TWENTY FOUR.

2.4K 291 33
                                    

*WADATA*
_Twenty four_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

*And yesterday you guys were just praying for A'isha and Suleiman, supporting Sa'adatu but only few remembered poor Shatuuu and prayed for her, Haba mana kullum I'm shouting Ilysm amma a rasa masu cemin Haka...... Weeping*

Da asuba haka ya kinkimeni kamar wata baby zuwa toilet tare muka yi wanka har na tsarki, a daki ma tare muka shirya shi a dole sai na daina jin kunyar sa. Sallah ma tare muka yi. Muka yi azkar da tilawar alqur'an. Bakwai muka barci, da kirjinsa yayi min pillow wani barci mai dadi ya dauke mu. Sai takwas da rabi na tashi har na tashi a jikinsa na sa kafata daya zan sakko a gadon ya janyo ni na fada jikinsa.
Bamu farka ba sai goma saura. Wanka ya shiga ni kuma na gyara dakin na ciro masa kaya a wardrobe dinsa. Sauran dakuna ma na gyara, wanka na shiga sai a lokacin nake jin ba dadi a raina matar sa wata Kil tana can tana jiranshi amma yana nan har sha daya dole duk dauke kanta taji ba dadi.
Wata doguwar riga na saka ta material mai kyau dinkin fitted gown ni kaina nasan nayi kyau dan light make up nayi sai na feshe jikina da turare. Kofata aka turo da murmushi ya shigo yana fadin

"Wannan kyau haka Eesher"

na murmushi nayi nace

"Na kai ka?"

Hancina yaja yace to zage ni. Kiss yayi min a goshin na yace

"Ga yara nan suna jiran ki"

Nace to. Hannu na ya kama har parlour muka zauna tare dashi a two seater yana rike da hannuna yana wasa da zoben hannuna suka shigo amma yaki saki na watakil sun saba da hakan. Dukansu ne yaran su shida abinsu. Kowa ya gaida shi da Daddy good morning tare da yin musabaha shima kuma yana amsa masu da cewa morning angels nima sun gaida ni. Babbar ce mai kwando a hannu ta aje a gefe na Lura Se bata rai take. Shi ya fara ce min

"My Eesher ga Mufida nan babbar ba zata wuce saar Ruky ba yace tana nan ABU Zaria she's like me she's reading law level 3"

Nace

"Masha Allah!"

Yace

"Ga kuma Abdurrahman muna kiran shi Abdul yana nan KASU level 1yana BA english  ga Fati na Zahra tana SS2 Salamatu na tana Jss 3 Abbas na Jss 1 sai kuma takwarar Mummy Sa'adatu Islam tana primary 4."

Ya juya garesu, yace

"Ga Eesher na she's your new mum, she's nice itama mamar Ku ce, ko My Eesher?"

Na dan rausaya masa ido na. Mufida ce tace

"Daddy ga break nan inji Mummy zamu sauka"

Zahra tace

"Daddy, we've been waiting  for you muyi breakfast amma kaki saukowa Mummy ma taki fitowa"

Yace

"Sorry sweetheart, barci muke ne I was late, yace am mufida jeki bedroom dina kan bedside drawer zaki ga key you bring it"

Tace to. Yace the rest can go. Tashi suka yi suka tafi, a raina ina mamakin su.
Kitchen yasa ta bude ta kawo plates da cups duk da tana ta buntsire buntsire yace tayi serving nace A'a barshi jeki kawai bata ce komi ba ta fice abinta. Ni nayi mana serving chips ne sai kwai da tea. Bayan mun yi break yace bara ya sauka su gaisa da First lady kamar yadda yake kiran Sa'adatu nace jira ni bara muje yace to. Mayafi na dauko muka sauka shi kanshi benen mai kyau ne sai wata kofa a baki sai siririyar corridor daga gefe wata kofa ce yace ga BQ dinmu nace to sai kuma babbar kofa tana kallon mu. Nan muka shiga, yaran nata kallo manyan kuma na chatting a wayoyin su, sai Abdul na danne danne a system dinsa. Parlour din kansa ya hadu sosai ya dan jingina da kujera yace

WADATAWhere stories live. Discover now