NADAMAR.. 11

159 11 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*NADAMAR DA NAYI*

_WRITTEN BY_
*MRS OMAR*


_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*

_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*

_Toh page ɗin yau naku ne masoya wannan littafin na baku shi kyauta ina jin daɗin yanda kuke bani haɗin kai kuna comment a kowani page da nayi post thank u all_

_PAGE 11_

Da sauri Major Faruok ya rufe idanunshi babu abinda yake firtawa a bakin shi sai.

"Innalillahi wa'inna illaihi raji un lailaha illa anta subahanaka inni kuntu minaz zalimin."

Abinda kawai bakinshi ke nana tawa kenan cikin karairaya Hafsat ta iso gaban Faruok tana wata rangwaɗa kamar zata karye.
Shidai Farouk idanunshi a rufe suke ya kasa buɗesu.
A hankali tasa bakinta ta hura mashi iskan bakinta, take ya karajin jikinsa ya mutu, ya fara nai man rasa natsuwarsa.
Bakinta takai dai_dai kunnanshi ta ce.

"Please Ya Faruok help me I can't control my emotions because i love u so much, Ya Faruok yakamata ka gane ni ce mai sonka please,wallahi komi kake so yau a shirye nake zan bak.."

Hannunta ta kai dai_dai sumarshi cikin wani irin salo mai wuyar fasarawa da sauri Faruok cikin fushi ya fincikota ya haɗata da bango ya maida hannunta baya ya murɗe yana magana tamkar baya cikin hayyacinsa.

"Wa'iyazu billahi Hafsat tur da halinki lamarinki har yakai haka kina shirin bada kanki ga namijiin daba muharraminki ba? Tur!! Hafsat tur da halinki a haka har kike tunanin ni Faruok zan aureki bayan bansan yawan mazan da kika bawa kanki ba.
Lallai Hafsat a hilni am de har a numata mi wawai mi mbangu ma 6awo a andi Nana a debbo m6angugo am ba. Wallahi kinyi asara."

Da ƙarfi Major Faruok cikin ɓacin rai yayi wulli da ita saman katifa. Sai mai da lumfashi yake da sauri da sauri zuciyar yan maza ta ɓace dama Faruok tun yana yaro bai iya fushi ba.
Abinka ga marar kunya irin Hafsat ta ƙara nufar Faruok yayinda idanunta suka canja launi.

"Ya farouk yide ma on wati mi wawai mi hokkuma ko dumejun on gam mi he6a a m6anga am.
Haba Ya Faruok ya kake so nayi da rayuwata wallahi tunda na tashi a gidan nan nake saka idona nake burin kazama mallakina please Ya Faruok listen to me.."

Hannu ta kuma kaiwa dai_dai bakinshi kafin ta rufe baki Faruok ya kai mata wani wawan mari cikin fushi.

"Never!! Hafsat i will never listen to dis stupid ideas of yours.
Humm Hafsat dole naso Fatima saboda ita mai tarbiyya ce halinku ya banbanta duk namijin kirki yana so ya zaɓawa Ya'yanshi uwa ta gari, Hafsat wallahi ke ce kika dace da Musaddik ba Fatimata ba."

Magana Faruok yake kamar zai ɗaura hannun saman kai ya fasa ihu.
Wata irin tsawa ya daka mata ya ce.

"Hafsat get out of my room before I make your life miserable, Stupid girl, fool kawai!"

Shiru tayi tana kallonshi Faruok cikin zafin zuciya ya fincikota yayi waje da ita da ƙarfi ya wulli da ita ya maida ƙofa ya rufe.
A hankali ya dawo bakin gado ya zauna yayin da ya lumshe idonsa yana fad'in.

"Why!! Hafsat why did u do this to me. Kinsan irin wahalar da nake idan naga tsirancin mace? Wayyo Allah Hafsat kin cuce ni."

Da sauri ya rike cikin shi yana mirgina kan gado juyi kawai yake ya rasa inda zaisaka kanshi.

Yana tura Hafsat waje Aunty Zee ta fincikota suka nufa ɗakin Mom ɗinsu.
Suna shiga cikin fushi Aunty Zee tayi jifa da Hafsat kan kujerun parlour ɗakin zaka ɗauka Aunty Zee zatayiwa Hafsat hukunci ne akan abinda tayi amma abin mamaki daga ita har uwar magana daban suke, cikin zafin rai Aunty Zee ta fara magana kamar zata kaiwa Hafsat duka.

"Hafsat u a very stupid girl, duk abinda muka faɗa maki yanzu ya tashi a banza kin kasa shawo kan Faruok kinsan ko idan kika bari Faruok ya aure Fatima munyi babbar asara? See u kamar zakiyi wayau amma a banza baki dashi, ni wallahi dan Faruok ba sa'an aure na bane amma wallahi dasai na baki mamaki."

Mom ɗinsu ce ta taɓe baki ta ce.

"Humm ai wallahi Hafsat lamarinki akwai gyara, me Fatima zata nuna maki da har kika kasa shawo kan Faruok duk abinda muka faɗa maki a banza.
Bamu ce maki ki bashi kanki ba.
Amma mun ce kiyi duk abinda zakiyi dan shawo kansa kin san ko irin dukiyar da Faruok ya mallaka yanzu? Kai!! Wallahi Hafsat kada ki yarda Faruok ya auri Fatima."

Cikin muryar kuka Hafsat ta fara magana.

" Mom Aunty Zee u know Ya Faruok Duk abinda muke yana sane damu, wallahi nayi duk abinda zanyi dan ya amince dani amma abin haushi har da fad'i yake wai ni ba matar auransa ba ce saboda banda tarbiya."
"OK haka ya ce alright to idan yasan wata baisan wata ba."

Cewar Aunty Zee kenan. Sun daɗe suna tattaunawa kafin daga baya dukansu ko wace ta kama gabanta.

★★

Kafin a ce maka me Faruok zafin zazzabi ya rufe shi sai juye yake.
Babu abinda yake bayan faɗin sunan Allah a bakinshi hannuwansa duka biyu na kan marar sa.
A hankali aka turo ƙofa. Idanunsa a rufe suke shiyasa bai shaida wanda ya turo ƙofar ba....

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now