FULANIN BIRNI

1.4K 86 4
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4⃣9⃣

Zaune suke gaba d'aya su d'akin modibbo suna fira, tana basu labarin k'uruciyar Kabiru abbansu Yusuf kenan.

Wani gurin suyi dariya wani gurin su zubadda hawayen tausayi.

Laila ce kad'ai bata gurin da Amira.
    Laila tana gurin tasalla uwargidan ard'o, Dama tinda akazo suke wani together wanda ni ban san daga ina abun yafara ba.

Amira kuwa tana masaukin su, kunyar raihan yahanata sakat, da tsoron Yusuf takasa sakewa, acikin su takasa yafewa kanta abunda ta aikata.

Modibbo ta dubi bingyal tace "Ab'a selli, náá? (Kina lafiya ko?) Bingyal ta duk'adda kai tace "Al hámdilillày" modibbo ta gyad'a kai batareda gamsuwa ba.

Ita kad'ai ke tafiya, tana 'yan wak'ok'i a zuciyarta. Durum...taji dirowar mutum a kan icce, k'ara tasaki tareda zurawa aguje. Faruk kuwa me zaiyi inba dariya ba, seda taji sautin dariyarsa ta dawo baya, tana jifan shi da kallon lafiya.

"Yi hak'uri sarauniyata" sarauniya tasake maimaita tambayar. "Ehh sarauniyata, dama yau ce ranar dana d'iba zan amayar miki da abunda na dad'e ina raino acikin zuciya ta. Ummu salma. Alalhak'ik'a na dad'e ina son ki, so bana wasa ba I mean aure kenan idan nace bana wasa ba."

Kallon shi take kamar a mafarki, "ya.....y.....a faruk nice fa bingyal k'anwarka nake I'm too Young. Yaya ni bantab'a dating ba, bansan ya akeyin saba please mubar wannan zancen dan Allah kar sis raihan taji."

"Zatafi kowa farin ciki idan taji, naji dad'in samun zuciyar ki budurwa hakan zai bani damar koya miki salo iri_iri kala_kala na soyayya, bingyal kije kiyi shawara da zuciyar ki na baki daga nan har mu koma sokoto, kiba zuciyarki dama ta zab'i abunda takeso amincewarta ko akasin hakan.
   Ni nan zan jiraki daga yanzu har randa kika k'are karatu koda shekara nawa zamuyi zan jiraki ke kad'ai nake son yin tarayya da ita acikin rayuwar aurena".

"Huuuu....! Tasauke nun fashi "shi kenan yaya zanyi shawara nagode! Har cikin ranshi yaji godiyar.

Ya barta atsaye tana kallon sa takasa gasgata me take gani.

Faruk kuwa murna fal aranshi yacinye wancan d'an k'auyen acewarsa, mema bingyal zatayi da mai mata harda 'yaya uku. ai saini dai saurayi irinta.

Muryar Yusuf ta katseshi "kaikuwa murnar mene kake haka da har fuskar ka takasa b'oyewa? Faruk ya kyalkyale da dariya.
  
"Zan gaya maka idan komai ya kammala."

A wani dakali na k'ofar gidan suka zauna suna tattauna matsalae plaza d'in yusuf.

Da gudu ta fito tana haki batayi auneba tayi tintib'e da k'afar faruk aikuwa Sega ta ajikin Yusuf dikda arud'e take bata fasa fad'in "A'uzu billahi" abban salim anti raihan ce anti raihan! Yusuf ya zare ido yashiga girgizata "meya sami raihan d'in meya sami matata" gefe ya tureta suka zuba da gudu atare.

Kwance suka sameta ta kudundune azani tana rawar d'ari, faruk ya ambata "subhanallahi, raihan ina magungunan ki, bana gaya miki karkiyi wasa da magani ba , munfara shawo kan matsalar nan zaki maida mu baya. Ya juya kenan da niyyar komawa masaukin sa yad'auko injection d'in da ake mata Yusuf ya rik'esa.

"Ban gane inda maganganunka suka dosa ba dama tana shan magani miye lalaurarta ne" faruk ya fizge hannun Yusuf daga rik'on daya masa.

"Wannan ba lokacin magana bane, kabarni inyi aikina tukun".

Ba'afi minti biyar ba yadawo da allura yahad'a agaban su, ya umurce mijinta daya tadda ita zaune amata, haka kuwa akayi ana mata allurar ko minti ashirin ba'ayi cikakku ba ta tashi zaune.

Dik yanda Yusuf yazo su gana da faruk akan ciyon matar shi amma yak'i yarda se wani zillewa yake.

Hakan yasa ya kyalesu duka azatonshi ciki ne da ita.

