NADAMAR DA NAYI 24

143 6 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

      *NADAMAR DA NAYI*

            _WRITTEN BY_
            *FATIMA ISAH*
           ( _MRS OMAR_)

             _STORY BY_
         *HAUWA M. JABO*

            _DEDICATED TO_
              *BEEBAH LUV*

              _Page 24_
            ***********
             

Shiru captain Bilal yayi yana kallon Faruok dan ya rasa inda zaisa kansa domin kuwa Faruok ya gama ɗaure mashi kai.

"Bilal please talk to me, nasan wannan damuwar tawa kai ne kawai zakayi min maganinta please kada kace a'a."

Hannun Bilal Faruok ya kama ya rike gam.
  Kai Bilal ya girgiza ya ce

  "Oh my God major ina ma ace mafarki nake da nayi murna sosai, sai gashi alive ne, major kayi min komai a rayuwata babu abinda zakazo dashi naqiyi maka muddin ina dashi naji na amince zan auri Fatima amma badan ina sonta ba zan aureta ne kawai a bisa umarninka."
"Naji nagode."
"Amma akwai babbar matsala major taya zamu fuskanci Dad da wannan maganar?"

Ajiyar zuciya Faruok ya sauke sannan ya cije lips ɗinshi na ƙasa ya ce.

"Wannan ba wata matsala ba ce matsala ta ɗaya Fatima shine wane irin zama zakuyi da ita dan Fatima nada taurin kai sosai."
"Kada ka damu major zan iya hakuri da ita zan shanye duk wani wulakanci da zan fuskanta daga wajanta zataci albarkacinka dan bazan iya wulakanta duk wani abu dayazo ta hannunka ba."
"Ka daina irin wannan maganar Bilal sanin kanka ne yanzu ka zama ɗan uwana na jini dan haka bana so ka dinga tuna baya."

Murmushi takaici Bilal yayi sannan ya tashi tsaye saida yayi tafiya da bazata wuce taku uku ba ya tsaya ya kurawa wani katun pic nasu dake manne jikin bango.
Ido ya lumshe kana can yayi murmushi ya ce.

"Major kenan shege ne kawai ke manta alkhairi a rayuwarsa dan haka i will never forget u in my life."

  Tashi Faruok yayi shima ya taka ya isa har inda Bilal yake ya dafa kafaɗarsa ya ce.

"Bilal zan iya yi maka komi a rayuwata dan yanzu ka zama ɗan uwana ina maka kallon ɗan uwana wanda muka fito ciki ɗaya dan Allah ka daina tuna baya."

Juyowa Bilal yayi ya kalli Faruok saura kiris hawayen da yake maidawa su fito ya ce.

"Naji major nagode insha Allahu ranar data gama ida sai a ɗaura."
"Insha Allahu."

Haka suka dinga fira sama_sama har Bilal ya manta komi..

*****

Kwance yake cikin bathtub ya cikata da kuffa kanshi sama idanuwansa a rufe tunani kawai yake yanda zaije ya fuskanci Dad da maganar abokin shi bilal a hankali ya firta.

"ya rabbi please get me out of dis problems. I known my Dad can accept anything but..."

Sai kuma yayi shiru yana girgiza kanshi.
A hankali ya fara buɗe idanunsa amma dakaga fuskar Faruok kasan yana cikin matsala murmushi yayi mai ɗauke da karfin hali.
Jikinshi ya wanke a hankali ya fito daga cikin bathtub ɗin ya ɗauki towel yana goge jikin shi bayan ya gama ya ɗauki wani ya ɗaura fitowa yayi bedroom dinshi ya zauna dai_dai inda pic ɗin Fatima yake ya ɗauka yana shafa fuskarta take hawaye suka fara fita daga cikin idansa ya zuwa fuskarsa ido ya lumshe ya ce.

"Fee why did u do dis to me? Just because i love u so much? which  made me promise myself to do anything to make you happy, ina ma zaki soni kamar yanda nake sonki oh ya rabbi please give me strength to pass through this problems "

Ya faɗa a hankali ya saka pic ɗin a kirjinshi yana mai sauke numfashi a hankali ya faɗa kan gadon yana mirgina...

Fatima kai tsaye
Peace hospital ta nufa asibitin na kusa da unguwarsu mafias quarters. Direct office ɗin doctor Sadiq ta nufa kasan cewa su basa tsayawa jiran doctor domin shine family doctor ɗinsu a hankali tayi knocking kasan cewar tasan koda yaushe  office ɗinshi yana tare da patient a hankali taji ya furta

"Yes coming."

Hannu tasa ta tura ƙofa zuciyarta cike da fargaba.
Kai ya ɗago da sauri dan ganin mai shigowa take ya saki fuska yana faɗin.

"Hajiya Fatima kenan Amarya a gidan major Faruok kece da kanki."

Fuska Fatima ta ɗaure danjin ya ambaci sunan Faruok a zuciyarta tana dana sanin zuwa hospital ɗinshi.
Murmushi yayi dan ganin ta ɓata fuska dukda baisan abinda ke faruwa ba yayi karfin hali cewa.

"Am sorry ga waje ki zauna."

  Ya nuna mata kujerar dake fuskantarshi.
Bayan ta zauna ya aje pen ɗin dake hannunshi yana faɗin.

"Amarsu what is ur problem?"

Dan shiru tayi tana mai jin kunya sai da doctor Sadiq ya ƙara maimaita maganarshi kafin ta ɗago kai tana kallonshi.
   Ajiyar zuciya ta sauke sannan kamar an fizgi maganarta ta ce.

"Pregnancy test nazo kayi min"
  Murmushi yayi yace
"Yaushe raban da kiga menstriation ɗinki?"
  Kai ta sada ƙasa cike da kunya ta furta
"One month one week."
   Kai ya girgiza ya ce.
  "Yanzu kina tunanin maybe kina da ciki?"
Kai ta ɗaga mashi.
"Alright let me do the test for you."
  Ya mika hannunshi yana mai ɗauko wata rubber fara 'yar kara ma ya bata.
Toilet ya nuna mata ya umarceta dataje tayi fitsari ta kawo mashi, ba musu ta ajiye hand bag ɗinta ta shiga.
Bata wuce 30 minutes ba ta fito rike da kwalbar ta aje gabansa baiyi magana ba ya danna wani abu dake gabansa ba a wani ɓata lokaci ba nurse ta shigo da sauri.

"Aisha da Allah ki ɗauki wannan yanzu nan kikai lab ayi pregnancy test ki kawo min result ɗin yanzu ina jiranki."
"Ok sir"

Aisha ta ɗauka tana sauri yanayin da doctor Sadiq yaga Fatima ne jikinta yayi sanyi yasa bai kara ce mata komi ba yacigaba da 'yan rubuce_rubucenshi.
Ba'a wani ɓata lokaci ba nurse Aisha ta dawo da takarda a hannunta tana zuwa ta mikawa doctor Sadiq, amsa yayi yana dubawa a hankali ya ɗago kai yana murmushi ya cewa Fatima.

"Amarsu ta ango Congrat.."
   Bai ida rufe bakinsa ba Fatima ta tashi tana faɗin.
"What doctor don't tell me am pregnant please."
  Baki doctor Sadiq ya buɗe yana kallonta kai ya girgiza ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.....

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now