FULANIN BIRNI

942 58 3
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 5⃣4⃣

A hankali take saukowa daga kan gadon nata, bata son tayi dogon motsi wanda zaiyi sanadiyar tashin sa daga bacci.

Mirror chair tajawo tazauna bayan ta kunna blue light, a hankali tarage hasken tana kallon kanta ta madubi tak'ara haske da kyau sosai leb'enta sun k'ara jajir kamar na turawa.

Hannu tasa acikin gashinta tana zarowa tamkar dama d'orashi akayi, yaringa zubowa k'asa abun tsoro kusan 70% na gashin kan nata yacire bayan wanda ta baro kan gado.

Kuka ne yazo mata da k'arfi, tasa hannayenta ta rufe bakinta tana  mai cigaba da zubda hawaye.

Motsinta ne yasoma ta yarda shi, yafara lalubenta agado baiji taba yabud'e ido tareda tunanin ko taje toilet ne.

Hasken daya gani yasashi bin d'akin da kallo, lokacin da idonsa yasauka kanta bak'aramin tsoro yaji ba dasauri yasauko daga kan gadon yana kiran sunan ta.

"Raihana ta lafiya meya sameki kike kuka? Juyowa tayi tareda share hawayen fuskarta tana k'ok'arin danne damuwar ta gudun kar ta sakashi acikin ta.

"Miye wannan? Yake tambaya lokacin da k'afarshi taci karo da lallausan gashinta dayake a zube kamar anyi mata aski.

Dasauri tazo gareshi ta rungumesa tana kuka.

Yarasa ta inda zai soma lallashin ta, se bubbuga bayan ta dayake yi.

Kan gado suka koma, ya zura hannunsa ya kunna wutar d'akin mai haske sosai.

Bak'aramin bugawa gabanshi yayi ba lokacin daya ga kanta dakuma wanda yake a zube.

Seda yasaita muryarshi dake Neman gagarar shi, kana yace "kuka banaki bane matata addu'a zamuyi mubarwa Allah lamarin shi, wannan gashin daya zube yana yuwa ya mutu ne, sabo zai fito mai kyau original wanda ba editing, koba haka ba."

Murmushi tayi ta girgiza kai.

Da haka yasamu bacci yasake kwasheta.

A hankali a hankali ya shinfid'ar da ita kan gadon.

Ya kwashe dikkan gashin nata na kan gado da wanda yake k'asan mirrow.

Leda yasamu yazube shi a ciki zuciyarsa sai bugawa take, azahirin gaskiya ciyon nan yafara firgita shi, ace wasu daga cikin sassan jikin mutum suna zuba, oh Allah kayiwa wannan boyar taka sauk'i da rad'ad'in wannan ciyon nata.

Kasancewar yau weekend ne yasaka basu fitoba har kusan 11. lokacin har bingyal ta d'ora girkin rana wato lunch, inda ta tayi potato salad.

Already ta gyara carrot da potato d'in ta tayi musu yanka gajeru, ta wanke su tas ta tsane ruwa. Ga kuma tafasasshen nama da aka Yanka k'anana .

Gefe d'aya angyare cabbage, green beans, green pepe, sliced Onion.

Garlic, magi, cream salad, salt, nutmeg,

Bayan ta tafasa potato da carrot tareda gishiri da magi, sannan ta soya wannan cabbage d'in da Gbeans, da Gpepe da Onion bayan ta zuba d'an d'ano, bawai ana so su k'one bane sama_sama akeson su.

Ta kwashe komai ta zuba inda yadace.

Bawai angama bane da akwai sauran hadi sedai kuma ba buk'atar had'asu yanzu se antashi ci.

Wanka taje tayi tasaka kayan da suka dace da ita ta d'auko littafin Umdatul_Ahkam tana dubawa.

"Bingyal.....bingyal..... bingyal"...dasauri tayi jifa da littafin da ke hannunta kan gado ta fito waje aguje.

