FIFTEEN

2.7K 448 47
                                    


*WADATA*
_Fifteen_

✍️SHATUUU ♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

_Where are my cousins, Oum Zahra, Oum Lubna and Oum Annur... You guys are amazing, your support always keep me going.... Thank you lovelies_

Sai takwas muka isa, can gidan Inna muka sauka lokacin ana ta sallar isha dama mun yi magriba a gidan din mun san a hanya zata same mu. Shi kam bai ma shigo ba nice dai na shiga ciki. Tana sallah a tsakar gida hasken wata ya haska ta. Famfo naje na dauro alwala nazo kusa da ita kan tabarma na tada sallah ta gami da shafa'i da wuturi. Na idar tana ta addua don hakan ba damar mu gaisa har Sulaiman ya shigo yaja kujera ya zauna ta idar ya gaida ta nima na gaida ta ba wani sosai ta amsa ba. Na kunto Amatullahi dake ta barci a baya na na mika mata ita. Sai naga ta amshe ta tana murmushi tana fadin

"Tubarakhallah, Masha Allah!"

Sauran kuma ban gane mai take cewa ba.
Sun jima suna hira ta kawo mana burabusko da miyar taushe muka ci. Sai goma da rabi muka tafi gidan mu. Daki daya muka gyara din ba zama muka zo yi ba.
Da safe ma ta aiko mana abin da zamu karya ni kam dai ina ta mamaki amma don kar Sulaiman yaji ba dadi kamar ina zargin mahaifiya shi sai kawai naci.
Ranar da naje gidan Inna naga wata budurwa haka dai bata fi saa ta ba itama da ganinta kaga bafulatana sak. Kuma ta dan fi su gogewa zato na ita baa nan garin take ba. Ko da na mata magana ba wani sosai ta amsa ba sai dai ta amshi Amatullahi tana ta mata wasa. Ko da Sulaiman ya shigo sai naga tana ta faman murmushi Inna ke ta masa bayani da fullanci ban dai san me take cewa ba.
Sai da muka koma gida ne yake ce min

"Kiji Inna da wani zance fisabilillahi wai gobe mu tafi da yarinyar nan wai yar yar ta ce tazo hutu daga Hong yarinyar sam bata da kunya"

nace

"To yaya zaka yi? Hakuri zaka yi ai"

yace

"Ba zaki gane bane"

Ilai ko da zamu tafi tare da ita muka tafi da zamu shiga mota ta amshi Amatullahi a hannu na muna gaba ni da Sulaiman ita tana baya. Har dasu Wasila ayi mata rakiya ana tayi mata rada. A hanya kam Sulaiman sai wani ja na da hira yake abu kadan ya shafi wani bari na jikina ni kam duk bana so don sai Rahama taga kamar wulakanci muke mata.
Ko da muka je gida ta hakimce a falo ni daya nayi gyara na na turare ko ina da kamshi. Kitchen na shiga na Dora girki sannan na ciro frozed Samoasa da spring rolls dake freezer na soya na hada pine apple smoothie. Wanka nayi na shirya cikin wata yar doguwar riga marar nauhi. Sulaiman ma jallabiya ce mai gajeran hannu yasa. Na kawo mana abinci amsar Amatullahi nayi nayi mata wanka na kada mata madara tasha. Diaper kawai na saka mata da yar vest na nade ta da powder ta Johnson baby, nayi mata addua kana na fito. Kusa da miji na na zauna muna yar hirar da muka saba sai dai yau na kasa sakewa saboda bakuwar da muke da ita, can dai naga ya kamata ace ta bamu wuri don haka nace

"Rahama ga daki can in zaki kwanta"

Tace

"Karki damu bana jin barci"

nace to. Can Sulaiman ya jawo ni yana fadin

"Yan matana I'm sleepy, muje mu kwanta"

nace bana jin barci yace to. A kirji na ya dora kansa kamar wani yaro yana fadin

" In kin gama ki dauke ni mu tafi."

Ganin da gaske yake nace

" To mu tafi."

Sam ni na mance da ita ma sai da na jiyo muryar ta tana cewa

" To a ina ni zan kwanta ba na iya kwanciya ni daya fa? "

WADATAOnde histórias criam vida. Descubra agora