"Um nikam meke damun ki ne haka kaddai kinje kin d'ebowa jikina wahala" laila ce ke fiddo wad'annan lafuzan masu kama da jirwaye.

Ummi tayi tari tace "koma meye ai ba laifinta bane mijinta yaka mata yashawar ceta suyi planing idan suna da buk'atar hakan" laila ta kwab'e fuska.

"Ko kad'an bashida laifi idan bata luradda  shi ba taya zai gane" raihan kam kasake tayi tana kallonta ita dai kam batada lokacin tsayawa wani challenge da ita abunda yake gabanta ya isheta.

Haka aka k'are bikin bada itaba, Yusuf kuwa ya manne da ita koya ta motsa zaice yadai?
   Laila dake ganin tasamu damar shigar da Amira gun Yusuf, sai takoma jin haushi ganin yanda yake lik'e da matarshi kamar gum.

Yaune suke ta shirye_shiryen zuwa gida, salim na tareda bingyal ta shirya shi tsab, tana jiran fitowar raihan.

Tana daga tsaye Amira tazo tajashi dasauri tasha gabanta "malama lfy atare zamuje fah" amira tayi tsaki tacigaba da tafiya.
   Bingyal ta fizgeshi tana huci.

Amira ta gyara tsayuwar ta "naga alamar yayarki kike tayawa kishi shi isa kike shigemin hanci , to ki kiyayeni ba sa'anki bace ni kina jina, baki isa ki hanani mu'amala da salim ba ina gaya miki."

Bingyal tayi dariya "nikuwa na isa har nayi yawa ke d'in banza, miy.....bata k'arasa ba amira ta wanketa da mari wanda seda ta dena gani na wani 'yan dak'ik'u.

Ta d'aga hannu zata rama kenan taji muryar laila na cewa "kull... Dan uban ki karki soma, Marin amira dai_dai yake da rub'ewar hannun ki, mafi sauk'in Abu shine kicire hannun ki da kanki."

A walak'ance take kallonta "ita amirar waye 'yar gidan uban wa ce kokuma yar gold ce, ni tafini ne da zata maran wlh koda sama da k'asa zasu had'u sena rama, wadda tayi nak'uda na ma bata taba samun hannu ba bare wasu banzaye.

"Ke dakata" cewar fatim "karkiso ki zagar mun uwa agabana se inyi gutsi_gutsi dake anan" bingyal tayi 'yar dariya "ni kuma ba nama bace bare kimun gutsi_gutsi mari kuma seku zab'i acikin ku wadda zan rama akanta" kan ta rufe baki Fatim ta wazga mata wani Marin atake fuskar ya kumbura tayi ja.

Ihunta ne ya fito da raihan da Yusuf tareda twins da faruk.

Tambayar yake meke faruwa kowannen su ya musu banza ya daka musu tsawa dasauri amira ta lab'e bayan laila, fatim kuwa idonta kyam akansa dama bawani tsoron shi take ba.

Laila ce tayi k'arfin halin cewa "son ka duba wannan mitsitsiyar yarinyar da nakusa jika da ita ace ta zageni" Yusuf ya kalli bingyal ta girgiza mishi kai alamar ba haka bane, kallon salim yayi ya kalli amira da rik'on da ta mishi atake yafara hararo meyake tafiya a gurin.

Raihan ta rungume  bingyal "auta gaya min wani shegen ne ya mareki billahillazi za'ayi masifa kan mubar garin nan" cikin kuka ta zayyane mata dikkan abunda yafaru, bata kai k'arshe ba Yusuf yayi tsalle ya dakawa Amira mari wanda yasa ta fad'uwa.

Raihan ko fatim tajawo ta aika mata nata marin tareda ingizata baya, ba laila ba hatta yusuf da twins sunyi mamakin marin da raihan tawa fatim agaban mahaifitar ta.

Ta k'ara da cewa "daga yau nawa kowa iyaka da yarona ni  nahaife shi nafi kowa can_canta da renonsa yana buk'atar kulawar uwa saboda haka Ku kyalemin yarona , ta nuna Amira , ki bari kishigo gidan tukun sannan ki kirashi da d'anki, tinda dai har yanzu ba'a gama yimiki kamfen shiga zuciyar ubansa ba.

Tana kai nan ta fizgo salim tarik'e hannun bingyal suka bar wajen.

"Tir k'ashi lallai magani gaskiya ne asiri tabbas ne,  wai yau nice ake gayawa sha tara agaban yusuf yakasa d'aukar mataki."

Yusuf ya dafe kai yarasa abun yi a dai_dai wannan lokacin.

Twins kuwa hakan da raihan tayi bak'aramun dad'i yamusu ba.

Faruk kanshi sun bashi haushi musamman Amira dayake ganin tausayin ta, yau gashi ta tab'o mishi haskensa.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang