NADAMAR DA NAYI page 3

274 28 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

        
             WRITTEN BY
           *MRS OMAR*

              STORY BY
        *HAUWA M. JABO*

           DEDICATED TO
             *BEEBAH LUV*


                   _PAGE 3_

Kai ta ɗago itama ta kura mashi manyan idanta, fuska ta yatsina kafin ta ce.

"Ina kwana?"
Murmushi ya yi kafin ya girgiza kai ya cije le'bensa ya aje phone nashi a gefan kujera had'i da lumshe ido, a hankali ya wani juya k'wayar idonshi ya ce.

"Humm ashe kina magana? ai ji nake ke kurma ce." Ya fad'a yana kallon 'kwayar idonta.
Fuska ta yatsina ta turo baki.

"Fatima kenan wai sai yaushe za ki gane Allah ɗaya ne? ki amince dani nazama uban yayanki."

"Humm ai kam babu rana ba lokaci, dan zuciyata mutum ɗaya na mallakawa ita,  Yaya Faruok kasani bazan ta6a amincewa da kai a matsayin mijina ba."

Sake girgiza kai ya yi dan jin kallamanta masu zafi, ya murmusa sannan ya fara magana cikin rarrashi.
"Please Fatima ki tausayawa zuciyata wallahi duk duniya babu macen dana ta6a so sama dake, idan na rasaki zan shiga babban hadari please ki faimce ni Fatima. Kinji?"

Baki ta ta6e ta ce

"Ji yazama dole amma yarda bata zama dole ba."
Murmushin takaici ya yi wanda daka kalli fuskarshi kasan baikai zuci ba.

"Fatima yanzu abinda zaki ce kenan? zamana dake baki tab'a faɗa min magana ba, haka yasa nayiwa Dad tayin auranki dan irin tarbiyar da ki ka samu."

Tsoki tayi, ta saki murmushin takaici wanda baikai zuci ba ta ce.

"Yaya Faruq kenan u will never understand me. Ta yaya bazaka fahimci abinda nake ji a zuciya ta ba, wallahi duk lokacin da kayi kuskuran aure na to wallahi zaka tafka babban kuskuren da baka tabayi a rayuwarka ba.."
Mai aikinsu ce ta shigo ɗauke da tire a hannunta, lemun kwaline da cup a kai, saman table  ɗin gabansa ta aje har ta ɗaga kai zata juya Faruq yayi mata alama da ta zuba mashi, bayan ta juya ta fita ne ya ɗauka ya kafa a bakinshi bai wani sha da yawa ba ya aje cup ɗin, sai da ya aje kafin ya ce.

"Nasani Fatima zuciyarki babu So na a ciki, amma na tabbata idan kika aure ni zaki So n.."

"Never!!! idan ko haka ta faru to na tabbata ranar zakayi NADAMAR aure na, kuma daga ranar zaka tsani duk wata mace dake duniya dan sai n.."

"Dakata ba sai kin ida faɗin abinda zaki faɗa ba, Fatima har kina tunanin zan iya hakuri da auranki dan kawai ki auri wannan makahon yaron? kin manta tarin alkairin da mahaifinki yayi min? To wallahi Fatima yanzu ne ya kamata na nuna masu abinda sukayi min dan su tabbatar da ni ɗane ba butulu ba"

"Aikin banza kai ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya mtss fool." Ta 'karasa tana murguda baki.

"What? Fatima ni ki ke faɗawa wannan maganar har kina da bakin zagina? To bari ki ji yanzu na fara sonki ki yi duk yanda zakiyi, but don't call me that again because if u...... humm Fatima kinci sa'a wallahi ina sonki wallahi da yau kin gane shayi ruwa ne, haba Fatima bazaki tausayawa mahaifiyarki ba ko bak'ya tunanin halin da zata saka kanta ne? Idan har kikaki aurena.."

"Aikin banza ba'a son mutum amma bazai fahimta ba sai inda ba'a sonshi yake zuwa,."

Gaba ɗayansu suka juya suna kallon k'ofar dan ganin mai magana. Cikin isa ta iso gabansu tana wani karairaya kamar zata karye, ga wani uban make-up da tasha an kawo ɗaurin ɗan kwali gaban goshi, ta na wani yatsina sai kace itace sarkin kyawawan duk duniya. Baki Faruok ya saki yana kallon irin abinda take dai_dai inda yake zaune ta zauna saman hannun kujera ta wani murmusa kafin ta ce.

"Haba Yaya look at me and look at her dame tafi ni? Nafita sanin kanka ne Yaya inada duk wani abu da mace take bukata, ya kamata ka fahimci haka."
Sai da Faruok ya kalli Fatima yaga murmushi kwance a fuskarta kuma ya tabbatar ba murmushi wani abu bane illa na mugunta yasa ya tashi cikin isa da tak'ama yana taku har ya iso dai_dai inda take ya zauna har suna gugur juna ya ce.

"Sahiba wai da gaske bamu dace da juna ba?"
Cikin rawar muryarta Fatima za tayi magana ya yi saurin ɗaura ɗan yatsansa a kan le6enta ya ce.

"Sheeeeee.... Ba sai kin  wahalar da bakinki ba."
Ido ɗaya ya kashe mata kafin ya ce.

"Humm Hafsat kinyi kuskure babba da zuciyarki ta zab'ar maki kiyi soyayya dani, har take sak'a maki zan iya auranki, wallahi Hafsat tunda nake ban tab'a jin sonki koda na sakan ɗaya a zuciyata ba, a kullum mafarkina shine naga na auri Fatima  mace tamkar da dubu. Tun ranar da na fara gane kina shige min na san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Hafsat ki sani shi so ɗaya ne ba'a sake masa suna.."

"Amma yaya Faruok ya kamata ka fahimce ni sannan ka gane Fatima babu sonka ko kaɗan a cikin zuciyarta"
"Hafsat na tabbata idan Fatima ta aure ni wata rana zata so ni.."

Cikin sauri fatima ta mike tsaye ta ce.

"Kaga Yaya Faruok gaskiya Hafsat ta faɗa ya kamata ka fahimce ta ita ce dai_dai da kai nima ka barni na auri dai_dai dani."
Cikin fushi Faruok shima ya mi'ke kamar zai daketa ya ce.
"Idan naki fa?"
"Humm zaka mutu kuwa bakayi aure ba indai ka ce Fatima zaka aura."
"Hafsat ki fita daga idona kafin na k'aryaki yanzu"

Tsoki Fatima tayi ta buga k'afa kafin ta nufi hanyar ɗakinta ita ko Hafsat cikin kissa ta k'ara nufar shi...

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now