Raihan ce keta faman kwala mata kira.

"haba sis kinbani tsoro wlh nazata ko wani abun ne" murmushi tayi "I'm so sorry my little sister. Kin ji tsoro ko, ba wani abu bane sonake kizo kiyi serving d'in mu."

"Kai sis breakfast d'in ma sena yi serving d'in Ku sekace wata kuku" batareda ranta yaso ba tayi serving d'in su, dik wannan abun saboda Yusuf takeyi aganinta mezai hana yayi serving matar shi, dole sai ita.

"Kai har kingama lunch kenan? Ya tsine fuska tayi alamar eh tacigaba da zuba musu soyayyen dankalin turawa tareda soyayyen alaiyahu wanda yaji anta da kwai, tea mai kauri ta had'a musu tajawo wani cup wanda akayishi musamman domin shan cornflakes da sauran su.

"Karki had'a bana sha" Kalmar data fito daga bakinshi kenan.

D'an k'aramun tsaki tayi tacigaba da zubawa raihan. Lokaci dayawa yanajin kamar ya shak'eta saboda rashin kunyar ta sai kuma yadubi darajar yayarta da iyayenta yafasa aikata k'udurinsa akanta.

Sosai sukaji dad'in breakfast d'in nata, har basa son su dena ci.

Suna tsaka daci sukaji anyi knocking, raihan ta umurci bingyal dataje ta dubo waye.

Cikin takunta datakeyi mai kama da na marar lafiya, taje ta bud'e k'ofa.

Murmushi tasakar mishi lokacin da tayi tozali da kyakkyawar fuskar shi, shid'inma ya maida mata da amsa.

"Gimbiyata kinyi kyau fa" ido ta ware mishi irin really d'in nan, wanda hakan datake mishi bak'aramin narkar mishi da zuciya yakeyi ba.

"Auta lafiya waye ne? Se a lokacin ta tuna cewa akwai mutane a parlor d'in.

Atare suka shigo suna dariya.

Raihan ta bud'e baki   "my sugar nifa  narasa kan abokin nan naka, kwana biyu d'in nan senaga yana shisshigewa auta kodai ank'ulla banida labari ne?

Baki ya tab'e "kunfi kusa  ki tambaye ta, ni ba shiga shirgin yara nakeyi ba daga haka ya tashi tsaye yayi restroom d'in shi.

Faruk ya girgiza kafad'a jealousy kawai ba abunda zai hanani auren auta sedai in madam kin hanani, ya maida dubanshi ga raihan.

Hannu bibbiyu tasaka ta rufe baki  "au abun har ya kai nan, lallai kun yaudareni da baku sanar dani ba, yakamta nayiwa gwaggo wannan albishir d'in, nafi kowa murna da wannan had'in na tabbata zaka rik'e min k'anwata amana, inama ace zanyi tsawon rayuwa naga ranar auren ku."

"A'a madam ba yanzu nake son sanarda su akwai shirin danaje idan nagama lokacin kowa zai sani, dai_dai ta k'are school d'in ta."

Kuka ne yaci k'arfin ta dasauri bingyal tazo ta rungume ta "haba sis wayace zaki mutu nima wlh idan kika mutu sedai na biki, bazaki mutu ba wlh bazaki mutu ba! Ita d'in ma seta fashe da kuka.

"O gosh! Ya fad'a tareda dafe kansa.

Yusuf dake sauraren su ya dunk'ule hannun sa ya naushi kujera, wani bak'inci ke zarya tsakanin zuciya da ransa, meye makomar sa idan akace yau ba raihan a duniya, wazai maye mishi gurbinta adik fad'in duniyar nan.

"Noooo!!! Bazan tab'ayin aure ba nayi bankwana da soyayyya idanma har na rayu d'in na tabbata maraicinta ne ajalina."

Haka yaita sambatu shi d'aya daga bisani ya fuskanci alkibla batareda yace komai ba kukan zuci yakeyi wanda yafi na fili ciyo.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now