TWENTY TWO

2.3K 276 14
                                    


✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

@aishaimamshehu and all my wattpad Buddies, I guess without you many things will not be possible, so far I appreciate your votes, comments and prayers.... Ilysm

Dawowa nayi Aunty Lami na tambaya me ya faru? Saddiqa ke mata tsari ta juyo tace

"Me yasa baki fasa bakin ta don ubanta? Wannan matar ta cika yar iska irin su fa ke kashe kishiya saboda kishi"

Saddiqa tace

"Allah Aunty ita ma da ita, idan ni ce mace tazo gun aiki na taci min mutunci wallahi da sai na fasa bakin ta na mata jini da majina in yaso next time ta san limit dinta"

Kai Aunty Lami ta girgiza tace

"Gara da bata kula ta ba, A'isha kiyi hakuri Haka rayuwar take"

Nan dai akai ta maida zance, Tayi ta bamu hakuri kyace ita ce Dr Ahmad din, Saddiqa kam na lura haushi na ma take ji don cewar ta me yasa bazan daki yar iska ba nace

"Saddiqa ba amfani hakan"

Tace

" To aiko in baki koyi fada ba duk inda kika je haka zaki yi ta shan wuya."

Har muka tashi raina a cushe yake ban ma san ta inda zan fara ba. Tasha naje na hau mota, ina isa gida kam na wuce dakina.
Kuka na fara sosai ban san me ke damuna ba sam sam ba zan danganta hakan da abinda Laila tayi ba sai dai ina tuhumar rayuwa da yin wulli dani musamman Sulaiman gani nake duk Laifunshi ne, Tun ganina dashi zuciyata bata huta ba, na aure shi ya sake ni na rabu da yara na ya saka ni cikin zawarci da a dalili n haka ba wulakancin da bana gani. Nayi kuka har na gode Allah na, bandaki na shiga na saki ruwan sanyi a kaina ina maimaito kalaman Laila tabbas sakon ta ya isa ya daki zuciya ta, tabbas a rayuwa ta ina jurar komai banda a zagar min iyaye kuma ban san me nayi ba duk inda naje sai an zage ni wata kila zancen Saddiqa gaskiya ne da tace in ban koyi fada ba to fa ban daina ganin wulakanci ba.
Sai da ruwan ya ratsa ni sosai kana na fito na sunkuya nan bakin kofa na sha kuka wata kila da Allah ya halliceni cikin masu fada da na kwaci kaina yau amma ban iya ba to ya zanyi? Cikin dan lokaci ko sai ga zazzabi ya rufe ni a haka Mama tazo ta iske ni tace

"Lafiyarki yau dinnan kuwa?"

Nace

"Lafiyata kalau Mama zazzabi ne kawai."

Ta dan kalle ni na wasu dakiku kafin tace

"To ki fito wai Dr Ahmad yazo"

Nace

"Mama kice masa yaje ba zan fito ba"

Tace

"A'a ba zaayi Haka ba"

Da kuka nace

"Don Allah Mama kiyi hakuri Bazan iya zuwa ba"

Kalloma ta tsaya yi kafin tace

"Aisha akwai abinda kike boye min?"

nace

"Ba komai Mama"

tace to.

Ranar haka na kwana shi yasa kafin safiya da kyar nake bude idona saboda kumburi, bansan lokacinda zan daina kuka ba, wanka kawai nayi na shafa mai na zura uniform gani nake da ace musulunci ya amince maka da ka kashe mutum guda to yau da na kashe kaina ni kam saboda yadda zuciyata ke tafarfasa, Zan fito muka yi cikibis da Mama kallo ta bini dashi nayi saurin dukar da Kaina kasa. Hannuna ta kama taja ni har dakinta tace

WADATATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang