NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*NADAMAR DA NAYI*
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS OMAR_)_STORY BY_
*HAUWA M. JABO*_DEDICATED TO_
*BEEBAH LUV*_Page 28_
"Ikram wallahi duk duniya babu macen dana taɓa so sama dake tun ranar dana fara ganinki zuciyata taji duk duniya babu macen data ke so saike, Ikram bansan jinkirin da nayi wajen qin faɗawa Faruok muna soyayya dake zai zama haka ba wallahi dana san hakan zata faru da tun haɗuwarmu dake na faɗa mashi dan Allah kiyi hankuri wallahi banci amanarki ba, babu yanda za'ayi na bijerewa maganar Faruok kiyi hakuri wallahi ina sonki"
Ajiyar zuciya Ikram ta sauke a wayar sannan cikin sanyi murya tace"Don't worry i know u love me, haka Allah ya tsara kasan kana taka Allah na nashi dan haka dani da Fatima duk ɗaya ne kasan Fatima ƴar uwata ce ta jini zan Iya sadaukar da komi nawa a kanta ka sani haka Allah ya kaddara, nagodewa Allah da Allah yasa babu wadda yasan da wannan soyayyar tamu so please promise me u will never tell anyone about soyayyar mu"
Shiru Bilal yayi yana sauraronta har saida ta numfasa kafin yace.
"Nayi maki Ikram please kada ki manta dani a tarihin rayuwarki"
"Kada ka damu ana tare tunda ƴar uwata zaka aura nagode sai anjima"Bata tsaya jiran amsarsa ba kawai ta kashe wayar shi kam ido ya runtse ya gyara kwanciyarshi sosai..
***
Fatima tana shiga toilet kawai sai taga wani abu na bin ƙafarta da sauri ta duba ta gani, jini ne ta gani yana binta take tayi tsalle tace.
"Masha Allah, Allah nagode maka yazo"
Ajiyar zuciya ta sauke kawai tashiga gyara jikinta saida ta gama kafin ta haɗa kayanta dama sauran kayanta har yanzu suna gidan Faruok bata ɗauko ba shi kuma bai aiko mata dasu ba.
A parlour ta sameshi zaune ya maida hankalinshi ga danna waya da alama charting yake, Iya ce ta fito tana cewa."Ai ni wallahi Bashir bai ƙyauta min ba dama ya barki a nan danke kam sai addu'a yarinya kullum waya a kunne tana waya da ɗan iskan yaron nan ai gara a barta ta aureshi ko hankalin kowa zai kwanta"
"Iya kenan dama nasan babu mai son Musaddik sai ke"
"Dan Allah rufa min baki yarinya marar kunya sai kace ba yar fullo ba, wallahi kin dai ji kunya"Dariya Fatima tayi domin kuwa duk abinda yau Iya zatayi mata bata jin komi domin tana cikin farin ciki.
"Ke dakata wai dariyar me kike ne? dazun fa har kika fita kamar anyi maki mutuwa ke tunda kikazo gidan nan baki taɓa min magana cikin jin daɗi ba, ko dai umaru yazo maki da albishir ɗin auran makahonki"
Fuska Fatima ta ɓata tace.
"Ƙyaji dashi dai ni kam na tafi gidanmu"
Duk maganar da suke Faruok na jinsu bai tanka ba saida ta juya zata fita ya tashi ya amshi akwatin hannuta.
"Bawan Allah kaima Allah ya baka mai sonka gaka namiji har na miji ka likewa mace ɗaya wadda bata sanma kanayi ba"
Iya ta faɗa cike da jin haushin Fatima..
Faruok bai tsaya ko ina ba sai gidansu yana zuwa yayi horn mai gadi ya buɗe masu get, a harabar wajan ya hango Hafsat daga nisa tana tsaye da dogowar hijabin daya ganta kai ya girgiza yace
"So kenan"
Kai Fatima ta ɗago tana kallonsa saboda ta ɗauka da ita yake, bayan ya fito ya buɗe bayan motar ya ɗauko akwatin nata Habu driver yayi saurin amsa ya shiga dashi itama fitowa tayi tabi bayansa, zasu wuce Hafsat tayi saurin duƙawa tana faɗin."Sannu da zuwa yaya Faruok"
Ido ya kura mata yana smiling sai yaga Fatima itama ita take kallo cike da mamaki, shu'umin murmushi ya saki yace.
"Lafiya qlau my Hafsat ya kike?"
Kai ta ɗago da sauri tana kallonshi ya wani kashe mata ido ɗaya.
"Lafiya yaya"
Fatima ita dai kasa cewa komi tayi amma abin mamaki yake bata, baki ta taɓe tabi ta bayansa ta wuce shima bayanta yabi, har zata wuce ɗakinta yace da ita
"Amma yana da kyau ki fara zuwa kiba Mom hakuri kafin azo ga Dad ko?"
Ba tayi mashi magana ba kawai ta wuce ɗakin Mom, saida Faruok yasa baki kafin Mom ta hakura haka shima ta ɓangaran Dad.
***After one month
Bayan wata ɗaya Fatima ta cigaba da ganin menstruation ɗinta tsakaninta da Musaddik kam soyayya ba'a cewa komi domin kuwa a kullum soyayyar su ƙara karuwa take.
Faruok ko duk wanda ya gansa yasan akwai abinda ke damunsa duk yabi ya rame ya fige sai kace ba Faruok ɗin da jama'a suka sani ba, lamarinsa tun yana damun jama'a har yanzu takai an saka masa ido, har yau baije ya samu Dad ba akan maganar Hafsa shima Dad bai sake yi masa ita ba, duk wata hanya da Hafsa zatabi dan tashawo kan Faruok tayi amma a banza..
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION**NADAMAR DA NAYI*
YOU ARE READING
NADAMAR DA NAYI
ActionNADAMAR DA NAYI labari ne da yake d'auke da NADAMAR yaudara ,cin amana da dai sauransu. Labari ne a kan wata yarinya da ta fada soyayyar wani makaho iyayenta sukaki amincewa, suka aurar da ita ga dan uwanta amma daga karshe....