*WADATA*
_Twelve_✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
💥Shatuuu095@wattpad
My wattpad friends! Hi
Bedroom dina na koma sai sha biyu da rabi nayi sallah Zuhr sannan na fito na hade kwanukan da suka Bari na kai kitchen. Girki na dora shinkafa ce don cikin su sai shinkafar kam da miya nayi na yanka lettuce da kwai sai cucumber tumatir da albasa. Na wanke nashi na zuba salad cream. Na sa a tray na kai fridge bayan nayi foiling dinshi. Zuwa biyu har na kammala, ina kallonsu suka yi alwala suka yi sallah amma ba mai shirin gyara gurin, ruwa na hado da hypo nazo inda suka ci abincin na tsine macaroni din don kar nasa tsintsiya suce wulakanci. Moping wurin nayi nayi tafiya ta, wanka nayi nayi kwalliya ta. Waya na kira Sulaiman cikin shagwaba nace"Excellency yau kam na sallamawa yan matan makaranta kai... Irin ka mance dani ko?"
Yace
"Waye ni? Kina raina yan matana ina ma fa kan hanya"
nace
"To Allah ya kawo ka lafiya"
yace amin.
Incence burner na dauko na jona na hade gidan da turare na har parlour nasan dai xasu ce na masu hayaki amma ni gaskiya bani bari mijina yaji wari a gidana.
Knocking naji na tafi na bude zai rungumeni na kauce masa don yaga su waye a parlour din. Jakar shi na amsa na kauce ina fadin" Sannu da Zuwa"
Yace
" Yauwa Yan matana"
falon ya karasa yana cewa
"A'a Kari sannunku da zuwa zatona ai kuna gidan alhaji ashe nan zaku sauka."
Da fullanci suka amsa masa ni kuwa nayi ciki abina. Ya kai kusan minti ashirin kana ya shigo. Jikina ya fado yana fadin
"Yan matana na gaji sosai fa yau dinnan"
nace "Ko? "
Yace
" Bakiga aikin da nayi ba yau"
nace
"Na kallon mata ko? Shi yasa ka mance ni ko"
Kaina ya dungure yana dariya yace
"Ke yarinyar nan kar ki min sharri.,... Kawo min abinci dai naci tukun"
Mikewa nayi na nufi kitchen na hado komai sannan na aje gabanshi bayan na bawa bakin abincinsu.
Sai da na zuba mana nace bismillah ya taso muka fara ci ba wani da yawa naci ba sai dai yawan juya abincin da nake yi. Spoon din hannunsa yasa ya datse hannu na na dago muka hada ido hakan ya tuna min da farkon zuwan shi zance gurina. Da tuhuma yace" me ke damunki yan matana?"
Kaina na girgiza hade da yin yake nace
"Nothing"
Kai Ya girgiza yace
"How I wish... Nasan cewar zuwan su Karimatu bai yi maki dadi ba amma don Allah kiyi hakuri ki cire damuwa a ranki is not good for your health, Ni kaina ban san xasu yada zango gidan nan ba zatona gidan Alhaji zasu sauka ashe nan ne. Don Allah na roke ki kiyi hakuri ki shanye duk abinda xasu maki don Allah zaki yi don biyayyar aure.
Na san ba wani jimawa xasu yi ba don sayayyar kayan auren yar Wasila suka zo"Tunda ya Fara magana nake kallonshi Har Ya gama Nace
"Duk ni na fada maka haka? "
Yace
VOUS LISEZ
WADATA
AléatoireThe story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk Wanda Yayi hakuri bazai Taba tabewa ba, labarin A'isha da Suleiman masoyan gaske Wanda kaddara ta d...