NADAMAR DA NAYI 25

170 11 0
                                    

AGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

            _WRITTEN BY_
             *FATIMA ISAH*
               ( _MRS OMAR_)

               _STORY BY_
          *HAUWA M. JABO*

             _DEDICATED TO_
               *BEEBAH LUV*

  
                _PAGE 25_
                 **********

Duk sanyin Ac dake office ɗin doctor Sadiq amma Fatima zufa ce ke fita daga jikinta.
Zama doctor Sadiq ya gyara kafin ya ce.

"Please calm down Fatima ba ina nufin kina da juna biyu ba ne, kawai dai naga kamar baki shirya ɗaukar ciki bane yanzu shiyasa nake maki albishir ba babu komi, dan haka ki kwantar da hakalinki"
"No doctor that's impossible kada ka ɓoyan ina da ciki."

Murmushi yayi ya ce.
"To nidai abinda sakamako ya nuna min kenan amma ina tunani wannan ba abin damuwa bane domin kuwa yakan canza lokacin zuwa, ba dole sai lokaci da yake zuwan maka ba maybe kema haka yayi, ki kwantar da hankalinki zakice amarcinki hankali kwance.."
Doctor Sadiq ya kai karshen maganar shi yana dariya.
"To amma doctor babu abinda zaka ban nasha dan yazo."
Ido doctor Sadiq ya kora mata cike da mamaki ya ce.
"To amma Fatima meye abin dawuwa bayan idan ma cikin ne dake yana da ubansa ko major ne bai shirya haihuwa yanzu ba?"
Shiru tayi tana tunani can ta girgiza mashi kanta.
"Ok anyway zan baki sati biyu idan har kinga baizo ba zaki iya dawowa sai ai maki blood text."
Fatima bata kara cewa komi ba sai dai kawai tayi mashi godiya ta fita.
Tana fita kiran Musaddik na shigowa wayarta da sauri ta ɗauka tana mai sakin murmushin jin daɗi.

"Amincin Allah ya tabbata a gareka yakai kyakkyawan basaraken zuciyata."
Ajiyar zuciya Musaddik ya sauke ya wani ƙara kashe murya ya ce
  "Tare dake hasken ruhina tauraruwar dake haska min zuciyata, jin muryarki kawai ke rikita min zuciyata naga ranar da zan ganki ido da ido wash, da a ranar sai nayi azumi nayi sadaka duk dan nagodewa Allah da ya bani idon ganin abar so na."

Ido Fatima ta lumshe har ta manta da inda take dan jin kalaman Musaddik masu kashe jiki. Maganar shi ce tasa ta buɗe idonta a hankali.
"Hubby ko bakya son idona su buɗe ne dan kada na kara maki kishiya?"
"Noor Hayat ɗina kenan a duniya nafi kowa son idanka ya buɗe domin kuwa zan nunawa duniya nafi kowa sa'ar miji, dan banda burin da nake yanzu irin naga na cika maka burinka."
"Ina sonki uwar ya'yana ina ma duka haka matan duniya suke da irin halinki da maza sunyi sa'a."
"Ni nafi kuwa sa'ar miji kamarka domin kuwa duk wasu mazan duniya kallon mata nake masu.."

"Da izininwa kike waya da wani kato ko kin manta da aure na a kanki?"

Kai Fatima ta ɗago tana kallon Faruok dan ita kwata_kwata bata ɗauka da mutum a wajen ba domin hankalinta duk ya tafi wajan masoyinta.
"Magana nake maki kika tsaya kina kallo na."
Wayar tayi sauri ta tsinke dan kada Musaddik yaji abinda ke faruwa.
Sai da ta saka wayar cikin hand bag ɗinta kafin ta saki murmushi ta ce.

"Yaya Faruok kenan a kullum kana bani mamaki idan wannan makauniyar zuciyar taka ta kitsa maka ka kira ni matarka, shin wai ko mafarki kake lokacin da ka sake ni? ka manta ni yanzu nan da saura wasu kwanaki na mallaki abin kauna ta."
"Amma ai kuma kada ki manta har yanzu ke matata ce."
"Taya na zama matarka ko ka maida aurenmu dukda saki ukun da kayi min, dan in sani saboda ba a kanka aka fara maida mace ba a lokacin da akayi mata uku."
"Fatima ni ba jahili bane da ilimi na nasan abinda nake amma ya kamata ki dinga kiyaye dokar ubangiji domin kuwa kema kinyi karatun nan."
"Kaga ya Faruok dan Allah ka barni wallahi ko a mafarki bana so na kara ganinka a rayuwat.."
"Why?"

Ganin Faruok na nufarta yasa ta fara baya_baya amma bata san motarshi na wajan ba har saida ta jingina da motar.
Runfa Faruok yayi mata yana bin duk jikinta da kallo da rigar data saka ta fito mata da dukiyar fulaninta mai ɗaukar ido.

"Saboda ni na zama mugo shiyasa bakya so ki ganin a rayuwarki amma ki sani har gobe mutane zasuce nine mijinki na farko nine na fara saninki a ƴa mace.
Fatima dama soyayya na zama kiyayya? Cewa fa nayi ina sonki amma bai.."
"Ya Faruok kenan ai ni duk duniya yanzu bani da babban maqiyi sama da kai tunda ka rabani da abun qaunata."
"Amma kuma kada ki manta ni ɗan uwanki ne na jini saboda idan aka tsaga jikinki dole za'a samu jinina a naki"
"Banda wani ɗan uwa namiji ƴan uwana basu wuce su Anty Zee ba sune ƴan uwana na jini bakai b."
Duk amsar da Fatima ke bashi idanuwanta a rufe suke take bashi amsa shiko bakinta kawai yake kurawa ido idan tana magana, ido ya fara lumshewa a hankali ya fara kai bakinsa ga nata yana magana kasa_kasa.

