*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*NADAMAR DA NAYI*
_WRITTEN BY_
*MRS OMAR*_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*
_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*_PAGE 7_
*ASALINSU*
Asalinsu haifaffun garin yola ne ta jahar Adamawa,
kakansu mai suna *ALJAHI MUHAMMAD HABIBU LAMIDO* babban mai kuɗi ne a cikin gari, babu wanda baisan da zamanshi a cikin garin Yola ba.
Kakansu Alhaji Muhammad Habibu cikakken bafulatani ne na usuli sune fulanin da ake ƙira funnange sune fulanin asali wajan ƙyau da komi sune.
Alhaji Muhammad Habibu yana zaune ne a wata unguwa mai suna mafias quarters yana zaune da matarsa ɗaya mai suna Hajiya Hadiza. Yara biyu kaɗai Allah ya azurtasu dasu duk maza *BASHIR MUHAMMAD LAMIDI* sai *JABIR MUHAMMAD LAMIDO*.
bayan sun girma ne sun mallaki hankalinsu duk suka fara naiman na kansu. Inda mahaifinsu ya ɗaurasu a kan dukiyarshi.
ba jimawa Alhaji Muhammad Habibu ya naimawa BASHIR auran Hajara,Bashir baiso haɗin ba.
Saboda yasan ko wacece Hajara.
Amma babu yanda zaiyi haka ya amince da umarnin maifinshi dan irin kunya tasu ta fulani.
Babu laifi bashir yayi mata duk wani abu da akeyiwa mace idan zaka aureta.
Bayan aure basu wani daɗe ba Allah ya bata ciki bayan wata tara ta haifi ƴarta mai suna Aisha.
Sai da ta haihu uku kafin jabir yasamu Matar aure saboda akai_akai take haihuwa yanzu haka bayan Aisha tana da yara biyu Jamila da Saratu suka zama uku kenan.
Mahaifinsu yayi murna sosai da zaɓinshi domin itama cikin family ɗinsu take.
Itama cikin hukuncin ubangiji ta samu ciki bayan wani lokaci ta Haifi ɗanta namiji ranar suna aka saka mashi *FARUOK* dukda ita kuma Hajara tana goyan Zainab Aisha ita ce babba sai Jamila sannan Saratu sai Zainab ta goye duk kusan tare akayi goyan Zainab da Faruok. Bayan an yaye Faruok ne kakansu Alhaji Muhammad Habibu Allah yayi mashi rasuwa mutuwarshi ta girgiza jama'a sosai dan ya kasance mutuman kirki. Bayan mutuwar Alhaji Muhammad Habibu Bashir ya samu mata dazai ƙara aure, mai suna Shamsiya Hajara tayi hauka sosai dan ganin ya fasa auran amma ya ce ina.
ɗan uwansa ma ya goya mashi baya dama ita mahaifiyarsu babu ruwanta duk abinda ya'yanta keso to itama tanaso Bashir yayi murna sosai da samun mata kamar Shamsiya dan mace ce mai hakuri da juriya uwa uba tarbiya data samu daga gidansu.
Haka ya auri Shamsiya babu wani zaman lafiya daga wajan Hajara ita dai Amarya ko a jikinta. Saida tayi shekara biyar bata samu ciki ba sai daga baya ta samu ciki tunda ta samu ciki Hajara hankalinta yaki ƙwanciya duk a tunaninta Shamsiya namiji zata haifa, tasha wahala sosai itama Hajarar na ɗauke da ciki amma bata ta kanta kawai ta Shamsiya take bayan wani lokaci Hajara ta qara haihuwa yarinya taci sunan Hafsat.
Amma tayi bakin ciki sosai data sake samun ƴa mace itama Shamsiya mace ta haifa ganin Shamsiya ta haifi mace yasa ta ɗan saki fuska itama ranar suna ya saka mata Fatimatu.
Bayan sun haihu babu daɗewa Jabir da matarshi sukayi haɗarin mota baki ɗayansu suka mutu dama shi Faruok sun barshi a gida mutuwar Jabir ta girgiza ɗan uwanshi.
Bayan anyi sadakar uku ne Bashir ya maido Faruok gidanshi Hajara tace babu ɗan da zata rika haka Shamsiya tasa hannu biyu ta amshi Faruok ta rikeshi tamkar ɗan data haifa duk wata kulawa Faruok yasamu daga wajan Alhaji Bashir da matarsa Shamsiya watau maman Fatima.
Shima kansa Faruok ɗin ya nuna masu shi ɗane ba shege ba dan duk wata biyayya Faruok nayi masu.
inda ya ɗauki son duniya ya daurawa Fatima bayan Faruok ya girma ne ya zama cikakken namiji.
Alhaji Bashir yasamar mashi makarantar aikin soja dake N.D.A kaduna Faruok baiso aikin soja ba.
Amma ganin iyayenshi naso yasa ya amince bayan ya zama cikakken soja ne aka fara kaishi Abuja amma Dady yace ina dole a maidoshi kusa dashi a haka aka maido Faruok Adamawa da aiki bayan ya dawo ne fa.
Ya faɗawa mahaifin nashi abinda ke zuciyarshi daga shi har Mom sunyi murna sosai da zaɓinsa dan suma suna da wannan burin na haɗasu aure.
Amma abin haushi tunda Fatima ta samu labari bata kara ganin Faruok da mutunci ba.
