NADAMAR.. 18

164 12 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

    *NADAMAR DA NAYI*

             _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

             _STORY BY_
     *HAUWA M. JABO*

          _DEDICATED TO_
          *BEEBAH LUV*

_This page is for you my dear friend shatu na_.

              _page 18_

Ido Faruok ya lumshe yana mai murmushin zuci ya faɗa kan kujera.
Jiki a sanyaye aunty Zee ta fita a gidan.
Fatima tana shiga ɗakinta ta faɗa kan gado ta ɗauki wayarta  ƙirar iPhone xs max8, tana kuka ta danna number Musaddik tayi mashi miss call ya kai goma amma baiyi picking ba.
Kuka ta kuma fashewa dashi ta fara surutu Marat amfani.

"Why? Musaddik why are u doing this to me,haba, ko ka manta duk wani motsi nawa da naka yake tafiya. please Musaddik kada ka ida sa zuciyata ta buga"

Kuka tacigaba dayi har tana buga pillow kan gadon da take saida tayi mai isarta kafin barci ya  ɗauketa bata wani dade sosai ba taji muryar mutane harda Pendo Ummi da sauri ta diro daga kan gado ta nufi ƙofar ta buɗe tana fita tayi ido biyu da Pendo Ummi da gudu ta ida nufa wajanta ta faɗa jikinta, itama Pendo Ummi kamata tayi tana dariya.
Ita kanta Ummi ta yaba da gidan uwa uba jama'ar da sukazo a tare suma sun yaba gidan sosai, bayan sun dan zauna a parlour daga bisani Ummi taja hannu Fatima suka nufi bedroom ɗinta ta zaunar da ita, lokaci ɗaya Pendo Ummi ta ɓata fuska ta koma kamar bata taɓa yin dariya ba.

"Fatima kin bani mamaki yanzu duk abinda aka faɗa maki bai shiga kunnanki ba? duk abinda aka faɗa maki yabi ta bayan kunnanki ya fita, wallahi ban taɓa tunanin zamu haifi 'yar da tafi karfinmu ba."

Jikin Fatima ne ya fara rawa dan tana tunanin maybe ko Faruok ya kirasu ya faɗa masu abinda tayi jiya ne.
"Fatima yanzu a matsayinki na matar aure mijinki na parlour ke kina bedroom kin rufe ƙofa abinki maybe ma tun jiya kika rufe mashi ƙofa."

Ajiyar zuciya Fatima ta sauke a hankali kafin ta ɗan kakaro murmushin karfin hali tace.
  "A'a Pendo Ummi ni na isa nace bana jin maganarku, a tare muke dashi a parlour tashi na kenan na shigo ciki zan watsa ruwa shine naji muryarku."
  "Karya kike Fatima ga fuskarki nan da alamun kinsha kuka ki faɗa min gaskiya."

Dariya Fatima tayi ta faɗa jikinta tana faɗin.
  "Allah Pendo Ummi da gaske nake ki tambayeshi kiji fuska na kuma da tayi haka kaina ke min wani irin ciwo tin da safe dana tashi."

Hannu Pendo Ummi ta ɗauka tana shafa kanta kafin ta ce.
"Allah yasa da gaske kike Fatima dan muna so ki fitar damu kunya ki zauna da mijinki lafiya dan Allah."
"Kada ku damu babu abinda zai faru."
"Allah yasa Fatima."

Tashin ta tayi daga kanta suka fita waje dan saboda mutanan da suka bari.
Babu laifi sun dan jima a gidan kafin suka tafi,har suka tafi Faruok bai dawo gidan ba.

*****

Tafiya ta fara tafiya zaman Fatima da Faruok, amma wani irin zama suke na wasar yar ɓuya bata taɓa barin su haɗu duk wata hanya da zasu haɗu dashi bari take, dan komi zatayi yanzu bata fita parlour sai cikin dare sai ta tabbatar da yayi bacci taje kitchen. Fatima ta hora kanta da yunwa saboda idan gari ya waye babu abinda take wuni sha sai ruwan tea.
Faruok tun yana zuwa ya dinga bugun ƙofa dan ta buɗe har ya daina ya gane lokacin da take dafa abinci ya barta ne kawai dan kada ta gane ya ganta.
Yau gashi satinsu biyu dai_dai da yin aure gashi lokacin komawarshi wajen aiki yayi yau Monday hutunsa ya ƙare ga halin da suke ciki shawara ya yanke kawai ya ɗauko mata mai aiki dan yanaga hakan shine mafita.
Wayarshi ya ɗauko ya rubuta mata sako kamar haka.

