THIRTEEN

2.7K 302 7
                                    


*WADATA*
_Thirteen_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

@Mai_Dambu Naga Notification dinki, I'm overwhelmed so ga Dambu da zafinshi yana tururi....... I dedicate this page to you Sister

Bakina na masifar rawa na furta

" Sannu da zuwa Inna"

ta amsa da ka shima sannun yayi mata ta amsa da kai. Kitchen na shiga na dauko ruwa da lemo na kawo mata na durkusa na gaida ta, ta amsa ciki ciki. Tashi nayi don basu guri don su zanta. Tsawa ta daka min tace

"Zo kwasje kayan ki bani da bukata"

Sulaiman ne yayi mata magana ban dai san me yace ba. Ni kuma na dawo nace

" Inna kiyi hakuri in laifi aka maki don Allah ki sha."

Tace cikin daga muryarshi saboda matar batasan ayar da akace muryar mace Al'aura bace, she's just lousy,

"Ba ke kika man laifi ba, don kuwa nasan sake kika samu, fuska kika gani, kinga ko duk Wanda ya samu rana dole ne zai yi shanya. Ba laifin kowa bane illa kai Lamido da ka nuna nan duniya baka da kamar ta har ni kaina ka bata damar da zata raina ni ta raina yan uwanka bayan kana ta dawainiya da danginta. In banda zuciyar ka ta sike kazo da matar nan amma ta biyo tayi man sallama taki saboda tana ganin tafi karfin mu. Ko da sallah kai daya kazo sai wani nama da ta aiko man..." Ta juyo gare ni da abinda nake sai hawaye taci gaba.... "Ki kalle ni nan ni ba mayunwaciya bace uwar ki ya kamata ki aikawa taci ba ni sumayya ba...." Ta kuma juyawa ga danta "yaushe ne ka zama wani gaula da har yan uwanka xasu zo gidanka amma fitsarrariyar yarinyar nan suna zaune tana sa tsintsiya tana share su wato su ga kazamai ko? To ki gode Allah ni ba jahila bace da yau sai kin bar mijin da kike tunkaho dashi, har da wani sa wata yar iskar kawar ki ta zazzage su? Ke kin samu guri ko. To bara kiji wallahi ba ke yar birni ba Allah yasa kece dala sai na iya da ke. Kai kuma duk irin abinda kake ina samun labari har wani mota ka saya mata ko? Ina ce shi mahaifin nata ba shi yace zai dau nauyin karatu nata ba to daga yau har bayan rai na ban yarda ko biyar ka kashe mata a karatu ba. Kuma zancen mota so nake kafin jibi na tafi ka amshe ta ka ba Ahmad da yake ta fama ka saya masa kaki...."

Sulaiman ne ya katse ta da cewa

" Inna kiyi hakuri ki fuskanci gaskiya wannan abin duk ba na tashin hankali bane...."

Ta katse shi

"Bar ni kan karya ta tunda ka zama haka."

Yace

"A'a Inna sam! Kinga makaranta ni nayi wa mahaifinta alqawari zan biya Inna kuma kema kinsan girman alqawari ai. Kuma kinga mota da sunan ta na saya ba damar nayi kyauta da ita in har ba ita ta bada da kanta ba"

Tace

"Wannan kuma ya rage naka ni dai na gama zance idan kuma nima ban isa ba to shi kenan sai naji in yaso sai na sallama mata kai."

Yace

" A'a Inna ba zai ayi haka ba yanzu to ki kira Ahmad din ya dawo gobe in yaso sai muje kotu a yi takardu ta bashi motar"

Babu ko Kunya matar nan tace to. Tashi tayi tana fadin

"Ina masaukina ko nima a nan falo xaa bar ni?"

Dakin baki ya dau jakar ta ya kaita, nima da kyar na ja jikina zuwa dakina. Kan gado na fada na saki wani matsanancin kuka ya Ilahi! Wace irin masifa ce wannan? Shi kenan ni ba zan huta ba? Duk wannan meye laifi na a ciki? Me zan yi don na burge su?. Na jima nan ina ta kuka har kaina ya fara sarawa zazzabi mai zafi ya rufe ni.
Ban ji shigowar shi sai kawai naji yana kiran sunana

WADATAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن