THIRTY SEVEN

2.3K 278 16
                                    

*WADATA*
_Thirty seven_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

⚠️Not edited read at your own risk plz!

Wajen magriba sai gashi ya dawo dauke da kaya niki niki. Ni kam ina zaune takure jikin kujera ina gadin ta har lokacin barci take yi, shi ya aje kayan duk inda ya dace. Ya dube ni bara naje masallaci nace to. Da nayi sallah na hade kayan ko wanne inda ya dace na sake hada dakin tsaf. Ina isha naji tashin ta da na idar na taimaka mata ta tashi amma kar su ga nayi masu karambani sai na fita na kira nurse tazo tayi mata abinda zata mata ta tafi sai gashi ya dawo nace

"Ya kamata a samowa Amatullahi abinda zata ci"

Yace

" Kamar me kenan?"

Nace

" Something watery me Dan zafi tunda Yanzun ta tashi"

Yace

" Ba damuwa na hado dashi a cikin kaya sai dai ko ruwan zafi ko?"

Nace

"Akwai nan cikin dispenser"

Bai ban amsa ba wayar shi ta fara ringing ya zura hannu a aljihu ya dauko ta. Ina jin shi yayi sallama tare da fadin Usman.... OK..... To bari na fito yanzu.... Aha ku jira......... Yace dani bara na dawo nace to.
Ruwa na diba a mug mai dumi na hada mata, ta fara sha naji sallamar su Mama, Umma da kuma Yaya sai Yaya Sani. Dan rug din da ya kawo mana na shimfida masu ni kuma ina bata abinci da kyar dai take sha ina lallaba ta tana sha. Su Mama sun kawo min kaya da kuma abinci sai kayan dubiya na lallaba ta taci guda biyu sannan na gyara ta kwanta. Sai goma suka tafi na raka su shima Sulaiman ya tafi tare dasu. Nima ina dawowa nace

"Amatullahi mu kwanta ko?"

Ta daga min kai alamar to. Na canja kayana kana na rufe mana kofa na kwanta a kasa tace

"Mu kwanta tare Mami "

