NADAMAR.. 20

176 17 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

    *NADAMAR DA NA YI*

             _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

            _STORY BY_
     *HAUWA M. JABO*

 
         _DEDICATED TO_
          *BEEBAH LUV*

             _PAGE 20_
                ******

Hawaye na bin fuskarshi kamar panpo ya furta.

" _Ni Faruok Muhammad Jabir Lamido na yanke igiyoyin aure na dake guda uku idan kin samu miji kiyi aure_.."

Yana gama faɗin haka ya sulale ƙasa ya dafe kansa domin ya rasa duniyar da yake.
Yana furta kalmar sakin Fatima ta fashe da kuka ita kanta bata san kukan me take ba na murna ne kona me?  juyawa tayi da sauri tabar ɗakin tana zuwa tashiga haɗa kayanta tana murna.
Cak ta tsaya da haɗa kayan dan tunawa da su waye iyayenta kuma me zataje ta faɗa masu.

"Nashiga uku to yanzu idan naje gida me zance in na ce ya Faruok ya sake ni to meya haɗa mu?."

'No Fatima kada ki damu da duk abinda za'ayi maki wannan ce kawai damarki ta samun cikar burin ranki.'zuciyarta ke raya mata haka!

"Gaskiya ne zan iya shanye komi saboda Musaddik, am sorry Mom and Daddy nayi iya bakin ƙokarina dan ganin na zauna da Faruok amma zuciyata taki amincewa dashi."

Kuka ta fasa ta faɗa kan gado tana juyi.

Tunda Fatima ta fita daga ɗakin Faruok hawaye ke bin fuskarshi faɗi yake.

"Haba Fatima meyasa zuciyarki taki amincewa dani tazaɓa maki ni a matsayin enemy ɗin ki, Fatima ina sonki son da ban taɓa yiwa wata mace ba, Fatima kinja yau da bakina na furta maki kalmar saki sakin ma irin na jahilci saki uku, ko da yake haka shine kawai mafi alkhairi Fatima na barki ki auri wanda kike so dan ma kada na mai dake shiyasa nayi haka amma wallahi Fatima ki sani kece mace ta farko dana fara so kuma da sonki zan mutu."

Yana magana yana kuka kamar karamin yaro duk wanda ya kalli Faruok a wannan lokacin dole ya tausaya mashi dan Faruok mutum ne mai hakuri.
Daren ranar haka suka kwana babu wanda ya runtsa idonsa ita dai Fatima tunanin abinda zata faɗa idan taje take.

******

Around 7:30am

Faruok ya farka daga ɓarawon barcin da yayi awon gaba dashi da sauri ya tashi yana faɗin

"Allahumma ajirni fi masibati wa'akhlifni  khairan min haa, meyasa wannan lamarin bai zama mafarki ba? shikenan yanzu Fatima narabu dake meyasa ban daurewa zuciya ta ba da duk irin kalmar da zaki faɗa min? tabbas banyiwa su Abba adalci ba dana sakeki duk irin karamcin da suka nuna min irin sakayar da zan masu kenan wayyo Allah na."

Kai ya kuma dafewa, a hankali ya fara ƙokarin tashi ya nufi toilet ruwa ya watsa sannan ya dawo kan sallaya ya kabara sallah bayan ya gama nan fa ya zauna addu'a kamar yanda ya saba sai dai ta yau tafi ta kullum, yana gamawa ya dan zauna jim kaɗan ya tashi ya saka kakinsa bai wani tsaya shiri ba kamar yanda ya saba ya saka takalmi ya ɗauki key ɗin mota ya fita har ya kama hanya zai sauka ƙasa sai kuma ya ɗaga jajayen idanunsa da sukayi masa luhu_luhu ya kalli ƙofar ɗakin Fatima kai ya girgiza ya nufi ɗakin, a hankali kamar mai jin tsoro yasa hannu ya murɗa ƙofar abin mamaki yau ƙofar a buɗe take kai ya tura yana shiga suka haɗa ido suna kallon juna zaune take ta buga tagumi, da sauri ta kauda fuskarta gefe.
Dai_dai inda take ya ƙarasa ya qura mata ido take ya dinga tuna irin abubuwan da suka faru a daran jiya masu daɗi da marasa daɗi hawaye ne suka taho zasu sauka a fuskarshi da sauri yasa hannu ya gogesu ƙarfin hali yayi ya furta.

"Ki tashi ki haɗa kayanki idan kin gama ki saman a falo zan saukeki gida"
Da sauri ta ɗago kai ta kalli, idanunshi ya lumshe ya ce.

"Ina jiranki ki maida hankali dan zan wuce wajan aiki."

Shiru tayi tana kallonshi, dai_dai inda akwatan kayan ta suke ya nufa ya fara haɗa mata wa'anda ya gani a haka ya haɗa su, ya yaja akwati biyu ya ce.

