EIGHT

3.2K 336 12
                                    

*WADATA*
    _Eight_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad: Follow, Vote, Comment and Recommend..... Ilysm

Nasan kowa so yake yaji Meye asalin Suleiman, ok here we go!

Sulaiman Lamido Kamar yadda sunanshi yake Dan asalin garin yan leman ne ta jihar jigawa. Mahaifinsa Mallam Muhammad cikakken bafulatani ne, kamar yadda aka san yan garin dama haka suke bafulatanai da suka suna a canji sede shi yayi karatu har matakin NCE inda ya koyar a gurare da Dama ciki da wajen Jigawa . Ya hadu da wata mata itama bafulatana ce yar nan garin tasu ce itama ita ta nuna tana sonshi shima dai har ya nuna yana sonta to daga nan ne fa zance yaje gurin manya har ya aure ta. Bayan sun yi aure ne hali ya fara bayyana sumayya irin masifaffun matan nan ne amma shi Muhammad sanyan hali ke gare shi to hakan tasa suka zauna lafiya
Tayi haihuwar fari da ya mace aka saka mata suna Wasila bayan shekara biyu ta kuma haihuwa aka saka ma yarinyar Karimatu. Lokacin da suka isa makaranta mallam yasa su a wata primary daga nan ne ta sake haihuwar Suleiman Se Fadimatu sai kuma Zinatu  auta Ahmad.
Kamar yadda ada ba wani maida hankali aka yi da mace tayi karatu
ba, to suma su Wasila suna kammala primary kakansu yasa aka cire su daga makaranta ba don ran mallam yaso ba sai a masu haka har kan Karimatu. Daga nan ne aka masa transfer zuwa Dutse anan ne ya samu damar sa Fadimatu, Zinatu da kuma Sulaiman makarantar da yake so. Ita kam sumayya irin matan nan ne masu bala'in son yara takan iya batawa da kowa saboda yaranta. Da mace daya take Hulda a unguwar su.
  Sunyi zaman Dutse har mallam yayi retire lokacin Fadimatu ta yi candy shi kuma Sulaiman na ss2. Haka ya bar Sulaiman anan ya nema masa wata boarding yake yi. Ba jimawa ko ya ya rasu ba ga iyalinsa ba har mutan gari sun ji mutuwar sa
Haka dai rayuwar tasu ta mika. Fadimatu kam an yi saa an bar ta tayi karatu ganin yadda sauran yan uwanta ke shan wahala a gidan mazajen nasu duk kan rashin karatu. Amma ita Zinatu sam taki abin dole aka hakura aka kyale ta Sulaiman ma ya samu tallafi a gurin dangi ya tafi karatu nan jamiar bayero ta kano yana karatun english education. Allah kuma yayi masa baiwa ta karatu don haka yana kammalawa ya samu aiki anan buk sun dau nauhin sa aka tura shi can Winchester yayi Masters. Bayan ya dawo da shekara biyu ya kara komawa PhD inda ya zama Dr. Na karatu. Sulaiman mutum ne mai son taimako don haka duk abinda ya samu sai ya rabawa mabukata. Ya kuma kama Sana'a yana yi irinsu kiwo da noma sai kuma ya gina shaguna ya bada haya.
Sulaiman mutum ne simple kowa alheri yake fada akansa shi yasa yan mata ke tsananin sonshi a makaranta har ma a garinsu a bangaren aiki ko kuwa so yake ya aura masa yarsa. Gashi kam mai tsananin biyayya ga mahaifiyar sa.
    Sai dai fa mahaifiyar sa sam bata son auren da zai yi sai don ita bata son bacin ran yayanta sai ta kyale shi. Amma su Wasila nata zuga ta ta share su. Don sun fiso ya auri wata yar makwafta nsu tunda bakinsu daya.