"Idan har da gaske kike bakya sona ki buɗe idonki ki kalli cikin idona ki faɗan bakya sona idan ko ba haka ba yau babu wanda zai rabamu dake."

Ido Fatima ta buɗe da sauri danyi abinda ya faɗa sai taga yana ƙokarin haɗa bakinsa da nata da sauri tasa hannuwanta biyu ta ingijeshi tana faɗin.
"Wai kai meke damunka nace bana sonka bana kaunarka wai shin dole ne wai? wallahi idan da za'a bani wuka ace na kashe maqiyina to da kaine na farkon kashew.."
Bata ida magana ba Faruok ya fincikota da karfinsa yana faɗin.
"So u want to kill me? ok no problem kill me, zan so ace ke kika kashe ni da hannunki dan na tabbatar da kiyayyar da kike min."
"Ya Faruok ka sake ni."
"Saki bayan wanda nayi maki kike bukatar wani."

Tsaki tayi ta ce.
"Aikin banza"
"What?me kika ce?"
"Mefa na ce."
Fatima ban faɗa maki ba kada ki ƙara zagina?"
Banza dashi tayi tana ƙokarin kwatar rukon da yayi mata dan ma Allah ya taimaka wajan babu jama'a.
"Ina kika je ne naganki a nan?"
Shiru tayi bata ce mashi a mutu ba.
"Magana nake maki badai wajan ɗan iskan nan zakije ba?"
"Oho dai ko me zaka kirashi shine dai a raina."
Hannunta ta fizgi da ƙarfi ta juya da sauri tana tafiya.
Faruok har zai bita sai kuma ya tsaya yana kallon yanda take tafiya mazaunanta na juyawa sai yaji wani irin kishinta da yake take zuciyarshi ta tunasar dashi abinda ya manta.

'A'a Faruok kada fa ka manta yanzu Fatima nan da wani lokaci zata zama ballakin abokinka ka fara ƙokarin cire ta a ranka'
Ajiyar zuciya ya sauke dan tunawa da yayi ashe wajan maganar aurenta da Bilal zaya ya faɗawa Dad mota ya shiga da sauri amma dukda haka bai daina tunaninta ba har ya isa cikin harabar gidan yayi parking ya fito yana tunaninta.
Kai tsaye ɓangaran Mom ya nufa zaune take ta buɗe wani littafin adduo'i mai suna fortress of the Muslim tana nazari ta maida hankalinta gabaki ɗaya wajan littafin.
Sallama Faruok yayi cike da ladabi Mom ta ɗago kai tana mai amsa masa cike da anashuwa.

"Barka da hutawa Mom"
"Barka dai Faruok yanzu kake tafe?"
"Allah kuwa mom"
"To yayi kyau haka ake so."

Murmushi Faruok yayi ya ce.
"Mom aikin kenan idan bakya hidimar gida to kina nan kina nazarin littattafan addinin"
"To Faruok ba dole ba ai gara mutum ya dingayi yana tunawa da lahirarsa  dan duka duniyar nawa take kana zaune kana abinda kake so sai dai kawai ka wayi gari ka ganka kabari daga kai sai halinka."
"Gaskiya ne Mom ina ma duka matan duniya irin halinki gare su"
Murmushi Mom tayi dan ta fahimci abinda yake nufi ta ce.
"Hmm Faruok kenan nawa kawai ka sani amma akwai mata masu hali masu kyau da yawa bani ɗaya ba."
"Hmm Mom kenan any way mubar wannan maganar Dad na ciki kuwa?"
"Eh kamar yana ciki dan naga dawowarsa daga aiki lafiya dai ko"
"Lafiya qlau Mom akwai maganar da zamuyi dashi to ina so dole sai kina wajan"
"To Allah yasa sirika aka samamin"

Faruok shiru dai yayi baice komi ba, da sauri ya tashi yayi gaba dariya Mom tayi can kasan ranta tana jin daɗi da Allah ya bata Faruok dan yanzu ta fara cire lamarin Fatima a ranta.

Faruok ya fara isa ƙofar Dad dan haka yayi knocking Dad yace ya shigo tare suka shiga da Mom.
Bayan sun gaisa Dad ya ce.
"Lafiya dai ko faruok?"
"Lafiya qlau Dad dama akwai wata magana dana zo maka da ita"
"To masha Allah ina jinka."
"Dad dama alfarma nazo kayi mana akan abokina Bilal."
Sai koma yayi shiru yana kallon Dad
"Ina jinka wani abu ya faru dashi?"
"A'a Dad dama.. Dama Dad nazo ne akan na rukan masa alfarmar auran Fatima.
"What kana nufin auran kisan wuta zakuyi?"
Mom ta faɗa shiko Dad ido kawai ya bisa dashi.
Zama ya gyara yana fuskantar Mom ya ce.
"Ba haka bane mom"
"To idan ba haka bane to ya kake nufi?"

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now