sallama da kai"
"Wani mutum kuma to waye shi?
"Agaskiya bansan shiba, amma dik yanda akayi ahalinku ne, domin yanada ruwa da fulani"
Jin yace d'an uwansa yasashi washe baki..

"Ah_to madallah madallah kayi mishi iso zuwa barayata zan bud'e daga ciki."

Haka akayi yaje ya sanarda bak'on sak'on alhaji.

Har k'ofar da zata kaishi barayar Alh yakaishi, sa'anan yadawo.

"Ahhh....Alh da kanka shine ka tsaya waje ai da kayimin waya, da kaina zan fito. To sannu da zuwa."

"Yauwa Alh munsameku lafiya?

Baffa ne wato mahaifin su raihan.

Baffa_"Jam wuro waalí? (Antashi lafiya)
Dad_ "Jam ní" (lfy lau)
Baffa_"Noy korreji maa? (Ya iyali)
Dad_ "Al hamdililalay"

"Yauwa alh dama nazo ne kan zancen yaron nan Yusuf"

"Toh ina jinka alh"

"Zaman sa ahaka ba aure bazai yuba, wato na fuskanci ba aure agaban sa, yin auren kuma zai rage mishi damuwa da kad'aici"

Dad ya gyara zama "sosaima kuwa nayi wannan tunanin abunda yasa na kyalesa domin yak'ara samun lafiya."

"Hakane alh sedai Nazo mana da maslaha wacca nake ganin zata taimakemu gabaki d'ayan mu"

Seda yasauke wani nunfashi sannan yace.

"Alh ina Neman alfarmar daka sake bani wata dama in bawa yaronka 'yata, saboda kar salim yashiga maraici, sa'annan kuma bana son zumuncinmu yayi k'asa."

Tin kafun yakai aya. Dad yakeyin murmushi yana yana gyad'a kai alamar gamsuwa.

"Yo Indan wannan ai seka nemeni ni nazo nida zan nemawa yarona auren 'yarka.

Nadad'e ina wannan tunanin, domin raihana yarinyar kirki ce, tanada nutsuwa, da tarbiya, nasan kuwa sauran ma zasuyi, yo kowa ma zaiso had'a zuri'a da ku, gidan mutunci da karamci, Alhamdulillah nafi kowa murna da wannan al_bishir. Hak'ik'a banida kalaman gode maka, Allah yasa ka maka da wannan alherin da ka sake kawo mana."

"Ba godiya atsakanin mu alh, naji dad'in amincewar ka Allah yasanyawa wannan had'in namu albarka."

"Amin."

"Wace yarinyar ce acikin yaranka?

"Salamatu ce autar gabad'aya"

"Au ni nazata ai mabiyiyar raihana zaka bayar?

"Alh kamanta anmata miji?

"Aikuwa hakane na shafa wa wlh. Salamatu d'in ai ma salim yafi yarda da ita gashi tayi zama agidan, zata fahimci komai gameda Yusuf, fatanmu Allah yasa su amunce."

"Amincewa dole. Mu muke da iko dasu basu ne masu iko damu ba. Alhamdulillah yarane masu biyayya bana tunanin asami wata matsala."

Dad cikeda farin ciki ya furta. "Ai ni yanzu zan bada sadakin basai anje ko ina bana, in yaso sai asaka rana"

Baffa yayi dariya "Hakan ma yayi."

50k yaje ya d'auko a bedroom d'in shi sababbi fil.

Baffa yasanya biki nanda wata d'aya.

Daga haka suka cigaba da tattaunawa akan yanda komai zaizo da sauk'i.

Da murna baffa ya shiga gidan shi yasami gwaggo da anti salma sai Abdul.

Gwaggo tace "yau dai da alamar farin ciki a fuskar ka. Wanda na jima banga irin sa ba."

"Hakane ungo wannan" ya bata kud'in.

"Na miye wannan?

"Sadakin 'yar ki ne"

"Wace yar kuma?

"Autar ki, na bawa Yusuf ita har abada. Sai dai kuyi hak'uri ban nemi shawarar ku ba, na zartadda hukunci."

Anti salma tayi hamdala.

"Madallah da uban kirki wannan abun yana raina matuk'a salim bazaiyi maraici ba."

Abdul ma kanshi yaji dad'in hakan, "Baffa wannan had'in yayi gara da kayi hanzarin sake dawo da sirikinka agidan ka, Yusuf mutumin kirki ne, kowace mace zata so yakasance abokin rayuwar ta."

Gwaggo batace komai ba se washe baki take.

"Kai kake da ikon aurar da ita ga wanda kaso asanda kaso, nayi matuk'ar farin ciki Allah yasanya kar su bamu kunya.

Toh pah readers ana wata ga wata kenan.
Shanuwa ta auri barunje.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now