FULANIN BIRNI

756 50 2
                                    

FULANIN BIRNI

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

ASISI B. ALEEYU

PAGE 93

A gaban ummi ya zube yana kwasar gaisuwa.

"Am yusufah abunda yasa nake neman ka, magana ce mai muhimnanci. Akan zancen matarka amira"

Wani irin fad'uwar gaba ya ziyar ce shi lokaci guda yafara ganin fuskar ta lokacin data zubar masa da ciki.

"Kana jina?
Ya gyara zama sa , cikeda alhinin zancen ta yace "uhm ummi inaji"

"Yauwa to abunda zan fad'a maka shine, idan dai har bazaka iya maida ta gidanka ba to ka sauwak'emata taje tasamu wani mijin ta aura, banga amfanin wannan horon ba, iya horuwa yarinyar nan ta horo ta gane kuskurenta tayi nadama, to mene yasa bazaka yafe mata ba, laifin da kake yiwa ubangijinka baifi wanda ta maka ba? Shida ya ķage me baki d'aya, wannan ba hali bane mai kyau ka canza rayuwa ba'a son mutum da rik'o"

Kansa k'asa yana saurarenta har ta dasa aya, ya ďago idonsa da suka canza launi ya kalle ummi batareda yace uffan ba.

"Auu dan na maka nasiha shine kawani ta b'une fuska, kaje kayi abinda kaga dama rayuwar kace"

Ķasa ya mayar da kansa yana tunanin tabbas salma ce takawo k'arar sa gurin ummi, inkuwa hakane wlh zata yabawa aya zaķinta.

Fuuu ya mik'e tsaye ya bar d'akin ransa a matuk'ar b'ace.

Salma kuwa taci wankanta cikin wata rigar turawa mara hannu sai gidan mama da take dashi, rigar iya gwiwa take fara ce sol mai kamada weeding gown, ta gyara kanta ta tufkeshi baya ta jawo wani zaren gashin agaban kanta yana yawo.

Tuni takoma kajool ta india.

Tana bedroom ya shigo, ya fige wayarta yana duba last call d'in ta, cikin sa'a yaga no din unmi sai ta yesmin k'awarta.

Tabbas dai ita tagayawa ummi wannan zancen da sukayi.

Da k'arfi ya banko k'ofar d'akin wanda yayi sanadiyyar firgitata har ta yadda kwalbar tiraren da ke hannunta , atake ta farfashe.

Ya cakumo rigarta har saida zip dinta ya buďe.

"Me kike tunanin kin aikata haďani da mahaifiya ta? Kin kuwa san abunda kikayi? Ba abunda na tsana sama da akai laifina gurin mahaifana, amira k'anwar babar kice ko k'anwar babanki ce? Da zaki kafe kan sena mayar da ita. Wlh tallahi akan wannan abun da kikayi zamu samu matsalar da bamu tab'a fuskanta ba , uwata fa, saboda k'iyayyar dakike min har ya kai kina nemarwa kishiyarki hanyar dawowa saboda naraba hankali na gida biyu ko.

Fine kin kyauta. Koba komai a yau nasan da wacca nake rayuwa.

Tin da yafara ta zuba mishi ido har ya dasa aya batace uffan ba, mamaki fal aranta , yaushe tayi wannan zancen da ummi ? Iya sanin ta sunyi waya jiya akan ya jikin raihan dake fama da mura bayan wannan ba abunda sukayi magana.

Hankaďa ta yayi gefe batareda ya damu da inda ta faďa ba. Yayi ficewarsa cikeda b'acin rai.

Rufo k'ofar da yayi da k'arfin tsiya ya bata damar fashewa da kuka,  dama haka aure yake da k'alubale iri-iri , bak'in cikin safe daban na yamma da baban.

