8

511 70 8
                                    


Tana cikin wata na karshe da zata kare iddah, wani yammaci tana zaune a kofar madafi, tankaden garin masara da za'ayi tuwo ta keyu. A cikin dakin girki mama lili ce take kokarin hada miya yayin da inna hadi take zaune tana kulle kullen kubewa, kuka da gishirin da take sayarwa. Sai su ka tsinkayo sallamar larai kanwar mal umar mahaifinta, wadda take aure anan garin dange. Bayan an gaisa ta zauna akan tabarma da inna hadi take zaune, amina ta kawo mata ruwan sha da lemon zobo da mama lili ke saidawa, sai cewa tayi, "yanzu inna haka za'a sa ido auren Amina ya kare ba tare da an nemi sulhu a wajen mijin ba? idan ba tayi zaman aure ba me za tayi?" tace "to larai ai babu mai laifi sai ubanta gaya nan." Malam umar da ke zuba abinci ga dabbobi bai waigo ba balle ya tanka, sai inna ta ci gaba da fada, ta inda take shiga ba anan take fita ba, larai sai fadi ta keyi, "kiyi hakuri inna, kai kuma yaya kayi wani abu akai, kasan halin amina ba Magana ta keji ba, ko wani mijin ta aura sai ta kara aikata irin haka tunda ka goya mata baya." Amina ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba, mama lili ce tazo ta ja hannunta zuwa daki.

Duk rashin Magana irin na mal umar, sai ya tako yazo gaban inna da larai ya fara Magana, "larai ina ce zuwa ki kayi ki gaisa da mu, ashe abinda ya kawo ki daban, kinzo zuga da hada fada. To ki sani idan ma shi abu ya turo ki, yayi kadan, saboda yasan yadda a kayi ya saki amina. Kuma wallahi ko bayan raina ban yarda amina ta kara zama da abu ba!" Inna tana jin haka tace "ai na sani wannan ja'irar yarinya sai ta hada ka da kowa Babba. To ni kuma zan fada maka ba zan zauna da ita ba, sai dai ko in koma wajen dangina". Haka dai inna taci gaba da fada tana goyon bayan larai kuma tayi tsayinta akan ko ita ko amina dole daya ya bar gidan. Mal umar kuma takaicin larai ne a ranshi, yana ganin har da zugarta hakan ya faru. Ko banza mijinta abokin abu direba ne.

Dagakarshe shi da mama lili suka bata hakuri yace "kiyi hakuri inna zata bar gidan nan, amma ke larai ki sani Allah zai bi ma yarinyar nan hakkinta da nawa idan bamu yafe miki ba." Larai ta fice da kuka tana fadin "ba sai ka yi min Allah Ya isa ba yaya, ga ka nan ga amina, kuma wallahi inna idan bata koma dakinta ta bari kun zauna lafiya ba, zan zo gobe in tafi dake ki zauna a wajena."

Kafin mal umar ya tafi masallaci sallar magrib, ya shiga dakin da amina take tare da kayanta da aka dauko daga rariya, ta hada kai da gwiwa tana ta famar kuka. Murya cikin damuwa ya kira sunanta, ta dago kai tana share hawayen da ke zuba daga idanunta. "ki kasance cikin shiri, zan zo in tafi dake inda zaki karasa iddah Insha Allah kafin inna ta sauko, Amina kiyi hakuri da rayuwa, tun dazu lili take ta baki baki ya kamata ki daina kukan nan baya maganin komi sai karin damuwa. Ga kannenki duk sun shiga damuwa ganin kina kuka" Amina ta share hawaye ta dauki kofin ruwa dake gabanta ta sha. Daga nan yayi ajiyar zuciya ya fita zuwa masallaci.

A daren ranar amina bata kwana gidan ba sai gidan malama luba ta kwana tare da kayanta na bukata. Washegarin ranar mal umar yayi tattaki har garin Sokoto, a tashar mota bayan ya gaisa da tsofaffin abokan sana'arsa, sai ya samu ya kebe sannan ne yayi waya da mami, akan tana so zai zo ya ganeta.

Maganar daya kwana da ita cikin ranshi ya keta addua Allah Yasa fadinta alhairi ne. kai tsaye daga tashar mota ya wuce ofishin WH dake titin abdullahi fodio. A ofis ya same ta suka tattauna. Yayi mata bayanin halin da ake ciki sannan ya nemi alfarma akan a sa sunan amina cikin tallafin da ake bayarwa na karatun boko, kamar yadda ita amina tayi mishi bayani cewa har an sa sunanta a cikin irin wannan tallafin kafin ta baro garin rariya. Ya kara da cewa "idan akwai makarantar kwana kuma ina rokon arziki ayi mata hanya ta shiga, ni dai buri na tayi ilimin da zata iya tallafar kanta kafin Allah Ya fito mata da miji."

