FULANIN BIRNI

1.2K 63 13
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE  6⃣5⃣

Dubbanin mutane suka shaida d'aurin auren Salma Adam & Yusuf kabir.
Surayya Adam & Faisal Bashir.

Tsayawa bayyana irin farin cikin da baffa yakeci a Yau zai zama b'ata lokaci, ku k'issima akanku. Irin farin cikin da uba zai shiga aduk lokacin da akace gashi ya aurar da 'yarsa ga wanda ya yace.

Tinda aka shafa fatiha Gabanta ke faman bugawa.
Hawayenta sun k'afe. Yau kam ido kawai take bin mutane dasu.

Dik wani motsi sai yesmin ta tambaya lafiya.?

Tsantsararren lalle aka mata kalar Dubai. haka ma kanta yasa k'ananun kitso mai ban sha'awa.

K'arfe biyu baffa yayi kiranta zuwa restroom d'in shi.
Yesmin ta rakata tareda anti salma.

Suna kaita suka juyo.
Baffa ya dakatar da yesmin da cewa, "A'a 'yata zoki zauna nan. Ya mata nuni da gurin da bingyal take.

"Salma.!

"Nakiraki ne domin in k'ara yimiki nasiha, akan wacca nake kullum. Nasan nayi miki laifi ban tintibe zuciyar kiba, amma kisani zakiyi alfahari da wannan zab'in nawa, zakiyi farin ciki insha Allah.

    Salma wlh bazakiyi dana saniba. Nasan da wanda na had'aki. Ina rok'onki da ki kasan ce kamar sauran 'yan uwanki, kamar mahaifiyarki, dik abunda mahaifiyar ki take yimun shi zakiyiwa mijin ki, kirik'e tarbiyar da muka d'oraki akai.

"Dan Allah salma karki yarda dai_dai da rana d'aya yaka womin k'arar ki, dan Allah, kiyi taka tsan_tsan da b'acin ran mijinki, idan kikayi masa biyayya har mu zamu amfana da ita, kibishi kamar matar nan dataje gurin malamin sunna cewa yayi mata magani domin ta mallake mijin ta, sai wannan malamin yabata kitse ta kaiwa zaki yaci, karon farin dataje kai tsaye sai zakin yayo acikinta kamar zai cinyeta ta dawo aguje, ta fad'awa wannan malamin. sai yasa ke maida ita cewa " kije ki basa yaci" haka takoma zuciyarta na cike da tsoro.
      Wannan karon sai ta ajiye masa a inda bazai cimmata ba. baya ganin waya ajiye mishi kitsen.

Kullum wannan matar haka takeyiwa zakin nan. Baya ganin Wanda yake kawo masa kitsen nan, sai dai yaganshi kurum yacinye.

Da haka har ta fara bayyana kanta. Zata kawo masa kitsen yaganta batareda ya tab'ata ba, har akazo tana isa agabansa tana kai mishi yanaci.

Sannu_sannu  zakin nan yayi sabo da wannan matar. Har takai idan taje kaimasa kitse tana wasa da shi tabashi abaki yaci, har sukayi sabon da yaganta yake zuwa gurinta, koda bata kawo masa komai ba.

Wannan matar ta koma gurin malamin nan mai hikma tagaya mishi cewa fah zaki dai sun shak'u har tana jin bazata iya rabuwa dashi ba.

Sai wannan malamin yayi hamdala yayi dariya yace "yake boyar Allah kije kibi mijinki sau da k'afa kamar yanda kikabi wannan zakin tin kina tsoronsa kina b'oyewa har kika fara bayyana kanki. Yake boyar Allah tinda har zaki iya hak'ura da jarabar zaki da muguntar sa kuyi sabo inaga mijinki da yake jinsi d'aya dake, inaga mijinki daya kasance abokin rayuwar ki, masoyinki uban 'yayanki ki koma kibi mijinki" Allah sarki sai wannan matar tafashe da kuka.

"Salma iya wannan kissar ta isheki kiyi koyi da wannan fad'akarwa. Amma zan k'aramiki da wata k'issar. Wata boyar Allah wadda taso tazarce nana fad'ima ga kyautatawa mijinta.

Annabi yacewa nana fad'ima idan baki dage ba akwai wata b'oyar Allah dazata rigaki shiga aljanna. Nana fad'ima tace wacece ya rasulillah SWA.? Annabi yace "gidanta yana gefen madina."

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now