Dan soyayyar makahonta ta rufe mata ido.
Shine fa har zuwa yanzu ake abu ɗaya.*DAWOWA LABARI*
Lum Fatima tayi zata faɗi ƙasa Faruok yayi saurin tararta ta faɗa jikinshi take lumfashinta yayi sama.
Hannu yasa yana dan buga fuskarta ko zata farka amma ina tayi nisa take ya ɗauketa cak sai ɗakinta duk da Dad ya nuna bai damu ba amma dashi aka nufi ɗakin nata harda aunty Zee ,Hafsat ko kamar zata kashe kanta.
Bayan ya shinfiɗar da ita ne ya kama hannunta yana murza tafin hannunta da sauri da sauri yana faɗin."Please my sis am ummu ta mayu please miwadin ma alkawar to nini gam mbangu go am ayidi a fadda horemada,mi daccima har duniyaru tagga.
insha Allah i promise na hakura da sonki Fatima koda zan mutu ne banyi aure ba zan hakura ki auri wanda kike so dan samun farin cikin ki"Hawaye ke sauka a idonshi kamar ƙaramin yaro sai surutu yake har baisan abinda ke fita a bakinsa ba. Cikin ɓacin rai Dad ya ce.
"Faruk a ginnado na? Anfu a yidi mi semta a gite duniyaru,toh hami yeccuma dat's impossible. Kuji min fa yara naso su maidani karamin mutum
To wallahi baku isa ba"Yana maganar ne yana nuna Faruok da fatima da ɗan yatsanshi cikin ƙarfin hali Faruok ya ɗago kai yana faɗin.
" Amma dad min dacca mo tan o mbanga mo o yidi,mi andi a yidi am dad amma wala no en wawi.kar yazo ya zama sai anyi abu daga baya azo ana regretting.
Dad wallahi Allah naso Fatima fiye da tunaninku but dole zan hakura da ita dan samun farin cikin ruhinta.."Yanda yake magana ne duk jikin Dad yayi sanyi ya ce
"Mi nani Faruok,mi hefti ko a viyata,amma miyida mi volla de didi(2)mi arti mi yecci duniya irin alkawar mi wadi je hautugo Mon mbangal.."
Saida Dad ya ɗan lumfasa kafin yacigaba da magana.
"Faruok kana ganin zamu bar yarmu ta aure wanda bamu san ko waye shi ba? ɗan gid.."
"Please Alhaji basai ka faɗi ko waye shiba. Saboda haka min medata daccugo bingel amin mbanga mo Mara lenyol titidum. Dan munaso ƴarmu ta aure miji mai NAGARTA ba wanda baisan usilinsa ba.
Cikin jin daɗi magana Mom Fatima Dad ya danyi murmushi irin nasu na manya ya ce.
"Ina alfahari dake matata"
Wani irin bakin ciki ne ya ƙara shiga zuciyarsu Mom Hafsat ba kamar Aunty zee da takejin kamar ta kashe Faruok.
Cikin sauri Faruok ya mike yaje ya ɗauko robar ruwan faro masu sanyi ya buɗe a hankali ya fara zuba mata a fuska take ta fara faɗin."Please Dad help me wallahi Allah idan na auri Yaya Faruok mutuwa zanyi"
Abinda kawai take faɗi kenan kamar irin saban kamu nan.
Cikin sanyin murya Faruok ke faɗin."Please sis open ur eye's
A hankali ta fara buɗe idanunta take ta saukesu kan k'yakk'yawar fuskar Faruok.
Da sauri ta tashi zaune tanabin su ɗaya bayan ɗayansu da kallon.
Jiki babu ƙarfi ta fara ƙokarin tashi Faruok zai kamata ta ɗaga mashi hannu.
Cikin jarumta tamike tsaye take wajan mahaifinta ta nufa duk suna kallon ikon Allah.
Cikin sanyi murya hawaye na fita idonta tafara magana cikin ban tausaye."Dad kanawa Allah ka tausayawa rayuwata ka barni na aure wanda zuciyata ke so. Dad wallahi Allah bernde am Musaddik tan yidi mbanga,useni dad listen to me..."
Bata ƙarasa ba cikin jin zafin maganar da take Mom ta ce.
"Anya Fatima wodi semtende fulbe a gite ma bo? Ado hulna am fa.
Yarinyaa sai kace ba Fulani suka haifeta ba"Dad ne ciki da jin zafin abinda ƴarshi keyi ya ce
"Shamsiya barta tayi duk abinda taga dama amma ta sani, I have promise my self that no one can stop this marriage. Zanyi murna ace idan aka kaiki ki kashe kanki dan haka shizai iya zama min farin ciki da samun ƙwanciyar hankali."
Yana maganar ne kamar zaiyi kuka. Duk wanda yaga babban mutum kamar Dad bazayi tunanin ƴa ɗaya zata gagareshi ba.
Yana gama magana ya juya ya fita duk suma suka mara mashi baya amma banda Faruok da yake zaune ya ɗaura hannuwanshi duka saman kai...Urs mrs omar...
Love u all my fans
YOU ARE READING
NADAMAR DA NAYI
ActionNADAMAR DA NAYI labari ne da yake d'auke da NADAMAR yaudara ,cin amana da dai sauransu. Labari ne a kan wata yarinya da ta fada soyayyar wani makaho iyayenta sukaki amincewa, suka aurar da ita ga dan uwanta amma daga karshe....