Wunin ranar dai bata fito ko parlor ba, tana jin k'iriniyar twins d'inta batabi ta kansu ba, dakyar tasamu ta lallab'a tashiga toilet tayi wanka ta wanke jinin dake mata zuba a k'afa, sanadiyyar hankaďata da yayi acikin kwalbar da ta fashe.

A zaune tayi sallar Magrib da asr wanda bata samu tashi tayi ba, ciyon kai mai tsanani ya rufe ta, atake jijiyoyin kanta suka fito ruďu ruďu, idonta a lumshe kan abun sallah ga zafin k'afar ta gakuma zafin ciyon kai wanda har idonta yasoma ciyo.

Yana kishingiďe kan gado yana jan carbi wayarsa tayi ring.

Ganin sunan ummi saida hantarsa ta kad'a , kaddai salma tasake haďa shi da ummi.

"Hello kanajina ,  ya jikin raihan ne, inata yiwa salma waya bata ďaga ba ko Lafiya?

"Uhm uhm lfy lau ummi. Wayace miki raihan batada Lafiya?

"Au baka saniba yarinya na fama da mura tin shekaranjiya, jiya har waya munyi da uwarta tace min ka kaita asibiti har an rubuto mata magani, shine naji ko taji sauk'i"

"Am eh hakane ummi dama dai banzata kin sani ba shiyasa"

"Toh shikenan ka gaida min salman da raihan d'in da salim. Sannan karka kuskura zancen da namaka na mayar da matarka ya shafi salma, karkuma kace mata ni baka umarnin mayar da ita, kayi k'ok'arin shawartar salma na tabbatar iliminta da hankalin ta bazasu bari ta hanaka ba"

"Toh ummi insha Allah"

Wani sanyi da tausayin matarsa ya ziyar cesa.

Dama ashe bazancen sukayi da ummi ba, to waya kai raihan asibiti?  Allah sarki ko musu bata masa ba, sai kuma ya tuna kishi irin na mata amma ta danne take k'ok'arin ganin ta ďora shi kan hanya. Lallai wannan itace mace ta gari.

A parlor yasame inna azumi tana bawa raihan magani.

Yace "inna waya kai yarinyar nan asibiti?
Inna tace "bakai ne ka turo faruku abokinka ya tafi da ita ba aka bata magani har ya nuna min yanda zan bata, ai taji sauk'i sosai , maganin nakeso ta k'arka're shanyewa"

Wani haushin kansa yaji rashin kularsa ga iyalinsa har yasa baisan lafiyar su ba.

Da sauri ya shige d'akin salma yasame ta kwance .

Yayi saurin isa gareta ya rungumota yana tambayar lfy?

Zafin dayaji jikinta yayi yasanya shi yin shiru. Yana kallon yanda fuskarta ya kumbura hawaye na zuba a kumatunta, ga jijiyoyin kanta da suka fito.

"OMG. Salma kuka kikayi har haka?  Kinga kin janyowa kanki ciyon kai , dan Allah kiyi shiru na hak'ura na yafe miki , na fahimta baki sanar da ummi komai ba, kuma zan mayar da amira dik abunda kika ce shi za'ayi kinji"

Dikda taji dad'in kalamansa amma zancen maida amira yatsaya mata arai saida taji wani fad'uwar gaba.

Kishi kenan kumallon mata.

Ta danne zuciyar ta tareda yak'i da shaid'an.
Tayi lamo ajikinsa tana sauk'e nunfashi.

Cak ya ďagata zuwa mota sukayi asibiti da ita.

Magunguna aka rubuta mata tareda yiwa mijinta kashedin kula da ita damuwa tayi mata yawa arai har jininta yasoma hawa.

Wata sabuwar kulawa da k'auna ta b'arke tsakanin masoyan biyu

Tauuuuu.....masu karatu kunji pah....ko yusuf zai maida amira?
Ko yaya wannan zaman zai kasance?
Anya amira zata juri kishi da salma? Wacca tagama siye zuciyar sa?

Ku biyo y'ar mutan sakkwatawa.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now