" _Assalamu alaikum yake tauraruwa hasken matan duniya, ya kamata ki daina azabtar dani haka ko kinsan rashi ganin wannan kyakkyawar fuskar taki zai iya sani na shiga cikin wani hali Fatima ya kamata ki gane nine masoyinki na har abada, any way yau zan koma aiki inaso kiyi min addu'a sannan idan na tafi bazan dawo ba sai 6 dan haka na yanke shawar zan samo mai aiki mace wada zata dinga tayaki zama dan Habibu shi gyaran gida kawai yake,zan bata numberki ta kiraki.nagode matata please ki kara kula min da kanki sako daga mijinki na har abada Faruok_"

Tana gama karanta sakon tayi jifa da wayar saboda gabaki ɗaya kalmarshi ta ƙarshe tafi bata haushi wai mijinta na har abada.
Fatima ta ɗauki lokaci tana kuka amma duk a banza tunda wanda take danshi baima san tanayi ba.

Faruok na fita ya tambaya maigadi inda za'a samar masu mai aiki cikin girmama irin ta baba mai gadi yace mashi yana da 'Ya budurwa bari zai turota ta dinga tayata duk abinda ya kamata Faruok yaji daɗin abinda baba mai gadi yayi mashi shiyasa ya bashi ƙyautar kuɗi masu yawa.
Faruok bai daɗe da tafiya ba baba mai gadi yaje ya taho da 'yarsa, kasan cewar Habibu na gidan shiya buɗe masu ƙofa ya nuna mata hanyar ɗakin Fatima, tana zuwa ta fara bugun ƙofa amma Fatima tayi shiru a hankali ta ce.

"Hajiya ko kina wanka nice wanda Alhaji ya turo."

Fatima har tayi banza da ita sai koma ta tuna wani abu tatashi tabuɗe kofar tana buɗewa sukayi ido hudu.
Murmushi yarinyar ta sakarwa Fatima itama babu laifi ta dan sakar mata fuska.
Parlour suka nufa Fatima ta zauna kan kujera yarinyar na shirin zama ƙasa Fatima ta hanata tace ta zauna sama.

"Ina wuni Hajiya."
Lafiya yan mata ya sunanki?"
"Sunana Habiba."
"Wow nice name, to da fatar zaki dinga debe min kewa sannan duk abinda nasaki zaki kuma zaki ɓoye min sirrina."
"Insha Allahu Hajiya."

Murmushi Fatima tayi cike da jin daɗi ta fara jan Habiba da fira dan ta saki jikinta.
Haka suka dinga hira kamar dama sun saba da juna dan Fatima na kiwar mutane sosai.
Har girki tare sukayi ita dai Fatima da suka gama bata dibarwa Faruok nashi ba abin ya dinga ba Habiba mamaki dan bata san yanda zamansu yake ba.
Bayan sun gama sallah sun dawo parlour suna hira Fatima takan trying number Musaddik ko zai ɗauka amma yaki picking.
Suna cikin hira basu san da shigowar mutum ba saidai kawai ɗaga kan da zatayi taga Faruok tsaye ita kawai yake kallo, da sauri ta saki wayar, ta miki tsaye zata bar wajan faɗi yake.

"Fatima ina zaki? kiyi hakuri zo kiyi zamanki babu ruwana dake."

Ina ai ko ta saurareshi kawai ta shige ɗaki abinta.
A hankali ya zame kan kujera ya zauna cike da sanyin jiki Habiba ma na gaidashi amma baisan tanayi ba.
Kanshi ya dafe yana tunanin zaman da sukeyi da Fatima, wayarshi ya fitar daga cikin aljihu ya fara rubuta mata sako dan yasan koya kirata bazata ɗauka ba.
Bayan ya gama rubuta sakon ya tura kawai sai yaga wayar tayi kara a ida yake zaune, a hankali ya dauki wayar yana kallon screen ɗin wayar.
Da sauri ya furta

"What? BZ.. To me wannan kalmar ke nufi? my number is BZ so what's  the meaning of that?"

Wayar ya kurawa ido yana kallon sunan data rubuta mashi.

_to makaranta Faruok fa na tambayar meaning ɗin BZ saiku bashi amsa._

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now