FULANIN BIRNI

1.1K 65 0
                                    

🎄FULANIN BIRNI🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3⃣8⃣

Sai kuma wani sabon tattali yadawo kulawa yake bata ta musamman hakama iyayen shi barinma laila data hanata yin kowani aiki, ita ke shiga kitchen da kanta tana girka musu dukkan abunda sukeso, hakan yak'ara mata girma sosai a gurin Yusuf da iyayen shi.
   Ba wani wahala da cikin ke bata laulayi kuwa iyakaci in tayi na 2 month ta dena yi, sedai kasala da son kwanciya suka aureta bata iya komai sallah ma kan ta gama dakyar Sam bata son motsa jikinta seta wuni a kwance bata gajiba.
   Yau kam d'aukarta yayi sukaje shak'atawa daga nan suka wuce oasis inda nan ne ta kwaso ice cream da biscuit.
A hanyar su ta dawowa ne taga ya karya kwana sunbi ta layin su farin ciki sosai ya lullub'eta zataje gida tana kewar su sosai.
      Tin da ya tsaida mota ta fita aguje seda takai k'ofar shiga sannan ta tsaya ta tsaida kanta, tana k'ok'arin shiga ya cabko ta ya manneta ajikinsa "ya kina min wasa da lafiyar d'ana ko 'yata idan kika mun b'arna zan b'allaki ne" baki ta zunbure tana harar shi yamata d'alli a lips ta marairaice ''niko Allah sena rama" dariya kawai yayi yarik'e hannunta suka shiga ciki.
     "Oyoyo 'yar uwa rabin jiki nayi ke warki" hugging juna sukayi suna dariya.
   Yusuf ya girgiza kai dik inda mata suke se sunyi shirme.
   "baban unborn baby barka da zuwa" harararta yayi "se yanzu bayan da kika ganmu 'yar uwarki kika fara yiwa magana kunma mance dani" sorry   kawai  ina murnar ganinta ne."
   Bingyal ce ta zuro aguje tana oyoyo oyoyo ta fad'a jikinta tana murna.
   Wani irin cafka ya mata ya hankad'ata gefe yana huci "bakida hankali kasheta zakiyi ne meyasa wai bakuda nutsuwa."
   Tsit falon yayi ana sauraren sa surayya ce taje ta tadda ita tsaye goshinta har yayi tudu saboda tabigi center table, raihan ta kallesa "dear kana ganin meka aikata ji yanda ka jimata ciyo akan tagan 'yar uwarta tana farin ciki, kasan cewa bazaka tab'a rabamu ba abunda kake yiwa kar atab'a zan sake samun sa amma bazan tab'a samun k'anwa da kaina ba."
    "Good ya fad'a nikuwa da ki b'arar min da d'a gwara naji muku ciyo dukan ku."
   Bingyal ta hararesa "wlh banyafe maka ba kuma bazaka tab'a raba jini da tsoka ba" surayya ta rufe mata baki ita kanta abun yabata haushi shiru kawai tayi ganin mijin yayar suna.
     Juyawa yayi yabar falon. Dai dai nan gwaggo tafito jin hayaniya tayi yawa kallon su kawai take da d'ai d'aya takai idonta gun bingyal "subhanallahi" shine abunda bakinta yasoma furtawa. "Meya same aura ne waya ji mata ciyo haka"? Shiru sukayi bawadda ta iya cewa uffan, se bingyal ce ta daure tayi magana.
   "gwaggo bigewa nayi a table d'in nan nazo tarb'ob anti Raihan" daga raihan har surayya sunyi mamakin yanda tayi hankalin b'oye abunda Yusuf ya mata.
   Gwaggo taja hannun ta zuwa kujera tana mata sannu, ta dube su "kukuma mena wani cirko_cirko kamar marasa gaskiya" surayya tayi dariya "gwaggo bakomai fa muna tunanin kotaji ciyo ne da yawa."
    Wayar raihan ta d'au ruri tana dubawa tagan yusuf tayi tsaki ta maida wayar ajaka, ba'afi minti ukku ba yakira gwaggo da sallama abakinta suka gaisa yace "gwaggo raihan fa nakira bata d'aga ba" bata amsa ba ta mik'a mata wayar ita d'inma bata ce komai ba ta d'aga wayar a kunne "kifito mutafi" shine kawai abunda yafurta ya tsinke wayar, ta dad'e a kunnenta kafun tasauke ta, kana tacewa gwaggo zan tafi, bata tambayeta komai ba tace Allah kiyaye hanya.
  A motar ma bawanda yayiwa wani magana kowannen su da abunda yake sakawa aransa.
Suna isa tafito tawuce d'akin ta bai kulata ba shima yacigaba da lamuransa.
   4Pm ta fito d'aura girkin dare tasame shi a kitchen d'in har soma kammala macroni jellop gefe daya plantain ce ya soya.
   Tayi saurin rik'e hannun shi tacigaba da motsawa yasakar mata saving spoon ya wuce parlor yabarta nan seda tak'are kab ta gyara gurin ta hada mishi zobo wanda dama ta dafa tin jiya takai masa dining.
     Ko kallonta baiyi ba, tadawo har inda yake ta rik'e hannun sa "tashi  muje kaci abinci" banza ya mata yak'ara d'aure fuska itama ta b'ata fuska "wai miye haka ne?
   "Kinga malama bana ci kicinye kayanki kawai."
"Kamar ya bakaci bayan kai kadafa da kanka."
"Eh d'in banaci kawai ki kyaleni bana son takura."
"Shikenan na kyaleka."
A fusace ta juya zatayi hanyar d'akin ta mistakenly ta bigi k'afarsa segata takai k'asa tareda buga k'ara.
  Da gudu yayo kanta ya kwasheta yana kiran sunan ta jini ne ke mata zuba idonta alumshe.
   Mota yakaita yakira faruk a can suka had'e.
  Taimakon gaggawa aka bata Yusuf kuwa duk ya rikice yafara tunanin ko laifinsa ne dayake fushi da ita.
Ba jimawa faruk yazo yana murmushi "congrat my friend ba abunda muke tsammani bane" wata ajiyar zuciya yasauke tareda hamdala.
   Cigaba da kula da ita sukayi kusan tsawon wata biyu kenan saboda wani bincike da suke kanta.
   Bingyal tazama kukun yusuf baya cin girkin kowa se nata Kullum ita ke musu lunch and dinner.
   Asibitin kuwa Kullum acike take da yan dubiya ba abokan Yusuf babare danginta da nasa.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora