NADAMAR...19

188 13 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*NADAMAR DA NAYI*

_WRITTEN BY_
*MRS OMAR*

_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*

_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*

_This page is for you Aunty maiJidda Musa nagode quarai da comment d'inki Allah yabar kauna_

_PAGE 19_
*******

Wayar ya ƙurawa ido yana kallon sunan data rubuta mashi, shiru yayi na wani lokaci yana tunanin sunan a hankali ya lumshe idonsa ya ɗan ƙwantar da kansa saman kujera yana nazarin sunan.
Ita dai Habiba tana zaune tana kallonshi, kamar an tsikareshi ya ɗago da kanshi ya kuma danna wayar sunan ya nuna mashi baki ya cije ya girza kai ya ce.

"BZ.. Why? Fatima ki rasa sunan da zaki zaɓa ki saka min a wayarki sai banza.. Fatima ban taɓa tunanin kiyayyar da kike min takai haka ba sai yau na yarda bakya sona amma ban taɓa tunanin har zaki iya ƙirana da banza ba."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi kafin ace me launin idanuwansa har sun chanza colour.
Hannu ya ɗaga ya buga kan kujera ya ce.

"No!! Fatima a ko wani lokaci ina hakuri da abubuwan da kike mani but dis time i will not forgive ur mistake Fatima! yau sai na nuna maki ni ba banza bane saina dasa maki abinda bazaki taɓa mantani ba a rayuwarki."

Kai ya ɗago ya sauke idonsa kan Habiba dake zaune tana sauraron abinda yake faɗi, fuska babu annuri ya ciro kuɗi ya mika mata.

"Kije gida sai gobe ki dawo."

Yana rufe baki ya ɗauki wayoyinshi data Fatima ya haura sama abinshi yana shiga ɗaki kasa komi yayi sai kawai ya faɗa gado ko takalmin ƙafarsa bai cire ba.

Fatima tunda ta shiga ɗaki take faman sauke lumfashi kamar irin tasha gudun nan, saida ta daɗe tana lumfasawa kafin ta tuna data bar wayarta a parlour gashi ta cireta a security bata san yaya zatayi ba.
Tsohuwar wayarta dake kan mirror ta ɗauko ta kunna, kokarin naiman number Musaddik tacigaba dayi ta ƙira yafi a kirga bai ɗaga ba sai ƙiran ƙarshe dan har tana shirin hakura ya ɗaga take ta wani saki ajiyar zuciya mai ƙarfi, hawaye ya fara sauka a fuskarta cikin sanyin murya ta fara magana.

"Haba Hubby me yasa zaka dinga azabtar da zuciyar da ta mallaka maka ruhinta gabaki ɗaya, meyasa zaka haddasa mata ciwon da babu mai maganinshi sai kai ko kasan rashin ka babbar matsala ce a rayuwar Fatima rashin jin muryarka na kwana ɗaya tamkar shekara dari ne rashin ganin wannan ƙyakkyawar fuskar taka tamkar bana gani ne idan har banji motsinka ba bazan taɓa samun sukuni ba, please Musaddik kada ka ida sa zuciyata ta buga mana"
"Fatima kenan yanzu har kina da bakin magana bayan duk wani so da ya kamata na nuna maki na gwada maki amma baki san da haka ba kinga yanzu ke matar wani ce kin riga da kin mallaka mashi duk wani abu naki dan haka Fatima na hakura da sonki na yarda sonki shine zai rabani da rayuwata.

Cikin tsawa Fatima ta ce.

"No Musaddik kada ka kashen waya Wallahi babu abinda ya taɓa haɗani da ya Faruok har yanzu alkawarin da na ɗaukar maka yana nan."
"Are u sure?
"Yes am sure."

Ajiyar zuciya Musaddik ya sauke mai ƙarfi tamkar tana kusa dashi ya ce.

"Wow sweetheart am proud of u i will never forget u in my life, Sweetheart ina so ki ƙara ɗaukan min alkawari cewa bazaki daɗe ba zaki fito kuma kada ki yarda wani abu ya shiga tskaninku."
"Kada ka damu Noorul Hayat ai ni taka ce ni ɗaya babu wanda zai iya rabamu in ba Allah ba, dan haka nayi maka alkawari mutuwa ce kawai zata hana ni zama mallakinka, a kullum ina maka kallon mijina na har abada.
Anyways mubar wannan maganar nasan yanzu account ɗinka babu kuɗi so nayi maka transfer kafin mu haɗu."
"Why? Sweetheart na faɗa maki bana son kina ban kuɗi dan soyayya ta dake bata kuɗi bace."
"Kada ka damu wallahi na sani shiyasa nake ƙara sonka Hubby na."

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now