Ranar alhamis ya kaini gida na yini na kuma yi musu sallama wai zai je Ibadan wani aiki zai kaini can yan leman nayi sati biyu in ya dawo sai ya biyo mu tafi nace to. Tun daga soro na shiga a guje nako yi saa Mama ce a waje da gudu na tafi naje na rungume ta. Fadi take cika ni kafin ki balla ni nace Kai Mama. Hayaniyar ce ta fito da Umma da Baba. Kowa yayi murnar ganina naje na rungume Umma tace sannunki da zuwa, Baba ma baki ya kasa rufawa yaga yar uwa. Shi ya fara cewa ina mijin naki? Nace yana kofar gida Umma tace kika bar shi a waje? Dariya nayi kawai. Baba ya fita suka shigo tare dashi. Sai da gaishe dasu Mama suka shiga dakin Baba nima na tafi dakin Mama har da Umma sai da zai tafi ne Baba ya leko yake ce min yar uwata je ki zai tafi nace to. Har gurin matarsa na raka shi yana rike da hannuna yace wato kinga Mama har kin mance ni ko? Nace ni na isa? Kawai dai ina kawaici ne.....sai yaushe ne zaka zo mu tafi? Yace mu tafi ma yanzu nace to. Yace ki zama ready kafin 8 nace insha Allah nace zan iya zuwa gidan Yaya Rabi? Yace aa nace to. Sai da ya tafi ina daga masa hannu har ya kule.
Gida na dawo muna ta hira dasu Mama abinmu kowa na yaba kyan da nayi. Dama na zo da T-shirt dita da zani don haka na canja na taimakawa su Mama mun yi aiki sai nake jina wani Iri dani. Sai biyu yara suka dawo kowa nata murna da ganina amma duk nace babu ruwa na dasu tunda babu Wanda yaje gidana cikinsu. Sai suka ce dani su Umma suka hana nace don Allah Umma ki bar su su zo tace aa ke dai tunda kina zaune lafiya ai Alhamdulillah wata rana sa je. Nace to Allah ya kaimu tace amin. Yaya sambo ya dawo har wani qwambo yake min wai kayan sa suna dakin Mama. Tunda aka yi magriba ya uxxura min wai nazo na tafi. Mama tace gidanka ne? Yace aa kin dai san yaran nan basu hankali ko? Dariya kawai nayi. Wanka na shiga nayi a bandaki amma duk sai nake wani iri don haka a gagauce nayi wankan na fito.
Cikin material dina na shirya sosai doguwar riga dinkin bubu. Sai sannan na tuna da alawoyi da turaren da na daukowa maman Shahid. Rukayya na bawa nace ta Kai mata. Sai da aka yi isha yazo dama ni a shirye nake ko tuwa ma ban ci ba. Gidan Yaya rabi ya biya damu. Taji dadin ganina sosai haka ma yaranta. Sai da muka shiga daki ne nake ce mata Yaya rabi wai garinsu zai kaini kuma ni ban san me zan Kai matsayin tsaraba ba tace kar ki damu yaushe ne tafiyar? Nace Saturday tace ba case zuwa gobe zaki jini nace Allah ya kaimu. Tace ko ciki gare kine? Nace ciki kuma ni lafiya nake tace na ganki ne kinyi sosai nace haka kowa ma yake fada tace to ke dai ki dage da biyayya Allah ya kashe miji ya baki. Dariya muka yi tare tace inda matsala sai ki kira ni nace to. Yaya Ismail ne ya kwala mata kira sai muka fito suna ta hirar su da Sulaiman yana ce masa ai mallam sulaiman ka bar kawo ta gidan nan ana saka ta a daki don ina gaya maka yadda aka shanye ni din nan ko kofar gida bana iya fita sai tace to kaima haka xaa kitsa ma taka tayi. Tace to sai me don ta daina zuwa? Kuma dai kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake. Dariya muke gaba daya haka Yaya Ismail yake da ban dariya. Shi ya rako mu har mota ina ta cewa kun hana su Amira zuwa yace aa yallabai ne ya hana zuwa kar su zo su katse masa hanzara