THIRTY TWO

2K 288 11
                                    

*WADATA*
_Thirty two_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

*Counting only 1140 words I'm really sorry banda caji amma Inshaaa Allah dinner will be served idan nayi caji..... Lots of love habibties 💕*

Ranar sai ga Aunty Maijidda tazo min gaisuwa tana ta complain na haihu ban fada mata ba shi yasa taki zuwa wannan ma don mutuwa ce shi yasa tazo min. Da daddare sai ga Sulaiman da su Amatullahi sun zo min gaisuwa har da Kanwarsu yazo. Tayi wayo tubaraka Allah. Bata fi wata tara ba amma dumur da ita kamar Maman ta, mun jima dasu suna ta hira. Yaso na fito amma naki. Da zasu tafi na dauko mata wani teddy da Guitar cikin kayan Muhammad na bawa Amaturrahim nace su gaida Auntyn su.

Rayuwa ta tafi, nayi arbain din Muhammad. Zuwa yanzu na fara hakura dashi sai in nazo kwanciya ne, ko kuma in naga kayan shi amma kuma na kasa bayarwa gani nake kamar in na bayar na cire shi a rayuwata kenan.
Bayan na idar da sallar isha ina nan zaune kan doguwar kujera da ta zama gurin zama na. Ba kasafai nake fita ba in na bar daki to aiki gare ni a tsakar gida wanda baya wuce girki, tunda yanzu wanke wanke da shara duk ana yi musu, sai girki kawai.
Yaya ne ya shigo da sallama na amsa masa, na tashi don kiran Mama don yawanci in kaga ya shigo to wani muhimmin zance zasu yi da Mama.  Yace

"Dawo ba gurin Mama nazo ba gunki nazo"

Dawowa nayi Ina fadin

"To Yaya"

Ya zauna tare fadin

"Shiga dauko min credentials dinki"

nace to. Daki naje na dauko masa, ya dudduba kana yace

"Dama North West University ke daukar Non academic staff, bansan ko zasu Baki clinic in charge dinsu ba, to akwai wani aboki na a screening committee shine naga wannan zaman naki  ya isa haka gara ki nemi aiki wata kila hakan yasa ki ware"
Wani sanyi naji cikin raina da Murmushi nace

"To Yaya nagode"

yace

"babu komai, zan tafi dasu zan yi photocopy ina ji next week zaa fara interview din"

nace to. Yan gidan mu kowa yaji dadin wannan abu da Yaya yayi a raina nace tun kafin aikin ya samu ?
  Bayan sati kuwa naje interview sun yi cracking dinmu sosai kuma insha Allah ina da hope cewar zan samu aikin nan. Su Umma an dage da addu'a amma da result ya fito wai ban samu ba, ban ji dadi ba ko kadan amma Allah shi ke shirya komai ga bawan sa na kuma muka lamura na yayi min zabi na alkhairi. Duk da haka Yaya bai hakura ba, sabon injin saka ya siyo min da kayan yi yace ina yi nan da sati na hada dari na bashi ya kai sabon shagon su da suke so su bude na kayan Baby nan cikin Kwari yana so ya barwa Yaya Sambo yana jira tunda anyi karatu aiki bai samu ba in yaso shi da ishaq suna zama a nashi kafin shima ya tafi service, Rukayya kam na can gidan shi tana koyan dinki gurin Aunty Naima. Ranar kam Yaya ya sha albarka a gidan nan ya cika dan fari abun koyi ga kowa.
Washe gari na fara saka, ina yi ina gwadawa Maama don itama ta koya dan zaman candy din nan tana yi itama. Cikin sati ko na hada na bashi masu zanin goyo dubu biyar marasa abun goyo dubu biyu da dari biyar. Nayi ta addua Allah ya sawa abun albarka, bayan sati biyu kayan shi suka iso ya bude sabon shagon sa wanda Yaya Sambo ke jira, bai dade ba ko Mama ta aiko yaje da CV dinsa Alhaji zai sama masa aiki, don haka sai Ishaq ya zama mai jiran shagon. Kaya kam Alhamdulillah suna tafiya yadda ake so nima kuma a gida ina ciniki.

Ba jimawa Yaya yayi min cuku cuku sai gani ina aiki a asibitin Murtala a tsarin raina bana son aikin asibiti amma ya na iya. Tashin farko suka kaini Paediatric ward gurin Yaran kasancewar lokacin Ina gidan Bashir nayi post basic Paediatric nursing hakan yasa na wuce can. Asibiti akwai aiki ban yi mamaki ba shi yasa suke da kwarewa. Bakwai nake zuwa biyu na tashi, a mota ta nake zuwa kullum na dawo bayan Yaya yayo min takardu da driving license kuma an barni a permanent Morning.

     

                           SULEIMAN

Yau kam insha Allah Yobe yayi shirin tafiya, akwai batutuwa da dama da yake son tattaunawa da Nasir gashi dama tun tafiyar su ko sau daya bai je yaga inda yake ba. Kafin asuba yayi wanka yana dawowa a masallaci ya tafi, ai kam ya sha tafiya bai isa ba sai wajen sha biyu, cikin garin Patiskum. Da tambaya ya gane gidan Nasir a cikin staff quarters jerin gidajen malamai masu matsayin Associate Professor.
Bashi ba hatta Sauda tayi mamakin ganin sa sun kuma yi murna ba yar kadan ba, yara ma nata tambayar su Amatullahi. Cikin kankanin lokaci Sauda ta cika masa gaban sa da abinci tana mitar ya bar su Amatullahi a gida yace ke da zasu zo hutu har sai sun ishe ki.
Sai da suka yi azahar kana ya fara budewa Nasir cikin sa yace

"Aboki, ka ko san Aisha ta baro gidan ta?"

Yace

" Wacce?"

yace

"Wace Aisha nake da ita banda Maminsu Amatullahi"

Yace

" Kai bari don Allah"

Yace

" Wallahi kimanin wata bakwai kenan, ta fito da yaron ta amma yaron ya rasu, I think wata uku kenan"

Nasir yace

"Kai amma ba dadi Allah yaji kanshi yasa mai ceton iyayen sa ne. Kuma Aboki ba labari ai da mun zo mata"

Yace

" Nima very late nake jin labarin da fari dai baya da lafiya bakin wan ta nake ji rasuwar yaron kuma Maijidda ke fada min wai wannan yayar Baban ta da ta zauna wurin ta take fada mata........ Amma ni aboki duk ba wannan ba so nake na maida mata ta dakinta"

Nasir yace

"Ta yaya kenan? Bayan kasan abinda ya faru a baya kuma har yanzu zai iya faruwa"

Sulaiman yace

"Aboki yanzu fa Inna ta fara saukowa kana sane da abinda ya faru ranar suna ko?"

Nasir yace

"Eh bana mantawa ko amma ita Aishan zata yarda ta koma"

Yace

" Aboki shawarar da nake so ka bani kenan, ko da abubuwan suka faru taki bari fa na ganta rabo na da ita tun ranar daurin auren ta!"

Nasir yace

"Haba Man, kar ka sare kai ka zauna da ita matsayin mata zaka fini sanin dubarar da zaka yi har ta sake amincewa da kai...."

Sun jima suna hira kafin ya tafi masaukin sa, washegari ya dawo nan ma dai zance daya ne suka yi ta tattaunawa sai da yayi sallar azahar kana ya tafi gida da quduri babba a ransa.

Yours truly

Shatuuu ♥️

WADATAWhere stories live. Discover now