SALMA TA DAWO

1.1K 83 5
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

ASISI B. ALEEYU

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 90

Hasbullahu wa ni'imal wakil.
Shine abunda maigari ya keta maimaitawa.

"Duniya ina zaki damu? Duniya abun tsoro , duniya makaranta duniya gidan wahala"
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.

"Alhamdulillah da Allah yasa abun yazo cikin sauk'i haka.

Yanzu abunda za'ayi zan bata ayatush shifaa ta karanta da kanta ta tofa acikin ruwan zam-zam ko ruwan sama ko ruwan rijiya.

Za'a zuba yayan magarya guda bakwai busashshen sai a nika.

Ta rik'a sha safe da yamma tana shafe jikinta aguri mai tsarki.

Mu'awazatain.
Sune suratul Falaq, Nasi, Ahad. Sau uku uku.
Sai suratul fatiha, Ayatul khursiyyu, suratul A'a raf Aya na 106-na122
Suratul yunus aya na 79-82
Suratul kafirun
Sai a k'ara da Allahumma rabban Nasi az'hibli ba'as ashfi wa antash Shifa laa Shifa'a  illah shifa'uk shifa'un laa gugadiru sakhma sau ukku.

Za'a iya karawa da.
Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uzika wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka bismillahi urkika. sau ukku.

Ba sihiri ba koma wane irin asiri ke yawo ajikinta zai karye ko tantama babu.

Sati d'aya tana shan ruwan, tana shafe jikinta dashi sau biyu a rana.

A hankali komai na waye mata komai yana dawo mata sabo.

Zaman ta ya koma gidan maigari hannun anti samira. Ita ke kula da ita.

Zaman su bazai yu agida d'aya da faisal ba.

AGURGUJE......

Tinda ta tashi da safe take jin ciyon baya da k'afa, tana daurewa ne kawai saboda kada anti samira ta shiga damuwa.

Tun tana daurewa har ta kasa jure azabar da take ji, a hankali ta rarrafa ta shige bedroom d'in anti salma.

Shigar ta keda wuya taji wani irin nishi mai k'arfi yazo mata, dasauri ta dafe kan gado tarike gam, gumi sai tsasstafo mata yakeyi.

Hasbullahu wani'imal wakil ta rik'a maimaitawa har Allah yasa jinjirin ya fad'o.

Daidai shigowar anti samira yafara tsala Ihu.

Hamdala tayi ga Allah tana k'ara jinjina wa bingyal irin k'ok'arin da tayi tana shirin d'aukar Babyn taji bingyal na salati da Kiran ubangiji.

Yunk'uri take iya k'arfin ta, fiye da minti ashirin tsakani sa'annan baby gal ta fad'o duniya.

Nan ta zube tana hamdala tana mayar da nunfashi.

Tsabar murna anti samira rudèwa tayi tarasa wanne zata kama.

Wayar faisal takira ta shaida masa yazo da likita a duba su.

Cikin k'ank'anin lokaci aka gyara su harda mai jego datake fama da jiki.

Faisal ji yake kamar yaransa ne sai tambayar likitan yake me za'a basu me zasu fara ci.

Sosai ake kula da ita da yaranta wanda ranar suna sukaci sunan raihan da salim. dikda bingyal bata san da rasuwar salim ba.

Watan su bakwai bingyal tafara shirin komawa gida domin tasamu dikkan wasu hujjoji na tinkarar gidan da su.

Yaranta kuwa gwanin sha'awa dasu har sun fara tattakawa idan ka gansu kamar yan shekara d'aya.

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now