*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*NADAMAR DA NAYI*
WRITTEN BY
*MRS OMAR*STORY BY
*HAUWA M JABO*DEDICATED TO
*BEEBAH LUV*
_Page 5_
Tsaye yake dai_dai harabar gidan su Fatima gidan da ya amsa sunansa gida. Dakaga gidan kasan gidan attajirin mai kuɗi ne wanda ya tada kai da naira dakaga gidan zaka tabbatar da gidan suda talauci har abada sunyi hannun riga dashi, kai basu ba har ya'yan ya'yansu basu ba talauci sunyi hannun riga dashi saboda a kalla gidan zaikai 500billions saiga wasu matsiyatan motoci a harabar gidan a kalla duk ɗaya zatakai 30million ko wace da colour ta. Gidan dan k'yau yayi k'yau ba'a magana. Shikam matashi ne fari dogo yana da dan jiki fari ne tas yana da hanci babu laifi ga saje kwance a fuskarshi banga colour ɗin idonshi ba saboda rufe suke da bakin glass. Dai_dai inda yake tsaye gefe ɗaya ga roba_roba wani matashin yaro na zaune a kai da alama shi yaron ya kawo akai. Basu wani 6ata lokaci ba Fatima ta fito direct wajansu ta nufa yana yin yanda fuskarta ta faɗaɗa murmushinta ne ya tabbatar da cewa wannan matashin saurayin mai glass shine Musaddik.
"Nayi fushi ai ji nake baka zuwa?"
Murmushi yayi ya fuskanci ta tamkar yana kallonta cikin sanyi murya ya fara magana.
"Haba sweetheart wane ni ai dole nazo naga lafiyar Sahiba ta saboda na tabbatar da yau an 6ata mata rai."
Ɗan gyarawa tayi daga inda take ta ɗan jingina da motar dake kusa dasu ta ce.
"Humm Musaddik Dady naso ya ruguzamin mafarkina wanda a kullum nake fata ya zama gaskiya. Dan banda wani buri daya wuce na auranka a duk halin da kake ciki.. Humm saidai iyayena nason rabani da farin cikin ruhina."
"Fatima ki amince to kawai zaifi."
Yana faɗin haka tamkar ya faɗa mata sakon mutuwa tayi wata zabura ta kalleshi shima dukda ba gani yake ba fuskarshi na fuskantar tata. Take hawaye ya fara bin fuskarta cikin muryar kuka take magana yanzu.
"Haba Musaddik ya zanyi da rayuwata ko kasan sonka zai iya rabani da rayuwata a duk lokacin da na wayi gari na samu kaina a d'akin wani namiji ba kai ba? to wallahi ina faɗa maka a ranar zan...."
"Humm dakata Fatima."Ya ɗaga mata hannu tamkar yana kallonta shima ya fara magana cikin zafin zuciya.
"Fatima kenan ai keke iya faɗin abinda ke zuciyarki dan kuwa idan ni nake fad'in abinda ke cikin zuciyata to tabbas da yanzu saidai aga gawata a k'asa, Fatima ai ke mace ce tamkar ke d'aya ce mace a duk duniya fatima kece farin cikin ruhina hasken zuciyata, kece mace ta farko dana faraso a duniya, ina rokon Allah duk lokacin da idona ya buɗe na fara saki a idona, dan ke tauraruwar duk mata ce duk da bansan fuskarki ba amma na tabbata ke kyakkyawa ce."
Ɗan shiru yayi ya numfasa kafin yaci gaba da magana.
"To wai Fatima dan me Dad ke son rabamu ko dan ya ganni makaho ba ido? Wayyo Allah Fatima zuciyata zata buga.."
Da sauri ya dafe zuciyarshi saura kiris glass ɗin fuskarshi da ya faɗi k'asa. Da sauri Fatima tasa hannu ta tallaboshi wanda yayi dai_dai da fitowar Dady a harabar wajan can ya tsaya yana kallonsu cikin 6acin rai yayi mata wata irin gigitaciyar tsawa wanda tasa jikinta ya fara rawa. Daga window ɗakin Faruok yaji tsawar da Dady yayi mata da sauri shida Mom suka nufi hanyar waje da sauri ciki zafin rai Faruok ya nufi inda Fatima take tsaye dan ganin duk illa hirin jikinta na kan jikin Musaddik harta dukiyar fulaninta na gogar gefan jikinshi. har zuwa yanzu tana rike dashi Tana kallon su. Wata irin wawar fizga Faruok yayi mata da k'arfi ta faɗa saman kirjinshi cikin zafin zuciya ya ɗago fuskarta daga samanshi yana magana kamar zai ɗaura hannu a ka yayi kuka.
"Fatima are u mad? Kina hauka ne har zaki kama wani kato a cikin gidan nan gaban idonmu."
"Wallahi Yaya Faruok kada ka k'ara kiran Musaddik wani kato ko ka manta Musaddik mijin da zan aura n.."Bata karasa maganar da take ba ta diga jin saukar mari a fuskarta. Dady ne cikin fushi haɗi da zafin zuciya, wata irin shaka yayi mata yana faɗi.
"Ki kuma maimaita abin da kika ce i said repeat what you said again,
Shakar da yayi mata ne idonta duk sunyi waje yasa Faruok yayi sauri ya faɗi k'asa yana bashi hakuri itako Mom tsaye take kamar hoto ta kasa komi juyawar da Faruok zaiyi yaga yaran da yazo da Musaddik ya ɗaukeshi har sun bar harabar gidan. Kallon daya zakayiwa fuskar Dady ka tabbatar da ranshi ya 6ace sosai. Rukon da Faruok keyi masa ne yasa a hankali ya saketa yana huci ya fara nunata da yatsanshi.
"Fatima tunda naga take_takenki bamai karewa bane zan kawo karshenshi tunda ina tausaya maki baki gani yayi k'yau. Sati mai zuwa insha Allahu za'a ɗaura maki aure da Faruok idan yaso sai ki mutu idan anyi."
Wata irin k'ara Fatima ta fasa kamar an aiko mata da sakon mutuwa ta faɗi k'asa tana faɗi.
"Please Dady kada kayi min auran dole wallahi idan na auri Yaya Faruok mutuwa zanyi please Dady help me."
"Aikin banza ai ni dama nafi son idan an kaiki to a kawo min gawar taki zaifi da irin wannan abin kunyar da kike so nayi."
Kafarshi taje zata kama yayi saurin janyewa yabar wajan da sauri Mom ta mara mashi baya. Wani irin tausayinta ne yakama Faruok take yaji zuciyarshi ta karaya a hankali ya nufi wajanta yasa hannu zai kamata cikin zafin rai ta ce.
"Stop ya Faruok don't touch me."
"Why?"
Hon din da akayi ne yasa sukayi saurin juyawa dan ganin ko waye..
YOU ARE READING
NADAMAR DA NAYI
ActionNADAMAR DA NAYI labari ne da yake d'auke da NADAMAR yaudara ,cin amana da dai sauransu. Labari ne a kan wata yarinya da ta fada soyayyar wani makaho iyayenta sukaki amincewa, suka aurar da ita ga dan uwanta amma daga karshe....