"Ki tashi kisa mayafinki sauran kayan idan na dawo zan ba Habibu ya kawo maki."

Cikin sanyin jiki Fatima ta tashi ta saka hijabinta yana gaba tana binsa a haka kar suka isa mota.

Fatima hankalin ta bai sake tashi ba sai da taga motar Faruok ta doshi titin gidansu take hawaye ya fara sauka a kan fuskar ta, ɗaga kan da Faruok zayi ya hango hawayen da ke fita a fuskarta da sauri ya taka birkin motar yayi parking, idanunshi ya dan lumshe kafin ya sauke  ajiyar zuciya a hankali ya furta.

"Kukan me kike ko tun kafin ayi nisa kin fara NADAMAR abinda kika sa zuciyata ta aikata maki?"

Kai Fatima ta ɗago tana kallonshi tawani saki shu'umin murmushi ta ce.
"Hmm har akwai ranar da zanyi NADAMAR rabuwa dakai? yaya Faruok kenan to idan ma mafarki kake ka farka dan wallahi babu ranar da zanyi NADAMAR rabuwa dakai dan wadannan  idanuwan nawa sun riga sun kekashe basa kallon kowaa sai Musaddik, kukan da kaga inayi kuma kawai ina tunanin halin da iyayena zasu shiga ne idan suka ganni amma ba NADAMAR rabuwa da kai nake ba."

Tunda ta fara magana Faruok yayi shiru yana kallon ta dan ya tabbatar da Fatima bazata taɓa sonsa ba take hawaye suka zo zasu sauka a fuskarshi yayi saurin tararsu yana irin basarwa ɗin nan, mota ya tayar yacigaba da tafiya har ya isa get ɗin gidan mai gadi ya buɗe masu da sauri yana kai masu gaisuwa amma babu wanda ya amsashi, wajen parking suka nufa bayan yayi parking yayi zaune a mota ya kasa komi sai tunani a hankali ya juyo ya kalleta ya ce.

"Gamu munzo Fatima ga takardar sakinki nan sannan duk wani bayani na ciki basai kin masu bayani ba nagode Allah yasa haka shine mafi alkhairi ki shiga gida ni zan wuce wajan aiki."

Yana magana yana kauda fuskar shi dan kada ta gane halin da yake ciki.
Hannu tasa ta buɗe ƙofar motar ta fita da sauri bayan ta fita Faruok yasa aka ƙwashe mata kayan da sukazo dasu.

Zaune suke a kan dinning table suna breakfast kamar yanda suka saba gabaki ɗayansu, daga naisa Aunty Zee ce ta fara hangota tana bin bango, da kai aunty Zee ta nunawa Hafsat ita dan ko marar hankali yaga Fatima yasan ba lafiya bace ta fito da ita, murmushin mugunta aunty Zee tayi kafin ta ce.

"A'a oyoyo gafa amarya Fatima."

  Da sauri kowa ya maida hankalin sa ga inda Aunty Zee ta kalla tana magana babu kamar Daddy da Mom, ganin yanda Fatima keyi ne yasa Daddy da Mom saurin tashi a kan dinning ɗin, kafin ace me har sun isa gabanta Daddy ne ya haɗi fuska yana faɗin.

"Ke lafiya meya kawo ki da wannan safiyar haka?"
Shiru tayi ta kasa magana saida ya kuma daka mata tsawa.

"Fatima ba magana nake maki ba kikayi banza dane."

Jiki na rawa ta meka mashi takardar hannunta.

"Ba abinda na tambayi ki ba kenan Fatima ki faɗa min dalilinki na zuwa gida yanzu."

Murya na rawa ta ce

  "Daddy duk amsar tambayar ka tana cikin Wannan takardar."
 
Ya buɗa baki zayi magana Mom ta dakatar dashi, a hankali yasa hannu ya amsa, hannunshi na rawa dan baisan abinda takardar take ɗauke dashi ba, a hankali ya buɗe ya fara karantawa a fili kamar haka.

_"Assalamu alaikum ya ku iyayena idan nace ina da kamar ku a yanzu nayi karya kunyi min komi a rayuwata kun zama gatana, zama daku yasa har na manta raɗaɗin zafin mutuwar iyaye hakika kunyi min komi a duniya sai dai kash naso na zama mutum mai maida alkhairi ba batulu ba amma zuciyata ta hana ni aikata haka, a gaskiya a da naso Fatima sai da na aureta saina gane ashe ba irin matar da tadace na aura bace gaskiya Fatima bata cikin irin tsarin macen da nake so dan haka na yanki shawarar kawai rabuwa da ita dan haka ni Faruok Muhammad Jabir Lamido na saki matata Fatima saki uku idan ta samu miji tayi aure."_

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun."

Suka ɗauka shida Mom.
Suko su Anty zee kamar su zuba ruwa ƙasa susha.

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now