Bayan dogon nazari, wanda ya sa mal umar a cikin fargaba ko yayi ba daidai ba, Mami tace "tabbas muna bayar da irin wannan taimako musamman a kauyuka, haka nan amina ta cancanta a saka ta aciki kamar yadda ta samu damar shiga tun farko. Mal umar ina so ka zauna ka jira ni anan ina zuwa."

A cikin ainihin ofishinta ta shige tayi waya da alhaji adam maigidanta, daga nan ta fito tace "mal umar babu damuwa, zamu zo har garin dange tare da abokan aiki da zasu je yin training da fadakarwa ga mata, kuma zan dauko amina. Kasa a ranka Insha Allahu Amina za tayi karatu, idan har tana da niyya da sha'awar yin haka, musamman idan mun samu goyon baya da amincewarka zata zauna a hannuna tayi karatu har tayi Aure da yardar Allah." yayi godiya, har ya rasa abinda zaya fadi ta gane irin farincikin da yake ji. Ko banza ga ba yada yawan Magana ba. Su kayi sallama, ya wuce.
**********************

Ranar da amina ta dawo da zama gidan Alhaji adam, inna jummai ta yi murna sosai da dawowarta, naana a lokacin bata gida taje gidan su kausar tana shigowa ta taradda da naana a palo tare da mami sai tayi tsalle tare da dan ihunta tana murnar ganinta. Daga bayansu taji wata murya tana fadin "keeee! Wane irin sakarci ne wannan zaki cika mutane da ihu" sai taga naana ta nutsu bayanta turo baki tare da fadin "yaya imam kaga aminar da nake fada maka" wanda aka kira imam ya kalleta sau daya, tare da fadin "sannu." Amina ta gaida shi a ladabce.

Kalar jikinsu kusan daya da naana, wato kalar mami, yana da haske kadan, ainihin kalar chakulet. A hasken fata daga shi har mami naana zata dara su kadan, amma bayan kalar fata sam baya kama da mami ko naana. Sai a idanu da su kayi tarayya su duka ukun. Ta gane shi tabbas shine yayan naana mai kama da alhaji lema kamar yayi kaki. Dogo ne mai jiki kadan da fadin kafadu da saje kwantacce kamar yadda gashin kansa yake, hakanan farkon haduwarka da shi zaka dauka baya da fara'a. Yana sanye da kananan kaya shirt kalar siminti da bakin wando. Ya ajiye wata jaka karama ya ajiye kusa da mami tare da gajeren bayani sannan ya juya ya fita.

A daren ranar ta na zaune a dakin inna jummai sai naana ta shigo tace, "wai ba ki jin bacci ne amina?" tayi murmushi tace, "da saura" "To bari mu taya jummai hira kadan sai muje dakina mu kwanta." Jummai tace "naana manya, wato zaki dauke min abokiyar hira, to mami ta san cewa tare za ku kwana?" "eh ta sani inna jummai."

Zaman amina a garin Sokoto a gidan Alh Adamu lema, a karkashin kulawar mami tare da canji mai yawa. Bayan dawowarta ta da kwana uku, ta fara zuwa center da WH suka bude saboda mata da suka fadi jarabawar WAEC, ko kuma wadanda suka bar makaranta na wani lokaci, daga baya suna so su koma. Akwai ajin darasi (lesson) akwai na remedial. A ajin darasi aka sa Amina, za tayi wata goma sha takwas. Idan ta dawo gida naana tana taimaka ma ta akan abubuwan da ake koya mata a center. Da yake ita a lokacin suna hutun jami'a. har littafan da ta kare sakandire shekarar da ta gabata duk ta ba amina. Suna haduwa da imam, kuma a tsakaninta dashi gaisuwa ce ta mutunci, kadarn kadahan.

Ranar wata alhamis ta dawo daga lesson, a dakin naana, tana kwance a kan daya daga cikin tagwayen gadaje biyu da ke cikin babban dakin, sai madibi, kwabar ajiye tufafi, da teburin karatu, a gefe hade da kujera biyu kanana A zuciyarta ta tuna yadda mahaifinta ya fada mata su kayi da mami. Ta fara tunani, ko yaya zamanta zaya kasance anan? sai tunanin rayuwarta yazo mata tun daga kuruciya, wanda ta gani da wanda ta samu labari daga malama luba, uncle musa har ma da tsohon mijinta Abu direba. Ta tuna asalinta wanda yake cike da gata da rashinsa, maraici na rashin uwa mahaifiya. Sai ta fara tunani tana hawaye........

Taqabbalal_lahu_minna_wa_minkum_ajma'in!
May the Almighty Allah (SWT) accept our efforts as acts of Ibadah and May He (Allah) also continue to bless us.
Happy Eid_el_Kabir

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now