dariya suka yi su biyun sulaiman yace haka ne kam zancenka yana bisa turba. Sai da muka shiga mota ne ya leko yace dani zamu zo har ni ma mu yini nace to sai kunzo. Dubu daya ya zuro min nace don Allah Yaya Ismail ka barta Kai baka gajiya ne? Yace babu komi sai dai ko in tayi nace aa jazakha Allah khairan yace amin. Sai da ya tafi nake cewa Yaya Ismail kenan Sulaiman yace yana da kirki he's so simple nace haka yake amma fa yazo yaga kirki anan na fada ina shafa kumatunsa yace da gaske? Nace sosai ni kam ina jin har nafi autar mata dace da miji. Ina sonka sosai Excellency. Da alamar yaji dadin magana ta sosai don murmushi yake yi.
   Ko da muka koma gida tare muka yi girki yace mu dafa Macaroni kawai tunda akwai guntun miya nace to. Tare muke komi yanzu ni da shi har wanka ma tukun muka kwanta barci abinmu. Sulaiman akwai hakuri bashi da takura wajen auratayya. Ina jinshi yana shafe mu da addua har barci ya kwashe mu.
Da safe tun wuri na tashi na fara aiyuka na. Na hada masa breakfast koko ne da kosai na yi dama haka nake duk jumaa girkina na gargajiya nake don babanta ranar da sauran ranaku.
Kafin ya fito har wanka nayi na caba adona dakinsa na nufa na same shi yana shafa mai, amsa nayi na qarasa shafa masa. Da kaina na dauko masa kaya. Shadda ce fara da aikin bakin zare ya zura masa ita. Sai da ya gama shiryawa ina kallonsa na bata rai. Ya juyo yace ya kika bata rai ko ban yi kyau bane? Nace ni dai sai ka cire kayan nan gaskiya in ka dawo gida kasa ni daya na kalla yace oh God nima fa ba wadda zan kula nace aa da kasan yadda kayi kyau da baka  ce xaka fita haka yace ni ne ma ke gurin kyau nace ka zage ni kawai. Wardrobe din na nufa naje na dauko masa wani sky blue yadi, na shagwabe nace gashi taho na canza kamo ni yayi ya rungume ni gami da kissing lips dina yace I like the way kike kishina.
Bawan Allah haka ya yarda aka canja kayan amma me? Kamar qara kyau yayi nace gaskiya ni gara wancan ma da wannan kaga yadda kayi yace oh yan matana I'm almost late nayi maki alqawari ba wadda zan kula nace to, tsayinsa ya rage na sake masa brushing gashinsa. Ina ta turo baki ni ala dole kishi.
Tare muka ci abinci yana ta yaba girki duk ma dai ya bari kosan yayi sanyi amma haka muka ci. Na daukar masa jakarsa har kofar gida na raka shi, sai da ya qule kana na dawo gida. Karasa abinda ban yi ba nayi. Tukun na kwanta barci. Can cikin barcina naji ana knocking na farka na zura hijabi na. Sai da dauraye fuskata kana na nufi kofar ina fadin waye? Rukayya ce aka bani amsa. Da azama na bude kofa ashe Rukayya ta ce. Rungume ta nayi nace Ruky ashe kece tace Yaya Mami nace shigo mana. Taya ta nayi da daukar kayan ta muka shiga parlour ta zauna, ruwa na dauko mata da lemo nace ke kadai tace ni kadai dawowa ta kenan daga makaranta. Mama ta bani kayan nan na kawo maki nace na ko gode... Ki sha ruwan mana na tsiyaya mata ta sha na bude kayan su klin ne dasu ashana da sabulu da dai sauran kayan tsaraba. Na dauka na kai daki,na dawo nace xaki ci abinci? Tace na koshi ko sai dai an jima...amma me kika yi? Nace koko da kosai ne tace A'a nace to me zaki ci tace ba komi. Remote ta dauko tana kame-kame na channel muna hira jefi jefi nace sai yaushe ne zaki gama jsce din? Tace sai upper Monday nace zaki zo min hutu ko? Tace Baba ba zai bari ba nace haka ne. Knocking naji nace ruky jeki bude tace to.
