4

712 79 0
                                    


A ire-iren kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) dake shiga kauye da karkara don bayar da tallafi da kawo ci gaba ga rayuwar mutanen karkara, akwai kungiyar WOMEN HELPERS (WH) da ta ke da reshe a jihar Sokoto, garin rariya dake a karamar hukumar dange shuni,  yana daga cikin kauyukan da aka zaba don taimakawa mata da basu tallafi akan ilmi da sana'oi.

Tun lokacin da kuluwa take a raye kungiyar ta kai ziyara a garin, a lokacin tana dauke da tsohon cikin amina karamar diyarta, lafiya tayi mata karanci. A ranar da aka kira mata zuwa fadar hakimi zasu gana da kungiya, kuluwa tana kwance a dakinta, amina ta kawo mata koko da ta dama tun safe, tana cewa, "maman kasim ki daure ki sha, yanzu fa karfe goma da kusan rabi, amma baki karya ba." Bayan ta sha kunun kadan, amina ta dauko zancen kira da akeyi musu a gidan hakimi. Tace, "amina ki je kawai Allah Yasa a dace ni kam ba zan iya shiga jama'a ba, a haka. Idan da rabo ke sai ki amfana da abinda su ka zo da shi."

Da misalin karfe sha daya, amina da sauran matan unguwa da kiran ya shafa suka rankaya zuwa gidan hakimi, a nan wakilan kungiyar WH da aka turo suka gabatar da kansu, kafin a fara tattaunawa da matan sai da suka kara tambayarsu idan sun zo ne tare da yardar mazajensu da amincewar hakimi, bayan sun samu tabbacin hakan, sai suka fara daukar sunaye da karin bayani akan aikin da su keyi a karkara. A nan ne suka lura cewa amina tayi karatun boko kuma tana da kaifin basira duk da kasancewarta mai karancin shekaru a cikin matan.

Ta taimaka musu kwarai wajen tattara bayani, ba a kanta kadai ba har akan sauran matan. Daga karshe aka dauki sunayensu da cewa za'a waiwayesu bada dadewa ba.

Bayan 'yan watanni kungiyar ta sake waiwayosu kamar yadda aka fada musu, wanda ya kasance bayan rasuwar kuluwa ne. Anyi bayani cewa tallafin kashi biyu ne, akwai bangaren koyar da karatu da rubutun boko kyauta tare da biyan dalibai alawus, inda za a bude azuzuwa mataki mataki. Kashi na biyu kuma tallafin da za a ba masu sana'a ta hanyar bayar da jari bayan an bude musu kungiya. Da yake ita amina ba ta kowace irin sana'a, a bangaren karatun a kayi ma ta rajista.

An kafa azuzuwan karatun, anyi rajistar dalibai mata ciki har da amina, masu sana'a kuma an tsara a kan za'a dinga zuwa yi musu bita akan yadda zasu tafiyar kuma su kayatar da sana'oinsu sau daya a kowanne sati. Idan suka bi ka'idodin kungiya za a basu jari su na kudi ko na kayan aiki.

Bayan wani dan lokaci kungiyar ta kawo ziyarar gaggawa a garin rariya, a karkashin jagorancin babbar shugabar kungiyar ta jiha Hajiya Dr. Asmau Adam Lema, da lauyar kungiyar Barrister Saadatu da kuma sakatariyar kungiyar fauziyya sai daya daga cikin ma'aikatansu (consultant) mai suna Mr. Danladi. Sun kawo ziyarar ne saboda an samu matsala daga wasu mazaje na matan da a ka yi rajistarsu.

A ganin wadannan mazajen, matan zasu zo nan gaba su fi karfinsu ne, Abu direba shine jagoran wannan farfaganda ta hana mata su amfana da wannan tallafi. Akan haka ne kungiyar suka zo da shugabannin su don a hadu da masu fada aji a kauyen a tattauna.

Ranar da 'yan kungiyar WH suka zo ayi wannan meeting, yayi daidai da washe garin ranar da Abu direba yayi ma amina dukan kawo wuka. Bayan sun gaisa da hakimi da fadawansa, sai aka jagorancesu zuwa cikin gida wajen iya, su ka zauna kafin sauran mazan da aka gayyata su zo.

A cikin gidan suka taradda iya tana fama da amina a kan ta karya kumallo, ga dumamen tuwo da kunu mai zafi, ita kuma sai sharer kwalla ta keyi, zazzabi ya rufe ta, haka ma bakinta ya kumbura, ga kwancin duka a jikinta ko ina abin ka da farar fata. A nan iya ke fada musu abinda ya faru jiya tsakanin amina da mijinta. Ta basu labarin zaman aure irin na amina da Abu a takaice da dukan da yayi ma ta jiya.

