NADAMAR...14

187 15 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*NADAMAR DA NA YI*

_WRITTEN BY_
*MRS OMAR*

_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*

_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*

_Ina alfahari daku masoya wannan littafin haƙika kun zama jinin jikina, ina jin daɗi comment ɗinku sosai, Fulani yan uwana ina jin daɗi yanda kuke bani goyan baya, tnx Allah hokku amin Sa'a_

_PAGE 14_


A hankali nasihar Malama data Pendo Ummi ta dinga dawo mata a kunne da sauri ta rintsi idanunta gam tana fad'in.

"No!! Musaddik i can never do dis to my family.
Musaddik gonga mi wawata doggugo danyobe am,gam soinde ma66e nasdai am nder tosku.
Dan bana so mushiga cikin matsala."

Lips nashi ya cije danjin kalamanta masu daci amma da yake Musaddik irin mazan nan ne 'yan duniya a hankali ya laluba ya kamo hannunta ya ɗaura saman kirjinshi ya ce.

"Fatima ta6a kiji yanda zuciyata ke harbawa duk bugu daya da sunanki yake tafiya ko kinsan ko lumfashi nayi mai ƙarfin da sunanki yake fita, ban ta6a soyayya ba Fatima sai a kanki ke ce kika shayar dani ruwan soyayyar da ban ta6a yiwa wata ba.
Kowadi Fatima? A yidi a viya am jotta a dacci yidugo am na?
Haƙika Fatima yanzu zuciyata ta fara faɗa min kin daina sona."

Hawaye na fita a idonta a hankali ta zame jikinta daga nashi ta janye hannunta ta koma kan wata kujera dake ɗakin ta ɗan lumfasa kafinta juya ta kalle shi, azin kamar irin yana ganin ta nan ta ce.

"Musaddik na kula dakai u will never understand me.
Kada fa ka manta ko waye mahaifina Alhaji Bashir Muhammad Lamido zai iya komai indai har muka gudu babu inda bazai shigaba cikin kasashen nan a
kamomu a wajanshi ba abu bane mai wahala ina tabbatar maka muna guduwa ko tashar Yola bazamu bari ba za'a kamamu..
Humm Musaddik bana so na sakaka a cikin matsala dan haka gara kawai mu hakura da juna.."
"Dakata Fatima"

Cikin tsawa yayi maganar daka kalleshi zaka tabbatar da ranshi ya 6ace yaci gaba da cewa.

"I understand u Fatima au dama kin fara son wannan dan iskan sojan baki faɗa min da wuri ba kika tsaya kina yaudara ta.."
"No Musaddik please listen to me."
"Stop Fatima let me finish because i will not listen to u.
Fatima kina so kice min yanzu kin fara son Faruok ne saboda shi mai arziki ne? nikam talaka ne kuma makaho yanda bai aje komi ba shiyasa zuciyarki ta za6a miki mai arzik..

Da sauri ta nufi wajanshi tasa hannunta ta rufe mashi baki tana faɗin.

"No! Musaddik don't say so please."
"OK naji bazan ƙara faɗar haka ba idan har da gaske kike to kizo mu gudu."
"Bazan iya ba Musaddik
Idan har nayiwa iyayena haka banyi masu adalci ba, sun bani dukkanin wata tarbiya, Musaddik idan nayi haka zan nunawa duniya cewa ni bani da tarbiya..."
"Ya isa haka Fatima na gaji da jim wa'anan kalaman naki masu kama dana yaudara yanzu babu wani abu da zaki sake faɗa min na yarda dake dan haka fita ki barmin daki i don't want to see u again."

Yana kai karshen maganarsa ha fisge hannunta har yana bigewa da kujera ya turata waje ya rufe ƙofa, faɗi take.

"Please Musaddik listen to me, kada kayi min haka na tabbata da sonka zan mutu."

Musaddik baima san tanayi ba, ta dade nan tana kuka kafin ta danyi ƙarfin halin tafiya, tana tafiya tana kuka har takai batasan inda take saka kafaffunta ba.
Wani irin horn kakeji mai kara daka jishi zai tabbatar maka da mamallakin motar yayi fushi, gabaki ɗaya ya danne steering motar.
Cikin fushi ya fito a motar ya nufota yana faɗa.
Ganin Fatima a tsaye tana layi yasashi am batar sunanta da sauri.

"Fatima ina zaki a wannan lokacin?"