Kallo daya na masa naga zallar kamar sa da Sulaiman, hijabi na yafa ina washe baki fadi nake Ahmad kai ne da wuri haka? Yace wallahi ko Aunty nace sannu da zuwa, jakarsa ya aje suka zauna shi da rukayya ina cewa gashi ban tanadar maka komi ba. Mikewa nayi najena dauko masa tea flask da basket din kayan tea da mug nace ga wannan. Kwai naje kitchen na soyo masa na kawo masa suna ta hira shi da Ruky nace sannu da zuwa ka sha hanya yace ai sammako nayi tun biki nake so nazo na ganki amma Oga ya hana ni zuwa wai na jira nayi karatu nace Allah sarki ai dama karatu sai da hakuri yace da ina ogan yake nace yaje aiki yace OK. Suna ta hirar su da Rukayya na tashi na shiga kitchen tunda gidan da baki yau bara na dafa shinkafa kawai na dora shinkafar, na ebo kayan miya na gyara nayi blending din su. Na dora miya, kayan vegetable na dauko na hadin couslow na gyara ina hangen su ruky ana ta hira sam ina jin sun mance dani ma. Sai da na kammala gyarawa ne, Ahmad ya shigo yace Aunty da kanki haka ai da kin kawo na taya ki nace kai dai kaje kayo sallah. Ruky ta taso tazo ta amshi gyaran kayan ta yanka su. Ni kuma na sauke miya da shinkafar na zuba a warmer na kai dining table. Na dawo na debi plates da spoons da tumblers duk na kai, sai da ta gama nasa ta ta juye su a tray tasa foil paper ta rufe. Kaza na dauko na hada ta na kai cikin oven ruky tace oven din yayi kyau nace sosai ma. Duk aikin maman Kaduna tace rannan ma ai tazo wai sun je kasuwa ta biyo ta gidan mu tace in anyi hutu naje nace Allah sarki tana da kirki. Sai da muka kammala na hada kunun aya nasa a fridge. Shima naman yayi na dauko na rufe na kai dining table na aje.
Nace ruky don Allah yi sallah ki dan gyara mana gidan bara nayo wanka tace to. Dakina ta tafi nima na tafi dakin Sulaiman nayi sallah kana nayo wanka. Lokacin har ta gama gyaran, dole indai yaro ya taso gidan mu dole yayi tsafta. Nace sannu ruky ko zaki watsa ruwa ne tace to. Tare muka tafi ina shiri ita kuma ta shiga wanka. Wata shadda na dauko light purple doguwar riga ba wani aiki jikinta don haka ta zauna cif! Jikina ina kwalliya Ruky ta fito, na bata kayan kwalliya sannan na dauko mata wata atampa ta wancan sallar na kuma taho da ita. Nace gashi saka. Ta amsa ta shirya knocking naji ana yi don haka na tafi na bude.
Da murmushi na tare shi, shima murmushi ne shimfide a fuskar sa nace sannu da zuwa na amshi jakarsa ya lakace hancina yana fadin sai kin ja min aji zaki bude ne? Nace wace ni? Yace ke a wadda nake so. Ina jin dadin yadda yake nuna min so ashe tare suke da Ahmad ban ma ganshi ba sai da Sulaiman ya kauce nace A'a Ahmad ashe tare kuke yace A'a Aunty ai bazi Gan ni ba ya fada yana dariya. Sulaiman ne ya ce nashi zoka shige.
  Kitchen na wuce na kawo masa ruwan sanyi ya sha. Tukun muka wuce daki, na taimaka masa ya cire kayansa yayi wanka ya kuma shirya jallabiya ce mai gajeran hannu muka fito. Suna nan suna ta hira abinsu nace to KU taso muci abinci ko?
Ni nayi wa kowa serving kana na zauna muka ci ni da mijina. Sai da muka gama ruky ta kwashe kayan ta kai kitchen. Nima na bita don na basu guri suyi hirar su cikin nutsuwa.

