*NADAMAR DA NAYI*
WRITTEN BY
*MRS OMAR*
DEDICATED TO
*BEEBAH LUV*_PAGE *1*_
_Da sunan Allah mai Rahama mai jink'ai ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala Allah ka sa yanda na fara rubuta littafin nan lafiya, na gama shi lafiya amin._
*GARGAD'I*
_Wannan littafin nawa k'irk'irarre ne banyi shi dan cikin fuska wani ko wata ba na yishine dan ilimantarwa haɗi da nishadantarwa, ban yarda wani ko wata su ɗauki koda kalma ɗaya daga cikinshi da niyyar su juya min littafi, in ba tare da izinina ba, duk wanda yayi haka to ban yafe ba._*GODIYA*
_Godiya ta musamman ga k'ungiya mai albarka na gaishe ku *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION* Allah ya k'ara basira da haɗin kanmu amin ya Allah._*JINJINA*
_Jinjina. dole nayi maki jinjina masoyiya ta gaskiya, hak'ika kin wuce k'awa aminiya sai dai na k'iraki 'yar uwa domin kin taka rawar gani sosai a zamana dake, ke 'yar uwa ce ta gaskiya ina alfahari dake *HAUWA SHEHU ALIYU* ( JIDDAH ALIYU) idan nace ina da kamarki a duniyar nan nayi k'arya saboda irin so da kauna da kika nuna min hak'ika *BANDA KAMARKI*_*********
Parlour ne na gani na faɗa wanda ya ke ɗauke da lausa_lausan kujeru, k'ayatuwar parlourn kawai zai tabbatar maka da gidan wani attajirin mai kuɗi ne. Parlourn tsit yake baka jin motsin komi sai sautin kuka k'asa_k'asa. Zaune yake akan kujera ya ɗaura k'afa ɗaya kan ɗaya, yayinda fuskarsa na kan wadda taketa faman kuka kanta a k'asa yake sai dai hawaye kawai dake sauka akan hannayen ta. Ƙafarshi ya sauke ƙasa ya gƴara zamanshi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Fatima kada kiga ina maki faɗa kiyi tunanin kamar bana sonki ne a'a ina maki faɗa ne kawai dan irin son da nake maki, nasan bazaki gane hakan ba sai bayan ba raina, ni ina son na gina maki rayuwa mai inganci, kada ki manta ke ɗaya mahaifiyarki ta haifa, shiyasa na zaɓa maki miji da kaina, saboda na tabbata Faruq yaron kirki ne. Fatima a matsayina na mahaifinki ki ɗaure ki amshi Faruq a matsayin mijin auranki, idan kika yi min haka kin gama min komi a rayuwa please."
A hankali ta ɗago jajayin idannunta ta dubi mahaifn nata da duk hankalinshi na kanta cikin muryar kuka ta ce.
"Dad I know kana sona fiye da tunanina but Dad bani da burin da nakeso irin na k'yautata maka...Amma sai dai hakan ba mai yuwa ba ne, bazan iya hana abinda zuciyata ke so ba rabani da Musaddik tamkar rabani da rayuwata ne Allah na gani bazan iya auran Yaya Far....."
Marin da ya wanka matane ya sa ta haɗe sauran maganar da ke bakin ta. Tashi tsaye tayi cikin zabura, da tsoron ganin fuskar mahaifin nata ta sauya lokaci ɗaya.
"Thanks Fatima da irin sakayar da kika nuna min a matsayina na mahaifinki wanda nasha wahalar tarbiyarta dake tun bakisan abinda duniya ke ciki ba, na gina maki rayuwa da har ta kaiki ga ganin wadda kike so har kike masayar yawu dani yau Fatima. To bari kiji dak'yau no one can stop this marriage and it’s my final answer, zaki iya fitar min daga ɗaki."
Hannu yasa ya nuna mata hanyar fita da gudu tabar parlour ta nufi ɗakinta tana kuka, kan gado ta faɗa ta saki wani kuka mai sauti. Wayarta ta jawo da sauri jikinta na rawa ta danna wata number mai ɗauke da sunan *NOOR HAYYAT* ringing ɗaya aka daga, tamkar dama jiran k'iran nata ake. Daga b'angaran da ta k'ira naji ya wani sauke ajiyar zuciya mai sauti.
"Amincin Allah ya tabbata agareki yake sarauniyar matan duk duniya, haba tawa ina kika shige ne? ko kinsan zuciyata zata iya tarwatsewa a duk lokacin da na rasa wannan muryar taki mai daɗi kamar sarewa, banida wani buri da ya wuce injini kusa dake, a kullum ina rukon Allah ya nuna min lokakacin da zamu zama miji da mata, Sahiba lafiya naji kinyi shiru?"
Tunda ya fara magana Fatima ta lumshe idonta bata buɗe ba sai yanzu da ta saki sabon kuka.
"Ya salam haba *SANYIN IDANIYATA* wa ya taɓa minke? wallahi ko waye sai yaga b'acin raina dan ban haɗaki da kowa ba!"
Kuka ta k'ara fashewa dashi muryarta na rawa ta fara magana.
"Musaddik na shiga uku! Dad naso ya tarwatsa min zuciyata, ba susan cewa rabani da kai tamkar rasa rayuta...."
"Dakata Teema! ban gane abinda kike faɗi ba."
"Musaddik Dad yace zai aurar dani ga ɗan d'an uwansa Yaya Faruq..."
Wata irin tsawa yayi tamkar tana kusa dashi"What Faruq? No!!! dear impossible taya Dad zai raba anta da jini!? ko yasan rabamu babban kuskure ne. Ba komi Sahiba nasan ba komi yasa Dad yatsaneni ba dan kawai ya ga ni makaho ne ba ido shiyasa yake son rabamu, amma ki sani duk ranar da aka rabamu to daga ranar zan sha guba na mutu kowa ya hut..."
Da sauri ta daga murya cikin sautin kuka
"Na shiga uku haba Musaddik me yasa zaka faɗi haka ko ka manta zuciyata tamkar kitse ce Idan tanajin wannan kalaman naka zata iya narkewa, duk duniya bani da wani farin ciki da ya wuce na ganni a ɗakinka mun zama miji da mata a kullum mafarkina shine mukasance tare har abad, bani da wani buri daya wuce ka zama uban ya'yana ko bayan babu raina zanyi alfahari da haka"
Murmushi ya yi tare da gyara wayar a kunansa ya ce
Na sani rabin raina keke faɗa ana ji ai ni bakina bazai iya faɗin komi ba domin kuwa, zuciyata cike take da sonki babu macen da nake buri aura irin ki duk da na kasan ce ni ba kowa bane amma kika sadaukar min da rayuwarki"
"Dan Allah ka daina faɗin haka Noor hayat kai fa na daban ne buri na kawai muyi aure..""Ai kam babu rana babu kuma lokaci indai akan wannan dan iskan yaron ne dan haka idanma mafarki kike to ki farka dan gari ya waye."
Da sauri ta ɗago kai tana kallon mai magana
YOU ARE READING
NADAMAR DA NAYI
ActionNADAMAR DA NAYI labari ne da yake d'auke da NADAMAR yaudara ,cin amana da dai sauransu. Labari ne a kan wata yarinya da ta fada soyayyar wani makaho iyayenta sukaki amincewa, suka aurar da ita ga dan uwanta amma daga karshe....