Ido ta ɗago tana kallon captain Bilal dake magana, a hankali ta buɗe baki zatayi magana kenan ta fara tari kamar zata mutu take a wajan ta fara aman jini a ruɗe captain Bilal ya dinga kiran sunanta yana faɗin.

"Na shiga uku please Fatima kada ki mutu Fatima!!"

Ina ai har takai ƙasa

Captain Bilal baisan lokacin da yasa hannu ya ɗauke ta cak ba sai cikin mota, direct hospital dake Abuja Read ya nufa da ita.
Da sauri likitocin wajan suka shiga bata taimakon gagawa.
Sai bayan an shiga da itane ya kira Faruok yake faɗa mashi abin da ya faru, a lokacin ne jama'ar gidan suka fahimci Amarya bata gidan.
Basu wani 6ata lokaci ba suka isa asibitin gabaki ɗayansu harda Dad.
Dad ranshi ya 6ace sosai kamar zai mutu direct ɗakin da Fatima ke ƙwance suka nufa suna zuwa cikin hukuncin ubangiji har ta buɗe idonta amma hawaye ne kawai ke fita a idanuwan nata.
Saukar duka kakeji kota ita anayi duk hankalisu ya tashi dan ganin Dad ya rufe Fatima da duka ya koma kamar mahaukaci, dan ranshi yayi matuka wajan 6aci.

Captain Bilal da Faruok dakyar suka iya rike Dad daga dukan Fatima amma fa ta wahala dan dakyar take maida nunfashi.
A hankali suka zaunar da Dad saman kujera suna bashi hakuri jajayen idanunsa ya ɗago ya fara magana ciki fulatanci ya ce.

"Fatima a Holli duniyaru mi fotai mi Volla a Nana,hande to be vi no na shamsiya danyima da mi jabai no soinde semtende ma amma a toski hore mada a semtini am a semtini Dada mada.
Ban ta6a tunani Fatimata zata zama marar jin magana ba, Fatima nasoki fiye da tunanina amma lokaci ɗaya kin fara saka min tsanarki a zuciyata.
To wallahi Allah Fatima ko bayan ba raina yau ta Allah ta kasance kika juyawa Faruok baya kika aure wani bashi ba ban yafe maki ba duniya da lahir.."
"Ya salam Alhaji kada kayi fata baki duk abinda Fatima tayi mana har muce babu yanda zamuyi da ita."

Wani irin kallo Dad ya watsawa Mom dan jin irin maganar da take.
To amma kuma ai tsakanin uwa da da sai Allah.
Murmushi takaici Dad yayi ya ce.

"Shamsiya kin ban mamaki, au dama kina nufi duk iskancin da yariyar nan take dasa hannunki?
Gaskiya ne."
"Haba Alhaji kada kayi min mummunar fahimta wallahi ba haka nake nufi ba."

Faruok ya kula idan yabarsu maganar zatayi nisa shiyasa yayi saurin tararsu.

"Mom Dad dan Allah kuyi hakuri kubar maganar har sai munje gida."
"Naji Faruok amma ka sani wannan yar iskar yarinyar bazata ƙwana a asibitin nan ba dole da ita zamu gida koma wallahi ko tana suma da yardar Allah babu fashi sai an ɗaura auran nan."
"To amma Dad look at condition da take ciki ya kamata a barta nan domin a duba lafiyarta."
"Faruok umarni ne kake ban ko shawara?"

Yanda Dad yayi maganar yasa jikin Faruok yayi sanyi dan ya tabbatar da yau ran mahaifinsu ya 6aci sosai.
Ya ce

"Sorry Dad. "

A hankali Mom ta nufa wajan Fatima tasa hannu ta ɗago kanta amma ko mahaukaci yaga Fatima yasan tana jin jiki.
Cikin sanyin murya Mom ta ce Faruok bazata iya tafiya da kanta ba dole saika ɗauke ta.
A hankali Faruok ya juya ya saci kallon Dad dan yaga ko zaiyi magana kawai yaga ya juya ya fita captain Bilal da ke wajan lamarin ya bashi mamaki sosai hannu Faruok yasa ya ɗauke ta cak suka fita Mom ta bisu cikin sanyin jiki bayan fitar su Faruok yayiwa captain Bilal magana akan ya kawo duk wani abu daya kamata a duba lafiyarta.
Duk Kansu kuwa ya shiga motarsa captain Bilal ya wuce sayo kayan treatment d'in da za'ayi mata, sukuma su Faruok suka wuce da Fatima gida...

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now