*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*NADAMAR DA NAYI*
_WRITTEN BY_
*MRA OMAR*_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*_page ɗin yau naku ne *NAGARTATTUN MATA* princess Amrah Hafsat m Shariff. Aunty jegal. Aunty Maijiddah Musa. Allah yabar ƙauna._
_PAGE 8_
Zuciyarshi ke mashi wani irin k'una kamar wuta da za'a fasata da tabbas sai anyi mamaki.
A hankali ya ɗago jajayen idanunshi da suka koma kamar gauta, ya sauke su kan fuskar Fatima da take zaune a inda su Dad suka barta itama hawaye ne kawai ke kwaranya akan fuskarta.
A hankali Faruok ya taso daga inda yake zaune ya koma dai-dai inda Fatima take zaune yasa hannunshi acikin nata ya haɗe waje ɗaya.
Tadawo kamar hoto ko tadago ta kalleshi cikin sanyin murya mai kama da maijin k'iwuyar magana ya fara bata baki."Haba! mace ɗaya tak tauraruwar matan fulanin Yola.
Sudai fulanin ansansu da kunya kawaici da kauda ido daga duk wani abinda zaisa mutane suyi fushi dashi kafin ma azo ga iyaye.
Haba! Fatima ina hankalinki da tunaninki yake?" please don't forget u are a real Fulani.Muryar shi ne tayi sanyi ita ko tunda yake magana idanuwanta na kallon ƙasa suna aikin zubar da hawaye.
Hannunsa yakai dai-dai fuskarta hawayen ta na sauka akan tafin hannunshi.
Ya ce
"Fatima yanzu bakisan wannan hawayen dake fita a idonki jinsa nake kamar ana watsa min tafasashe ruwan zafi acikin zuciyata.
Wallahi Fatima duk wani motsi naki yana tafiya ne da bugun zuciyata, kece gatana please ki amincewa buk'atata da kuma umarnin iyayenmu.
Fatima ado Lara ko a wadinta danyobe amin do hani bo? No!! Fatima ya kamata ki duba wannan Lamar.."Maganarshi ta tsaya ne dan ganin ta ɗago jajayen idanunta ta sauke su kan nashi .
Libs ɗinta ne ta cije masu kamada tashafa masu pink din jan baki, ta girgiza kai ta zare hannunta dake cikin nashi sannan ta fara magana cikin fushi."Ya Faruok har kana da bakin magana kace wai nayiwa iyayenmu adalci.
Su adalci sukayi min da har suke shirin rabani da rayuwata.
Anybody that is thinking of separating me from musaddiq I will never forgive him no matter who he is,that's my promise. Sai naga inda k'arfina ya kare.
Yaya Faruok tun lokacin daka faɗawa iyayenmu kana sona na dauki k'in duniya na ɗaura maka, ada ina maka wata irin girmamawa ina tunanin duk abinda kake min kana min ne kawai dan ka ɗaukan tamkar kanwarka wadda kuke ciki ɗaya."Murmushi takaici yayi kafin yayi k'arfin halin cewa.
"Fatima inasonki daukeni kamar yanda kika dauke ni da ki min kallon kima da mutumci."
"Humm Faruk ai jotta a mara mangu a gite am tunda a yidi a senda am be yide bernde am walla"
Bata karasa ba Faruok cikin zafin rai ya fincikota da ƙarfi ta faɗa jikinshi.
Suna jin saukar lumfashin juna idonshi na kan nata da sauri ta lumshe ido.Fatima yanzu ni kike faɗawa baki ganin kimata da mutumci daga nace ina sonki?
Any way idan harda gaske kike abinda kika fada open ur eye ki koma maimaita abinda kikace nayi maki alk'awarin ni nasan abinda zanyi."Ƙara rumtse idonta tayi dan ganin kamar yana son haɗa bakinshi da nata.
Murmushi yayi ya saketa yace"Marar kunyar karya.