Sai dare Yaya sambo yazo daukar ta a babur dama tun kan yazo ta shirya nace ta dau duk abinda take so. Ni dama na sani Ruky akwai son gayu kayan kwalliya ta diba da turare na bata wata powder nace ta kaiwa maama. Da yazo ya kawo cake da meat pie yace inji Yaya rabi nace to 7k na bata nace ta kaiwa Yaya rabi 2k Mama kuma 5k ta amsa. Har waje muka raka su Sulaiman yaba Ruky 2k da kyar dai ta amsa suka tafi. Sulaiman ya ba Ahmad key na matarsa yace gashi kaje gidan Alhaji kace ya baka sakon, ka kwana acan gobe kuma 6am tayi maka a gidan nan. Don da wuri zamu tafi yace ina? Yace yan leman. Har mota muka raka shi kana muka rufo gidan. Tun a parlour ya sure ni bai dire a ko ina ba sai kan gadonsa. Ya kuma biyo ni nace ni daga ni mutum yazo hutu ka hana shi zama yace ai laifin kine? Nace ni kuma? Yace kwarai mana duk kin rikita min lissafi ina bafulatani na mai kunya kin maida ni futsararre nace ni ba ruwa na yace kece da ruwa mana. Abu ya rada min a kunne nace A'a ni kaya zan hada mana kaya. Bai min magana ba sai sakwanninsa naji a jikina.
Sulaiman akwai iya soyayya kullum style dinsa daban ne masu rikitarwa nima na fara sabawa yanxun da salonsa..............
Sai sha daya muka samu nutsuwa ni da shi tare muka yo wanka tara dashi abinmu. Kaya ma tare muka shirya dashi cikin akwatuna yace gashi nan shi kwana daya zai yi ya dawo nace ni dai don Allah ka tafi dani ba zan ji dadi ba in ka tafi ya rungume ni yace kar ki dawo two weeks is just like two seconds nace to you but,to me it means more than thousand days yace kar ki damu I will  always be by your side na dan yi murmushi yace ki yi hakuri farkon auren ki na kai ki kauye ko nace A'a yace ina so ne ki saba da dangina nace to. Sai daya saura saura muka kwanta. Da asuba kam da muka yi sallah ba mu koma barci ba shiri muke tayi sosai.
Tea kawai muka sha. Allah sarki Ahmad shida ko sai gashi yazo. Sai da muka biya ta gidan Sauda muka yi masu sallama kana muka wuce.
Ahmad shi ke driving ni da sulaiman muna baya, yana rungume dani ta gefen kafadar shi. Yana ta aiki a system dinsa. Muna barin kanona fara jin barci nace Excellency, barci nake ji yace to kwanta. Da cinyarsa yayi min pillow na kwanta barci mai dadi nake yi.
Mafarki wai ga wata damba nan tana ta bin mu ni da sulaiman muna ta gudu. Daga karshe nayi tuntube na fadi shi kuma yayi gaba sai da yayi nisa ya dawo ya dawo kafin ya kawo guna dambar har ta karaso ta yi wani irin wurgi dani.

To fa..... Meye meaning din mafarkin A'isha? Kada fa... #mouth zipped#

Ehen ga desert na baku idan kuna son dinner then lemme see comments Kamar ruwa, I promise you the next chap but idan Yayi kasa just forget about next page se gobe Inshaaa Allah.

Yours Truly

Shatuuu ♥️

WADATAWhere stories live. Discover now