JARABTA

1K 88 9
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

ASISI B. ALEEYU

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 89

Yusuf yafara fita hayyacin sa domin bashida aiki sai Kiran sunan salma.
Tin ana lallashinsa har aka dawo tofa mishi addu'a domin abun yazo kamar da tab'uwar hankali.

Sallamar sa tasa shi yin shiru yana nazartar ta, har ta k'ara so daf da shi sannan ya kauda fuskarsa gefe.

Hannun sa ta kamo biyu ta haďa cikin nata idon ta taf da kwallah.

"Mijin Amira haka ka dawo, waya d'auki salma ne waya saka min miji acikin wannan mawuyacin halin"
Shiru yayi baice komai ba sai cikinta da yake kallo wanda yake watannin haihuwa.

Kanta ta ďora akan cinyar sa tana zubda kwallah.

A hankali yasa hannu ya janye mata fuska ya tashi daga gurin zuwa d'akin ummi.

Hawayen da take b'oyewa ne suka cigaba da ambaliya akan fuskarta, aranta take jin zafin har yanzu dayake acikin yanayi yakasa yafiya ga laifin ta, yak'i ya manta abunda ya wuce.

Amma laila ta dafa ta da sigar lallashi, nan ta shige jikinta tana kuka.

"Kiyi shiru amira komai na zuwa k'arshe insha Allah, kin kusa komawa gidan mijin ki wannan alk'awari ne dana d'aukarwa kaina."

Washe gari aka tashi da mummunan lamari ciyon salim daya firgitar da kowa, ba wanda yasan takamaiman abunda yasa meshi sai aman jini dayake yi hanci da baki.

A rud'e aka kaishi asibiti likitoci suka duk'ufa kanshi, domin bashi taimakon gaggawa.

Idan ajali yakira dole aje idan azra'il ya kwankwasa k'ofa ko da shiri ko babu sai anje, hak'ik'a Allah baya barin wani dan wani, Al-maut hak'kun wahuwa shaded, Mutuwa gaskiya ce kuma mai zafi ce mai tsanani ce.

Yaro ko babba mai imani ko marashi imanin wlh kowa sai ya d'an d'ani azabar mutuwa, alokacin da za'a zare rayuwar annabi yake cewa aisha, ya Aisha innal maut shadeed , hak'ik'a mutuwa nada zafi, har sayyada aisha tace wlh kar inji wani yace annabi yaji sauk'in mutuwa saboda yanda taga ya azabtu da fitar rayuwa.

Babu wani abun so sama da manzon Allah SAW yaji zafin mutuwa bare mu masu sab'on ubangiji masu kauce faďar Allah masu biyewa soye-soyen zukatan su.

Mun manta cewa akwai wata rana mai zuwa ranar da baki bazaiyi magana ba saboda ya kasance yana faďar k'arya ranar da gabbanmu zasu bada shaida akan mu ranar da uwa ke gujewa d'an ta ranar da masoyi ko mak'iyi bazai maka amfani ba ranar da rana zata riķa tafarfasa kwanyar kawunanmu, aranar makaranta Al Qur'an zai musu rana ranar qurani zaizo ya musu inuwa. ranar zaka yaro kanshi yayi fari kamar daro yayo bak'i na ban tsoro ranar fushin ubangiji
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.
Allahumma ajirni minan nar.

Salim dai ya karb'i Kiran mahalicci, kunga girma da buyar ubangiji ko, idan Allah yaso bawa daga cikin bayinsa sai ya jarabceshi jarabawa mai tsanani, har bawa ya Yanke k'auna ga rahmar ubangiji, alokacin da jarabta ya maka yawa sai ka fara tunanin kamar kai kad'ai duniya ta juyawa baya, idan ka jure kayi hak'uri sakamakon babba ne nan duniya ko acan k'iyama.

Acikin annabawanmu babu Wanda Allah bai jaraba ba, so jarabawar Allah yana nuna k'aunar sa ne ga bawansa.

Kuga yanda Allah ya jarabce yusuf ya karb'i raihana, ya bashi wacca yake murad'i sannan ya sake amshewa, ya bashi amanar ďa kuma ya anshe abunsa, dama shine mai bayarwa kuma shi yake amsa alokacin da yaga dama ba tareda amincewar bawa ba.

Tin yana fahimtar masu kuka da jajanta mutuwar har ya daina fahimtar me suke cewa.

Sai dai yabi bakinsu da ido yana kallon yanda yake motsi, baya fahimtar komai.

FULANIN BIRNITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang