WATA SABUWA

1.2K 82 12
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

ASISI B. ALEEYU

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 83

Love me kikeyi ne?
"Breakfast man?
"Amma bana hanaki aiki ba"
"Idan banyi ba wazaiyi, bana son take away d'in nan, I'm sorry" ka faďa ya ďaga "ok shikenan amma dan Allah ki kula da kanki bana son kina wahalar min da baby" hararar ta maka mishi "Au bama ni kake ji ba sai babynka" dariya yayi yafita daga kitchen d'in yana faďar "Waa? Ni na isa."

Sai da tayi wanka ta shirya cikin wasu ķananun riga da wando kalar kore sai kanta data naďe acikin farar hula ta ďan janyo siririn gashi a fuskar ta,  a take ta fito wata baby da ita.

"Wow masha Allah! Babyn nan tana son kashe ni da salon ta,  wankan ta. Kin ganki kuwa, kamar turawan America, a gaskiya ba ķaramar wauta naso nayi ba da na kusa rasa ki."

Wainar k'wai ta cusa mishi a baki. Ba shiri yayi shiru,  "Wannan surutun ya isa haka, muje mu karya" Binta yayi tamkar raķumi da akala. har zuwa dining nan sukayi feeding junan su.

Shigowar message ne ya katse musu firar da sukeyi, Arazane yake duban wayar sa, kallon ta yake tamkar yau yafara riķa ta,  har sai da bingyal tace mishi "Lafiya naga kazama wani iri da kai " murmushi ya k'irk'ira Wanda bai kai ciki ba, "Bakomai. Ina zuwa" ya nufi hanyar bedroom d'in shi, da ido ta bishi, tana tunanin menene ya canza shi lokaci guda,  koma miye inaga bayada alak'a da insani. Da haka ta rufe babinsa ta kwashe kwanukan da suka b'ata ta Wuce kitchen dan gyarawa.

Yusuf kam sai da yayi kwance sannan ya bud'e message d'in mai ďauke da number faruk!
"Assalamu Alaika. Abokina ina maka murnar samun ķaruwa daga mace mafi soyuwa a zuciyar ka. Allah yasauke ta Lafiya itada amira. ashafan kan salim my boy ina kewar yarona sosai" nannauyar ajiyar zuciya yasauke ya cigaba da karanta sak'on har saida yaji tamkar ya hadda ce shi, kana yayi saurin dialing number faruk d'in amma yaji ta a switch off. Gosh! Ya faďa tareda dukan kujera.

Car key ya d'auka ya fita da sauri, sai gidansu faruk. Bai tsaya neman izinin shiga gidan ba , ya wuce direct har babban parlor.
Yayi sa'a da maman faruk na zaune tana kallon news.
"A'a wanake gani kamar yusufah" murmushi yayi tareda sallama "Mama nine. Allah yasa bakiyi fushi da d'an ki ba"
"Uhm banyi fushi ba yusufa , uwa bata fushi da yaron ta, zauna ko" ta nuna mishi kujerar da take kusada ita.

Bayan sun gaisa yake tambayar ta k'o faruk yazo. Ajiyar zuciya ta sauke ta dubi yusuf tace "Yusufah bansan meya shiga tsakanin ku ba. Bazan so ji ba. tinda baku so nasan meya had'aku  ba, amma kusani hak'uri maganin zaman duniya, kuna yara ba'aji kanku ba sai yanzu da kuka zama iyaye, koda yake kaine uban shi zaman gwauranci bai ishe sa ba."

"Mama kiyi hak'uri zaiyi aure nan bada jimawa ba insha Allah, hasalima nine silar k'in yin aurensa da yanzu yanada baby" remote d'in dayake hannunta ta ajiye ta dubesa da kyau tace "ban fah gane inda ka dosa ba" dogon nunfashi yaja. nan yashiga bata labarin abunda ya had'ashi da faruk.

"Zancen banza kenan. Dama dan wannan abun yayi tafiyar sa, waton bai yarda da k'addara ba, yana jayayya da hukuncin ubangijinsa, kokuma so yake ka faranta mishi ka sab'awa umarnin iyayenka, ai abinda sukayi sunyi daidai. Allah dai yabaku zaman Lafiya, shi kuma ya santa zaizo ya sameni."

"A'a mama dan Allah kibi abin shank shi akayiwa laifi dole a bishi a sannu" harara ta makamai tareda nuna mishi k'ofar waje. "Tashi kabani guri kar ranka ya b'aci laifinsa ya shafeka" sanin halin mama yasaka bai tsaya cewa uffan ba ya kwashi takalminsa yabar gidan zuciyar sa cike da kewar faruk da kuma fargaban abunda mama zatayi wa faruk d'in.

Yesmin.....

Umar  ne ya ajiyeta gidan yusuf ya wuce gurin aikinsa. Da gudu ta shiga gidan tana kwalawa bingyal kira.
Salma! Salma!! Itama da gudun ta fito tana jin kamar muryar Yesmin. Da gudu suka rungume juna.
"Yesmin nayi fushi tinda kikaje kano ko waya babu" Yesmin ta kama kunne alamar hak'uri tace "wlh salma waya ta na bari a gida kuma ban rik'e wannan layin naki aka ba, amma ki tambiye mijinki Sau biyu ina bada sak'on gaisuwa yabaki , idan muna waya da umar suna tare " Bingyal ta tab'e baki "ni bai fad'a min komai ba."

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now