NADAMAR DA NAYI 29

191 9 0
                                    

*NADAMAR DA NAYI*

_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
(Mrs Omar)
_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*

_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*


Page 29
*********


*BAYAN WATA HUDU*

Yau Fatima ta cika wata hudu dai_dai da rabuwarsu da Faruok ta gama iddarta harda wasu kwanaki akai, Dad yasa aka kirata shiyasa take zaune a gabansa ta sadda kanta ƙasa, a hankali ya kira sunanta.

"Fatima!"
"Na'am Dad"
"Dago kanki ki kalle ni dan wannan maganar bata wasa bace"

Kai Fatima ta ɗaga ta kalle shi amma duk da haka basu haɗa ido ba.

"Fatima kinsan dalilin dayasa na kiraki"
"A'a Dad"

Ta fada

"To shi kenan dama nasan baki san dalilin kiran ba, amma yanzu zan faɗa maki"

Tsayawa yayi ya dan numfasa kafin yace

"To Fatima yau ma gani zaune dake a karo na biyu kamar yanda na zauna dake a farkon maganan aurenki da Faruok yau ma haka gani dake, shin kina da wani wanda kike so?"

Jikin Fatima ne yayi sanyi da sauri ta runtse idanunta kirjinta ne ya fara dukan uku_uku.

"Dake nake Fatima kinyi shiru.
"Akwai Dad"

Ta fada da sauri.

"To waye shi?"
"Dad wancan ne dai na farko Musaddik d.."
"Dakata basai kin ida ba"

Dad ya katseta da sauri.

"Fatima kenan har yanzu dai baki da takamaiman mai sonki dan haka a karo na biyu zan ƙara zaɓa maki miji ko kina da magana ne?"

Kai Fatima ta girgiza dan hawayen da keson su sauko a fuskarta daurewa take dan ta samu ta danne zuciyarta.

"Fatima da farko na zaɓa maki miji mai nagarta amma kikaqi zama dashi dalilin haka yasa nayi fushi dake amma sai daga baya na yafe maki, Fatima wannan auran da zakiyi inaso ya zama shine na karshe a rayuwarki indai har nine na haifeki, dan haka har yanzu kina nan akan bakanki na bijirewa maganata?"

Kai ta girgiza cikin sanyin murya tace.

"A'a Dad na amince Allah yasa haka shine mafi alkhairi"
"Anya Fatima maganar nan har cikin zuciyarki take"
"Dad har a zuci nayita"

Murmushi Dad yayi yace

"Allah nagode maka Fatima Allah yayi maki albarka, dan haka wannan lokacin bana son ko kwana uku a kara dan haka gobe idan Allah ya kaimu za'a ɗaura maki aure ga wanda na zaɓa maki"
"To amma Dad waye shi?"
"Kada ki damu gobe zaki sanshi, kiyi hakuri kinji ko Fatima wallahi bawai banson ki auri wanda kike so bane, nafi kowa son ki kasan ce cikin farin ciki na har abada Fatima zaɓinki ne kawai baiyi min ba dan ban amince da NAGARTAR shi ba, ina so 'yata ta auri mutum mai NAGARTA, wallahi Fatima ko yanzu kika kawo min wani ba wannan yaron ba indai har na amince da NAGARTAR shi zan baki shi ki aura Fatima dan Allah kiyi hakuri ki zauna da wannan zabin nawa"
"Naji Dad insha Allahu baza'a samu matsala ta wajena ba"
"To shikenan kina da bukatar wani abu kafin goben dan bana son taron matan nan shiyasa ko mahaifiyarki ban faɗa mata gobe za'a ɗaura auran ba dan haka idan kina da bukatar wani abu just tell me i will do anything for you"

Kai ta girgiza alamar babu"

"To shikenan Allah yayi maki albarka tashi ki koma ɗakinki"

A hankali Fatima ta tashi jiki a sanyaye ido Dad ya bita dashi cike da jin son ƴar tashi na ƙara shiga zuciyarshi.
Wayarshi ya duba ya ɗauko number Faruok yayi dialing ba wani ɓata lokaci Faruok yayi picking, domin kuwa indai kiran Dad ne to Faruok baya jinkirin ɗauka, saida suka gaisa Dad yace

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now