FULANIN BIRNI

1.1K 67 7
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 6⃣2⃣

Hello ummi barka da wuni"
"Wunin gidan ku. Eh nace wunin gidan ku, wato kamaida ni abokiyar wasan ka, ko. Har yaushe zan kai ina maka tinin kaje ku sasanta da yarinyar nan, toh wlh kaji da kyau muddin kace zaka bijire mana to kuwa gab nake dana yafeka, zan iya rayuwa babu kai 'yaya nawa ne dani."

"Subhanallah! Ummi dan Allah kiyi hak'ur karki mun baki in lalace. Wlh zanje yanzu maaaaa...dif ta tsinte wayar.

Juyar da motarshi yayi ya d'auki hanyar gidan su bingyal.

Faruk ya hangosa a lokacin da yake k'ok'arin shiga ta layinsu, shima juya tashi motar yayi yabi bayansa.

Ba wata_wata yashiga gidan batareda yatsaya tura d'an aikeba, ya bud'e k'ofar falon.

Tim kakeji ta fad'o ajikinsa tana sheshshekar kuka.

Abdul biyeda ita yana zuba mata belt, dasauri Yusuf yasha gaban shi.

"Haba babban yaya, duka fa bashine zaiyi maganin abun ba, bazai sata tayi abun da akeso ba sai dai yak'ara tinzirata. Ba abunda take buk'ata a yanzu zama da lallashi."

"Wannan da kake gani batada mutunci, Dama kabarni da ita, lallashi sau nawa akayi, wai ita mai kunnen k'ashi, nace kar ta sake zuwa makaranta shine ta lallab'a taje wai sunyi text, to  uban text d'in."

"Ahhh... Haba kaikuwa ace a had'e mata zafi biyu gana matsi gana rashin school, yakamata abarta taje makaranta, hakan zai rage mata damuwa sosai."

"Duka bazai mata ba ko kad'an, ina zata iya d'aukar wannan jarumtar taku ta sojoji, ai saika jimata ciyo."

"Ba gwara inji mata ciyon ba tinda batada mutunci.".

"A'a baza'ayi haka ba, karfa ka ballamin amarya akai min ita da ciyo ajiki. Human rights ce kawai zata rabamu da kai."

Jifa da belt d'in hannun sa yayi yawuce yabasu guri.

Hankad'ata yayi gefe yace "Me na wani manne min ak'irji, harda su lafewa, karkiyi tunanin na ceceki daga hannun yayanki k'azamar zuciyarki tabaki wani Abu.

"Ko kusa ina mai baki shawara kiyi dik yanda zakiyi ki kaucewa aurena, in bahaka ba wlh, bak'ar azaba zakisha, gidana ba gurin zaman k'ananun yara bane. Ancuceni wlh ji wannan kwailar taya zan iya had'a jiki da wannan babyn."

Dikda tana cikin kukan dukan da Abdul ya mata hakan bai hanata bashi amsa ba.

"Mezanyi a wani jikinka, Sannan ni banida k'azar zuciya sedai kai.
Kaine yakamata kayi iya yanda zakayi ka kaucewa aurena domin wlh bazaka tab'a samun nutsuwa ba.
Ni ba yarinya bace, kasan da wannan.
Sa'anan wlh bana fatar k'addarar dazata had'a jikina da kai, yo ad'aure kashi ko a b'ata igiya."

"Wow! K'arfin halinki na burgeni, zaki maimaita abunda kika fad'a muddin kika shigo gidana."

Tsaki tayi tabarshi a gurin tawuce d'akin ta.
Faruk take ta k'ok'arin kira amma wayar akashe tayi texts yafi nawa ba reply, hankalin ta yasoma tashi, kaddai yayi fushi ya barwa Yusuf d'in inaaa bazai yu ba.

Cikeda girmamawa ya gaida gwaggo da anti salma.
Sun tambiye shi bawata matsala gameda bingyal, yace bakomai lafiya lau suke.

"OK bari na kirawo maka ita kuyi sallama."

"Yauwa anti kirawo ta ina son in wuce."

Kukan dai ta sameta tanayi, ta girgiza kai "Allah ya shiryeki auta, idan kin gama kizo kuyi sallama da Yusuf."

Har taje tadawo bata fito ba.
"Ke auta wlh zan b'ata miki rai wato rainin hankalin naki har ni zaki yiwa ko, to kiyi gaggawar ficewa daga nan kafun rayuka su b'aci."

Da gudu ta fita tana share hawaye.

"Gani lafiya?
Ya juyo yana mata kallon zaki san ko ni waye.

