THIRTY FIVE

2K 283 24
                                    

*WADATA*
_Thirty five_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

Baa fi awa ba sai ga Rukayya rike da hannun wata kyakkyawar yarinya da bata wuce shekara bakwai ba, doguwar riga ce jikin ta white da royal blue sai hula kalar kayan da kuma wani flat peep toe fari tayi kyau sosai, kana kallonta kaga yar masu kudi Haka yar lelen danganta, Kusa dani ta zauna ta gaida ni na amsa amma ina daga kwance nace

"Ruky, yar waye?"

Tace

"Dr Rayyan"

Ban san sa'adda na mike zaune ba ina fadin

"Rukayya me ya kawo su gidan nan?"

Yarinyar ta bani amsa da gurbatacciyar hausar ta

"Ni da Daddy da Hajiya ne, Daddy yace you're I'll, we're here to greet you"

Sai kuma nayi shiru ganin baranbaramar da nayi amma nabi Ruky da harara na san tabbas itace tayi masa kwatancen gidan don na tabbatar wannan sabuwar number din shine, raina ya baci naji ba dadi ni bana son taron mazan nan wallahi sam. Nace da yarinyar

" Ina Daddy din yake?

Tace

" Yana waje"

Nace

" Hajiya fa?"

Tace

"Tana compound"

Nace

" OK yaya sunan ki?"

Tace

"Nana Khadija amma Daddy Sweetheart yake kirana"

Nace

" Good wani class kike?"

Tace

"I'm in nursery two in intercontinental Academy"

Nace nice.

Mun dan yi hira da ita, kafin itama Hajiyar ta shigo. Dattijuwa da bata fi shekaru sittin ba amma jin dadi ya boye tsufan ta, tana kama da yaron ta sosai. Ta duba ni cikin nutsuwa da kamala kana ta dauki yar ta don su tafi. Na tashi da kyar na dauko mata riga da na sayawa Amaturrahman ban kai ga kai musu ba, na bata nace nagode.  Sai da suka tafi Mama ta aiko min da wata leda wai in ji shi. Na amsa na buda, yan alawoyi ne sai card anyi rubutu ciki.
   C'omon you have a lot of attention, it's time you get back on your feet and resume, many awaits your presence and your cute smiles,
          Get well soon
              Rayyan Abubakar.

Nayi dan murmushi kafin na aje Mama ta shigo da wani roba a hannun ta aje tace gashi inji Hajiya nace nagode ba tare da na duba ba. Mama tace shima asibitin ku yake aiki? Nace eh tace ya kyauta nace uhm. Sai da fita kana na buda ashe dambun nama ne ya sha kayan kamshi sai kamshi yake ya kuma daku sosai. Rukayya ce ta shigo tana fadin

" Yaya Mami, ga wayar ki ki kira su kiji yaya suka je gida?"

Nace

"Ke da kika kawo su ke zaki kira su?"

Tace

" Ba zaki gane ba ne, na daga maman ce fa tayi min magana kin ga ai dole nayi masu kwatancen.... Har da abun kirki"

Ta fada tana daukar dambun. Mahuci na kwada mata ta fita da gudu. Wayar na dauka na tura masa sako.

   Assalamu alaikum.
     Da fatan kaje gida lafiya? Jazakhallah khairan, ka gaida Hajiya da kuma Nana. Good night.

Wasa wasa sati guda na bata ban fita sai yau nake shiri na tafi. Ban san wani duty nake ba amma nafi tunanin cewar evening ne. Don haka daya na bar gida na tafi aiki ban dau mota ba don jiki na babu kwari sosai. Na hau adaidaita sahu har asibiti yana sauri wai don haka a gate ya ajje ni. Na fara shiga kenan naji ana min horn ta baya na juya sai naga ashe Dr Rayyan ne yayi alama dana shigo mu karasa amma naki. Kawai sai naga ya fito shima ya faka motar gefe nace

" Ya haka?"

Yace

"Mu tafi tare tunda dai kai nake saidawa ko?"

Nace

" Ba haka nake nufi bane kawai dai bana son ana....."

Sai kuma nayi shiru yace

" Go on ana ganin mu tare ko? Nayi shisshigi cikin lamuran ki da yawa ko ban kai sauran da kuke rike hannu ba."

A raina naji ba dadi dama na aiyana zai ce haka sai nace

"Ba fa wani bane tsohon miji nane...."

Bai ce komai ba amma dai bai yarda ba. Ni kuma nace bana shiga motar sa. 
Sai da muka je har ward kana ya bani wayar shi yace Nana zata kira ki ku gaisa nace to.
  Haka nan sai na tsinci kaina da cin amana na shiga gallery din sa. Hotunan sa na barkatai dana Nana, wasu har da wata mata da nake tunani cewar matar sa. Wasu a kasashen turai suka yi, a iya hotunan zaku tabbatar da soyayyar dake tsakanin su. Na gama kenan ta kira mun jima muna hira kafin muyi sallama tace min Al-furqan zata tafi islamiya nace to tayi karatu da kyau tace to Aunty ina karatu a hadda ina Ahzab nace Masha Allah ki dage da karatu tace to.

A hankali na kwankwasa yace come in na shiga a hankali nace ga wayar ka. Yayi man alama da na aje masa kan tebur sa ban ce masa nayi ficewa ta abun haushi ma kamar wata yar sa zai ta wani bata rai.
Da aka tashi ma na fito wani mutum ya tsaida ni yana tambaya ta ni kuma na bashi amsa. Sai ko gashi ya zo ya wuce dana gama masa kwatancen nayi wucewa ta, zuwa na yana tada mota amma sai da ya fito yazo gaba na yace

"Dole kiyi ta amsa sunan Bazawara tunda kin maida kanki kowa ya tsaida ki"

Raina ya baci nace

" Kowa kam amma banda kowar wake."

Nayi tafiya ta me nayi masa haka kawai yau ya takura ni kamar wadda yake aure ko kuma ya haifa.
Ina fita na samu adaidaita nayi tafiya ta. Duk yadda naso na daure amma ba dama sai da naci kuka abuna na more sosai. Ina zuwa gida Baba yace yana son gani na sai da nayi wanka naje gaba na faduwa sosai. DA sallama na shiga jikina a salube sosai, sai da muka sake gaisawa yace

"Yar uwa ta, na san zaki yi mamaki don duk lokacin da nayi maki wannan kiran kin san ba magana a wasa na ko?. Kinga dai gaba daya dai shekaru ki ashirin da takwas bana kina da aure biyu, kin yi shekaru da ba sai na fada menene aure ba, mijin ki na fari nayi maki zabe, na biyu kin zaba da Kanki, amma duk baa dace ba. To wannan Karon so nake na baki nan da sati ki fito min da wanda ya kwanta maki cikin masoyan ki don na gaji da ganin ku haka ke da yar uwar ki. Ke na baki sati guda kiyi nazari ki zo min a irin lokacin nan da wanda kike so  kin ji ni ko?"

Tamkar anmin Duka Haka naji amma Nace eh yace to tashi kije Allah ya bamu alkhairi nace amin.  Daki na dawo jiki ba dadi wato Baba so yake ya ballo min aiki kenan ni kaf! Cikin su da wa nayi wani sabo da har zaa ce na aura, Mukhtar ko wa? Ni banda gurin aikinsa ma sam ban san komai akan sa ba to sai wa Bashir ko Sulaimam?. Tab! Da aiki a gaba na sosai fa.

Shatuuu ♥️

WADATATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang