FULANIN BIRNI

865 59 8
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 5⃣7⃣

Faruk kanshi ya saduda ya tabbatar wannan karon dik iya iyawarsa bai isa ya ceto rayuwar raihan ba, domin kuwa wanda yafi mu Santa yana gab da d'aukar rayuwar ta.

"Yusufffff.....!!!

Wani irin fad'uwar gaba da sanyi tareda kasala suka sauka lokaci guda a jikin Yusuf.

Daga lokacin data furta Yusuf tafara wani kakarin mutuwa jijiyoyin jikinta suka fara saki haske da kyalli kawai take, tamkar ana k'ara sabunta ta.

"Raihan!

Kalmar daya furta kenan tareda mik'ewa tsaye ya nufi world d'in da take.

Abokanan shi uku, Sadiq, Zahra tareda umar, suka bishi da kallo.

Zahra ne yafara tambayar lafiya kuwa kodai ciyon ya motsa naga yatashi lokaci guda tareda sunan ta abakin sa.

Sadiq yace "gaskiya da alamar tambaya" umar kuwa tsaye ya tashi yana fad'in "ai semu bishi bazama zamuyi ba."

Lokacin daya isa gurin bai tsaya Neman izini ko sauraren nurses d'in dake bashi umarnin cewa  kar ya shiga.

Da k'arfin sa ya bud'e ganbun d'akin, "Raihanaaaa!!!

Murmushi d'auke Afuskarta ta furta "Yusuf mijinaa"! Ya k'arasa gurin da take ya rik'o ta.
"Raihana ta"! Ya fad'a fuskar sa d'auke da matsananciyar damuwa.
Tasake fada'ar.
"Yusuf"!
Tareda hawayen k'unci  da d'acin rabuwa da mijinta.

Jini ne yake fitar mata abaki dik da haka bata fasa magana ba.

Yusuf ya yak'ara rikicewa.

"Wai ba doctors ne dan Allah. ina faruk kuyi wani abu kar ta mutu ya Allah."

Ciki_ciki take magana wanda sautinta yake fita dakyar d'aya bayan d'aya.

"No Yusuf ka....kahhhh kahhh barrr su."

"Yusuf mijina"!
"Yusuf mijinaa"!

"Na'am Raihanataa"!

Muryarshi har rawa take yi.

Dakyar ta iya kai hannunta gun fuskar shi ta shafo ta tana masa murmushi kai da gani kasan na bankwana ne.

Hannun ta ne yayi k'asa yafad'i.

Bin hannun yayi da kallo yana zare idon sa.

Gabansa dai falllll fallllll yakeyi.

"Yusuf mijinaa"!

Wannan karon bai amsa mata ba. Sai ido dayake bin ta dashi tareda fad'uwar gaba.

Wanda har doctors da nurses da suke kallon su, suna iya hango bugawar zuciyar sa.

Faruk yayi k'ok'arin tayarda Yusuf kan raihan amma ina se buge mishi hannu yayi. Kallon sauran doctors d'in yayi dasauri suka yi kan Yusuf domin tayarda shi amma fa dik yawan su watsar dasu yayi.

Hakama abokan shi da suka zo dik k'ok'arin su sun kasa rabashi da gurin.

Faruk ya kasa tsayuwa da k'afarshi, hakama sauran doctors d'in dik sun tausaya wa wad'an nan masoyan.

K'ank'amesa tayi jikinta sai kakkarwa yakeyi. "Yusuf mijinaa"!
Kalmar ta ta k'arshe itace ( LAH ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR RASULILLAH )

Atareda Yusuf suka idar da wannan Kalmar.

Bingyal kuwa ihun Yusuf ne ya k'ara mata k'arfi ta taso da gudu ta na kallan su.

Kuka sosai takeyi bata masan metake furtawa ba.

Umar ne yafita yaje gurin da su gwaggo suke yace musu suzo raihan nason ganin su daga haka yafice daga asibitin.

Gaban gwaggo yayi wani irin fad'uwa haka kawai taji bata gamsu da wannan kiran ba.

INALILLAHI WAH INNAH ILAIHIR RAJI'UN

KULLLI NAFSIN DHA'IKATUL MAUT

Wallahi tallahi kowace rayuwa sai ta d'an d'ana mutuwa, babu makawa

Raihan ba tayi saurin mutuwaba.

Ni Asiya
Da
Ke/kai masu karatu bamuyi lattin zuwa lahira kamar yanda raihan batayi sauri ba, hakama mu da muka tsaya bamuyi nawa ba.

Dukkan su kuka suke ba mai lallashin wani in kacire laila data fiddo wayarta tana bugawa mutane ciki kuwa harda dadyn Yusuf.

Atare suka iso da baffa.

D'an guntun hawaye ne kan fuskar baffa. Wanda zuwansa keda wuya yayi gurin matar sa gwaggo domin yasan irin halin da zata iya shiga.

Rungumeta yayi yana lallahin ta acikin harshen su na fulatan ci.

Ummi kuwa rungume twins tayi tana kuka fatim ce gefe d'aya rikeda salim wanda shima kukan yakeyi ganin kowa nayi.

Dady kuwa direct d'akin da raihan take yaje.

Baiyi mamakin ganin Yusuf rungume da ita ba.

Saima tausayin sa dayaji.

"Yusuf hak'uri zakayi bamuda ikon canza wannan hukuncin."

A yanzu ba abunda take buk'ata sama da addu'oin mu.

Sai a lokacin Yusuf ya juyo babu ko d'igon hawaye akan fuskarsa, sai dai idonsa da sukayi jajir kanshi ya fiddo manya_manyan jijiyoyi rud'u_rud'u.

"Dad ta tafi fah, shikenan bazata k'ara magana ba bazata k'ara yimun murmushi ba, bazata k'ara yin komai ba."

"Haka ne Yusufah bazaka sake ganin ta ba, kayi hak'uri kayi tawakkali insha Allahu zaka samu makaman ciyarta".

Dasauri ya juyo yana kallon sa "a'a dad babu tabiyunta a duniya babu wacca zata maye gurbinta aziciyata."

Gurin da su gwaggo suke ya nufa yana kallon su da d'ai d'aya.

K'afar gwaggo yarik'e yana ta zuba sambatu.

"Kingani ko gwaggo raihan bata mana adalci ba, ta tafi ta barni nida salim.

"Gwaggo indai aljanna atafun k'afata yake wlh na d'aga mata zata wuce, gwaggo ta mutu a yau litinin ranarda manzonmu ya rasu, ta rasu tana ambaton Allah, raihan 'yar aljanna ce."

Dikda k'uncin da baffa yake ciki bai hanasa murmusawa ba domin jin wad'an nan daddad'an kalamai daga bakin Yusuf.

"Ummi sirikar ki tabar ki tayi tafiyar ta" gwaggo CE tayi k'arfin halin cewa yakamata kumaida Yusuf gida.

"Ba inda zanje" abunda bakin sa yafurta kenan tareda mik'ewa atsaye da nufin yaje gurin umminsa, wani duhu_duhu yake gani atake yafad'i a gurin luuuu sai k'asa yafad'i somamme.




ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now