Bayan da ta kubuta daga hannun Abu, sai ta gudu zuwa gidan liman da taimakon Jamila, liman bai yi kasa a gwiwa ba tun da sassafe yasa aka kawo ta gidan hakimi, don shi kansa lamarin Abu direba ya ishe shi. Daga baya ya samu hakimi yayi mai bayani akan abinda ya ji kuma ya gani daga amina.

A cikin gidan hakimi, sai ga 'yan WH sun mayar da hankalinsu kacokam akan amina, (abin nema ya samu) suka roki iya akan ta basu dama su tattauna da amina, bayan fitar iya su ka dinga tambayarta cikin hikima da kwarewa tana yi musu bayanin halin da take ciki. A nan suka lallaba ta taci abinci kadan. Duk da basu dauki izni daga kowa akan zasu shiga matsalar amina ba, fauziya tayi recording duka abinda suka ji daga amina. Sun tashi daga taron da ya kawo su kusan lokacin azahar, ya rage daga hakimi sai liman, sauran mazajen da aka gayyata zaman duka sun watse bayan an wayar musu da kai, da taimakon liman da hakimi. To a nan ne WH suka roki alfarma akan zasu shiga matsalar amina da maigidanta.

Daga farko hakimi yaso ya ki yarda, yace "naji maganarku, amma ai mune wakilan wannan al'umma, amina kuma iyayenta suna nan da rayuwarsu" hajiya asmau ta gyara zama tace "hakane yallabai, tabbas kune iyayen al'umma, kuma a duk inda aka samu irin wannan matsala da ake take hakkin mace ko maras karfi, to ku ya kamata ku tsawata, ku zamo karfi da muryoyinsu a inda basu da iko ko dama. Mun samu labari ne daga bakin ita amina cewa kunyi iya kokarinku akan maganar, kuma ga shaida nan tunda gidanka da na baba liman nan ne mafakarta. Har da irin wadannan matsalolin duka kungiyarmu ta na taimakawa in dai ya shafi mace. Sannan kungiyarmu tana da hadaka da kungiyar da take kare hakkin dan-adam, wato Human Right Commision. Yallabai kayi hakuri, ko da baku yarda ba, zasu zo ne su shiga maganar kai tsaye idan har aka basu bayani.

Shiru ya ratsa a zauren na hakimi, yana tunani lalle ya san cewa human right zasu iya shiga kai tsaye don aikinsu ne. ko banza yana cike da jin haushin Abu direba saboda munanan halayensa akan iyalai, ga kuma abinda yayi na hure kunnuwan mazaje alhali ci gaba ake son za a kawo garinsu na rariya. Daga karshe, da liman yasa baki aka tabbatar babu wani abu na batanci da zaya shafi fadar, sai suka amince.

Liman da hakimi suka basu goyon baya, daga nan aka aika kiran Abu direba amma sai aka samu ya wuce garin Sokoto ina zai yi lodin gusau, sai jibi zaya dawo.

A motar da suke ciki doguwar wagon Toyota su na kan hanya zasu koma sokoto. Hajiya asmau tayi zurfi akan tunani, sai barr. Saadatu dake ta faman fada tace "hajiya kinga wani rainin wayo ko? ka daki matarka kamar ka samu dabba, safiya tayi kuma ka kama hanya zuwa wasu garuruwan saboda rashin imani." fauziya dake zaune kusa da ita ta amsa da cewa "ai wasu mazan are very wicked and irresponsible" mr. danladi dake zaune a gaba tare da direba duk sun fahimci yadda maganar take tun a can fada, suka dinga jajantawa.

Daga can bayan mota, hajiya asmau wadda tun dazu tunanin halin da suka baro amina ta keyi tace, "ina ga na fasa zuwa Abuja wajen conference da za'ayi jibi, mr.danladi you should pls go and represent us there, ni zan tsaya tare da barrister mu hadu da wannan monster din da yake neman kashe 'yar mutane." bayanin yayi musu dadi sosai, saboda sun kara tabbatawa hajiya bata dauki wannan case da sauki ba tunda har zata iya fasa zuwa wannan taron na NGOs mai muhimmanci, wanda dama halinta kenan bata da wasa da aikinta, kuma tana da kafewa idan akan kwato hakkin mace ne.

Kwana biyu tsakani, Abu direba ya dawo rariya, ga mamakinsa bai ga amina ta dawo ba, kuma babu wanda ya sanad dashi ko a waya cewa har yau tana can gidan liman ko hakimi, don ya sani ba zata wuce can din ba. Nan yayi ta fada yana sauke haushi akan iliya da jamila, yara su kayi shiru suna sauraren tijarar babansu.

Ya kare da cewa "to zan je gidan hakimi in dawo da matata, sai naga munafikin da zai kara hure mata kunne ta guje ni." Daga jamila har iliya babu wanda ya tanka shi, saboda sanin halinshi na fada ba tare da hujja, da kuma kin amsa laifukanshi.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now