"OK auta sai nadawo ki kula da kanki, zan kawo salim d'in."

Mamaki yacikata da jin kalaman sa.

Baki bud'e tana kallon sa. Har saida taga surayya ta wuce sannan ta gane nufinsa.

Shi kad'ai a parlor yashiga duniyar tunani, yaji anata zanbga knocking wanda da alamu andade anayi baiji ba.

"Yes shigo ciki."

Mai gadi ne hannun sa rik'eda farar takarda ya mik'awa Yusuf.

"Wannan kuma fa. Ta mecece?

"Ranka yadad'e, Faruk ne yabada akawo maka."

"Faruk! Yana ina" yafad'a tareda mik'ewa tsaye.

"Ranka ai ya wuce."

Bai jira k'arasawar mai gadi ba, yafita aguce.

Baiyi nasarar cimmasa ba, domin ko k'urar sa bai hango ba.

Haka yadawo yana citsan yatsa.

_Aminci agareka, ina fatar yarona yana lafiya._
_Yusuf ban tsammaci haka agareka ba. Ban tsammaci yaudarar abota, ko cin amana daga gareka ba._ _Nad'aukeka amatsayi na d'an uwa rabin jiki wanda yafi aboki_ _Ashe bahaka nake agareka ba._ _Tin farko daka gaya min kana son bingyal bazan yarda nayi nutso acikin kogin santa ba. Amma babu komai ni bazan iya jayayya da kai ba. Nabarmaka auta. Har abada_.
_Har abada yusuf! Har abada!_

O" shiit!!!

Car key d'in shi yad'auka yafita da gudu.

Ko da ganin shi mai gadin gidan yayi saurin wangale mishi gate.

Gudu yake bana wasa ba. Har ya iso gidan su faruk, bai wani tsaya Shiga da motar ciki ba, ya ajiyeta waje. Tareda baiwa mai tsaron gidan ajiyarta.

Sallama yayi yashiga gidan kasancewar gidan yazama kamar nasu.

Kamar faruk ta taryeshi da murna.

"Mama faruk fa?
"Aw ai nazata daga Airport kake gurin rakashi."
"Mama airport fa kikace?
Dasauri yajuya har yana tintib'e, da Cotton d'in gidan.

Hanyar airport ya d'auka dasauri, gudu yake har ba fitar hankali, duk wanda yaganshi sedai ya kauce hanya.

Yakai sokoto camp. Kenan yaji tashin jirgi,
"Yah ilahi" ya furta tareda d'ora kanshi motar, ya dad'e ahaka kafun yasamu k'arfin da wowa gida, wannan karon a slow yake tafiya, saboda bashida wani k'arfi ajikinsa.

Kwana biyu baifito daga gidan sa ba, dagashi sai salim.

A yaune yake da niyyar zuwa gida domin ya dubi iyayen sa.

Tin randa akayi masa zancen auren  bingyal baisamu kwanciyar hankalin komawa gurin amira ba bare yamata waya.

Ita ko amira tafara jin tsoro atunaninta ko yayi fushi ne akan abunda ta mishi, atake tafara tunanin bata kyautawa kanta ba, lokaci guda  kuma ta jaao wayarta ta kirashi.

Yana k'ok'arin saka takalmin sa kiranta tashigo, yayi murmushi ya d'aga tareda komawa zaune kan kujera.

"Ya dai matar Yusuf"
Wow! Har cikin zuciyar ta taji saukar wannan Kalmar, ta bud'e idonta tasake lumshewa.

"U'nnn barka da yau, kwana biyu"
"Yauwa matar Yusuf, kiyi hak'uri fa, kin jini shiru two days. Wasu abun ne suka sha gabana."

"Bakomai hope kana lafiya. Da yarona?
"lafiya lau"
"Yaushe zaka kawo min ziyara"
"Matar Yusuf yaushe kike son inzo?
"Umm idan nace yau banyi Sauri ba"?
"Shikenan zanzo zuwa 5pm"
"Toh sai kazo bye."

Ihu da tsalle tayi tana dariyar farin ciki mai had'e da kuka.

Yau Yusuf d'in ta ne yake kiranta da matarshi. Yusuf ne yake sassauta murysr shi saboda ita.

Lallai mai hak'uri yakan dafa dutse har yasha roman sa, dik Wanda baiga amfanin hak'uri ba to kad'an yayi.

Yau gashi kamar amafarki ina waya da Yusuf amatsayin masoyiyar sa, "oh Allah na nagode maka daka nunamun wannan ranar.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIحيث تعيش القصص. اكتشف الآن