Fatima har yanzu ina ganin kunyar fulani a idonki please! Fatima kada ki bari soyayya ta rufe maki ido. Kizo kiyi NADAMA nan gaba."Saida ta sauke murmushin takaici kafin ta ce.
"NADAMA Yaya Faruok a kan auran Musaddik babu wannan ranar insha Allahu. Auren kane kawai zaisa nayi NADAMA amma banda auran Musaddik ai shi arziki nufin Allah ne."
"Au har yanzu kina nan kan bakanki baki canza ba kenan"
"In canza? Humm Faruok kenan ai bazan taɓa canza hali ba har saika janye maganar aurena a kanka ka barni na aure zaɓin ruhina."
"Humm Fatima kenan ki daiyi tunani."
Har ya juya zai fita ya dawo ya ce.
"Mi nani Fatima a volla pat ko a yidi.
But I want you to think much and bring out the truth."Yana magana yana nuna kanshi da dan yatsanshi. Sannan ya juya ya fita da sauri kamar zai tashi sama.
A hankali ta sulale ƙasa rana kuka.»»»«««°°°°°=°°°°°°»»»»»»««««
Tsohowa ce mai kima nin shekara tamanin da wani abu take bakin murhu tanata faman hura wuta, amma wutar sai hayaki take.
Gida ne dai ginin bilo da bilo amma dai babu filista a bango ƙasan gidan shafe yake da saminti, gidan ba wani babba bane ɗaki biyu ne sai wani daga bakin ƙofar shigowa ciki.
Tana cikin fama da wutar ne Musaddik da yaron dake tare dashi suka shigo tana jinsu ta ɗago kai da sauri tana kallonsu.
Dai-dai inda take Musaddik ya iso yace."Maman kakas me kiketa faman dafa mana haka?"
Fuska ta yatsina kafin tace
"Anya Musaddik wannan rayuwar daka ɗaukarwa kanka mai ɓilliwa ce? A ce Kai ba ganni kake ba baka iya zaman gida kullum yawo.
Anya musaddik ta be viya wodi ko memi hore mada fa.
Wallahi Musaddik a nasta hakkilo mada.""O0!! Haba mama am jotta wodi ko a lari mi wadata vodai na?
Kinga mama mubar wannan magana nikam wallahi yunwa nakeji.""Au inda kaji yawon basu baka abincin ba?"
Kai Musaddik ya girgiza sannan yasa hannu ya yamutsa sumar kanshi yace.
"Ni kam am Mama kaka wai meyasa kullum idan zaki bani abinci sai kin min gori?"
"Saboda Musaddik yanzu baka da zuciyar nema tunda ka samu matsalar ido ka taro ka lalace nace maka ko ƙofar gida ka fara wata sana'ar amma ka k'iya kullum sai faɗa min kake kuɗi sun kusan zuwa amma har yanzu banga alama ba."
Bakin ƙofar ɗakin Mama kaka ya zauna kafin ya fara magana cikin sanyin murya.
"Mama kaka ki ƙwantar da hankalinki insha Allahu komi yazo ƙarshe sanin kanki ne nafi kowa son na zama wani abu."
Baki Mama kaka ta taɓe kafin tace.
"Allah dai ya shiryeka."
Bai ƙara ce mata kalla ba, wayanshi yayi ƙara ya ɗaukota daga aljihu ko ba'a faɗa mashi ba yasan mai kiranshi.
Cikin isa ya ɗaga ya k'anga a kunne sautin kukanta ya dake kunnansa da sauri ya dan janye wayar daga jikin kunnen nashi saida ya yatsina fuska kafin yace....Nice dai mrs omar
YOU ARE READING
NADAMAR DA NAYI
ActionNADAMAR DA NAYI labari ne da yake d'auke da NADAMAR yaudara ,cin amana da dai sauransu. Labari ne a kan wata yarinya da ta fada soyayyar wani makaho iyayenta sukaki amincewa, suka aurar da ita ga dan uwanta amma daga karshe....