*WADAT*
_THREE_✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
💥Shatuuu095@wattpad: Vote, Comment, recommend and follow.
*Where are all the writers of Kainuwa Association....wannan page din Naku ne.... Ku dade Ku nayi mutane na*
........Cigaban Asalinmu
Yan gidanmu na karatu dai dai gwargwado, Yaya diploma kawai yayi saboda Baba bashi da halin da zai ci gaba hakan yasa dole ya hakura ya fada kasuwanci anan kasuwar kwari yana sai da atampopi da lace kuma Allah yasa masa albarka yanxun haka yana da iyalinsa Aunty Na'ima ce matarshi yar nan hotoro ce da yaransu biyu sunan kabuga da zama, Yaya sani ma bai dade da aure ba matarsa Sadiya amma shi yayi karatu har matakin Masters inda yake aiki a nan FCE kuma yana zaune ne a quarters dinsu.
Mama na da kyakkyawar maamala da surakanta in ka gansu ba za kace surukai bane mussaman ma Aunty Naima su kan zo tare duk weekend sun zama tamkar aminai hakan kuma duk aikin Mama ne. Yan gidan su ma nada kyakkyawar maamala da Mama saboda irin zaman da take yi da yarsu hakan na faranta masu ransu dan gaskiyar bahaushe yace Mai da mahaukaci!
Yaya Rabi kam tana gama secondary ta samu mijinta dan kasuwa Baba yace to tunda Allah ya sa shi bai yi karatu iyakar sa sakandire to ita dole ne tayi, shi yasa ya saka ta a Kumbotso tayi NCE yanxun haka tana koyarwa anan first lady ta kuma koma makaranta tana yin degree.
Baba bai yarda ko da yaronsa daya ya zauna ba Sana'a ba don haka kowa da abinda ya iya a gidan mu. Ko Yaya sani dake aiki yana sanaar saro kaya ya saida Na maza ta hannun Yaya, Yaya Rabi ma na yin su cake, meat pie snacks dai in xaa yi aure a bata kwangila har abinci da lemo. Yaya sambo kam da ishaq suna zuwa kasuwa gurin Yaya in ranar weekend ne su bi Baba aiki. Nima kam har jos Baba ya tura ni koyar saka kuma Alhamdulillah na iya, rukayya ma na koyar dinki. Hatta dasu Aunty Naima da Yaya Sadiya sai da Baba yasa suka koyi Sana'a. A takaice 'Yan gidanmu Yan kasuwa ne Wanda Allah Ya rufawa asiri Ya wanzar mana da WADATAR zuci!Tsarin Baba ne duk hutu yake Kai mu Kaugama da jahun don mu ziyarci yan uwa.
Asalin zuwa na boarding school naje hutu ne gurin maman Kaduna a lokacin tana rukon yayan mijinta guda biyu. Ranar da naje xasu je exam nan fggc Zaria to sai Mama tace nima a saya form dani kawai na rubuta. Da ke harka ce da kudi sai aka rubuta dani ina ta murna abuna har hutu na ya qare na koma gida. Baba bai ji dadin exam dita ba don shi Sam baya son baya son boarding school amma dole yayi alkunya.
Ko da jarabawa ta fito duk mun ci amma ni a kazaure aka kafe sunana anan Mama tace kawai tunda bamu samu ba school daya na hakura amma na kyakashe kasa nace ni ina so don akwai wasu yan islamiyar mu da suke boarding kuma suna bamu labarinta hakan yasa na dokanta nima naje. Ala dole aka bar ni naje.
Maman kaduna ta biya min kudin komi kuma ta aiko da kudi a man provisions. Ko da yake har yanxu ma ita ke dauwainiya da karatu na Baba kuma ya man abinda baa rasa ba. Sayayya kam an man bani mancewa ranar lahadi Yaya da Mama suka kaini makaranta ina ta murna na zama uwar kaina a tunanina kam can ba tsangwama ba islamiya bare dukan hadda.
Amma tun a daren farko na fara kuka jina ba Mama ga kadaici da bakunta. Haka dai nayi ta fama har na fara sabawa nayi school mother wadda ke man kitso, wanki da sauran aiki tana kaunata matuka duk inda zata dani take zuwa hakan yasa na fara sabawa da mutane sosai sai dai na Kansan takuna
Sati na biyu aka kawo Amina Bello, dakinmu aka kawota nan kusa da gadona Aunty na ta kawo ta kasancewar ta house captain dinmu. Farkon zuwan Amina sam bamu shiri da ita, ita din yar shagwaba ce ga fada bata da hakuri ko ni kuma ina da sabanin halayenta amma tunda wata rana bata da lafiya na kaita gun Auntyna ta raka ta clinic shi kenan ta hada mu biyu take mana wahala tare to nan ne asalin kawancen mu.
Ko ranar visiting yan gidan su sun zo ranar naga shagwaba amma yan gidansu masu kirki don sun kira Aunty Jidda sun mata alheri sosai duk da dai taki amsar kudi sai ledar kawai ta amsa tayi godiya
Nima can su Mama suka zo da yan gidan mu gaba daya har suka gaisa da Mummy din su Amina ita ta wuce. Nima na kira Aunty Jidda sun gaisa dasu Mama kuma kowa yaji dadi.
YOU ARE READING
WADATA
RandomThe story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk Wanda Yayi hakuri bazai Taba tabewa ba, labarin A'isha da Suleiman masoyan gaske Wanda kaddara ta d...