Nace to. Na gyara mata kwanciya muka kwanta tare muka yi addu'a har barci ya dauke mu. Qarfe daya na farka na tashi na shiga toilet na dauro alwala nazo na dukufa cikin sujjada ta ina fadawa Allah dukkan bukata na da kuma matsaltsu na har sai da naji zuciya ta ta fara sanyi sannan na dau Quran dina na fara tilawar sa har qarfe uku sannan na koma na kwanta ina hailala har barci ya dauke ni. Da asuba da na tashi tana ta barci abinta, nayi sallah na tsaya zikiri har qarfe bakwai sannan na tashi. Kayan wanke wanke na hade su guri guda. Na hada mata ruwa nayi mata wanka da kaina na shirya ta cikin kayan da aka kawo mata wani riga da wando ne iya guiwa sai vest dinsa na shan iska sai dai ba hula don haka a kaya na na dauko mata na saka mata. Nayi wanke wanke a toilet da wanki na kuma share daki na nayi moping zuwan cleaners har na kammala komai. Na shiga wanka abuna sanin mu biyu ne yasa na dauro towel din Amatullahi wanda tsayin sa ya tsaya a cinya ta bai kuma rotsa ni sosai ba. Sam ban lura dashi ba sai da na tsinkayi muryar Amaturrahman na cewa Baffa, ashe wanka tayi. Ya dago idonsa muka hada ido shi yayi saurin janyewa kana ya mike ya fita sannan na shirya doguwar riga na saka ba wani turare sai roll on tunda muna tare na kuma dauko mayafin material din na yafa. Na tambaye su me zasu sha? Amatullahi tace dani yoghurt Zata sha ita kuma Amaturrahman tace golden morn zata sha nace to.
  Kowa na hada mata abinda take so na bata sai lokacin ya dawo ina kwana nace dashi yace kin tashi lafiya nace lafiya kalau. Kwanukan da su Mama suka kawo ya buda ni ko ci ban yi ba kuma har yanzu banda ra'ayin ci, ya dago idonsa ya kalle ni kallon why? Na kauda idona ina bawa Amaturrahman golden da katuwar loma don na lura har wani nishadi take Amatullahi dake kwance ma sai dariya take yi. Mug ya kai hannun sa ya dauko guda biyu ya hado tea yazo gaba na yaja kujera ya miko min nace ni fa na koshi yace saboda? Nace naci abinci ya jinjina kai bayan fada da tsiwa a Kadunan har karya kika koya? Nayi kicin kicin da rai na nace don Allah ka kyale ni. Tea din ya mikawa Amaturrahman yace rike min tare da fara nade hannun rigar sa da fulatanci tayi masa magana da murna shima ya mayar mata da murmushi, gaba daya sai suka saka dariya suna shewa. Abun ya sosa raina don haka na mike da zummar na fice, fisgo ni yayi na fada jikin shi wani irin shock naji kamar an jona ni a socket wani abu na fisga ta. Na kuma tabbatar shima yaji a kunne na yayi mun rada cewar ki sha tea din nan kafin na dura miki kin ga tare muke da yara. Na san zai yi don haka na karba na sha ya kuma miko min cornflakes na shagwabe fuska tare da fadin ni fa na koshi yace sai dai an yi duren kenan? Dole na amsa na fara sha naji ana knocking da hanzari na tashi na je na bude kofar Dr ne da nurse sun zo duba Amatullahi jiki da sauki suna ta zolayar ta akan yar lele har tayi fes da ita. Shi ya qarashe shanye cornflakes dinsa.
Da rana an zazzo dubiya sauran yan gidan mu. Sun kawo min wayata mun yi waya da Baba yace na duba Amatullahi wani aiki ne ya samu a can Taraba don haka yau sun tafi nayi masa fatan Allah ya tsare. Suna tafiya sai ga Amina ban san gidan ubanwa taji ciwon oho? Ba jimawa sai ga Sauda da kuma Aunty Maijidda, naji dadin zuwan su sosai kamar hadin baki ko wani shiri suka saka ni a gaba da maganar ya kamata fa na koma gida na na zauna da yara na don kuwa kowa cikin mu ya galabaita mu mun ta komai mu maida auren mu. Sosai nasihar su ta rotsa ni kuma nima nayi tunanin haka sai dai ina tsoron tunkarar Baba da wannan maganar.
  Da daddare nurse tazo ta dauki Amatullahi a matsayin za suyi mata scanning don haka ni kadai na rage a dakin ba kowa babu inji sai lantern dana kunna mana bana son haske sosai don haka na rage hasken can kasa. Kafin ya shigo turaren sa ya fada min isowar sa, da sauri na tashi na rufe jikina da mayafi. Ya karaso ciki da fadin sun tafi scanning din ne? Nace eh. Kujera ya ja yazo daf dani ya tsugunna kan guiwoyin sa tare da rike hannaye na yace
   Aisha, na dago idona ina kallon shi ya ci gaba gani akan guiwoyi na na qasqantar da kai na gare ki, ki dubi girman Allah da Annabi sa ki dawo gidan mu. Da ni dake da yaran babu wanda rabuwar mu tayi masa dadi ki duba ke a wahale ni a wahale suma a wahale. Ni dake a daren da muka san junan mu mun yi alqawarin duk rintsi zamu zauna da juna a lokacin zaki yi zaton ban san me nake ba. Ki duba girman alqawari ki dubi yaran ki ko ba ni ba ki dawo cikin rayuwar mu. Hawaye taf idona nace yaya zaka yi da dangin ka? Yace kar ki damu da su Inna bata da matsala wannan Karon. Tashi nayi na jingina da bango hakan nan hawaye yake min zarya nace Sulaiman, Baba yayi wani furuci da zai hana mu kasancewa tare yayi murmushi yace kar ki damu bacin rai ne ya sa shi fadar haka ni zan same shi nace Baba kaifi daya ne in yayi magana baya canjawa yace nine fa sirikin sa nace da ne wannan ai amma yanzu shima yaransa kawai yake so......... Kuka yaci karfina kafin na ci gaba nasan ina sonka sosai Excellency sai dai ina tsoron abinda kaje ka dawo. Jikinshi ya janyo ni tsam! Ya rungume ni har muna jin bugun zuciyar kowa yace ki sani nothing worth comes easy dole a rayuwa akwai challenges da zaki yi over coming kar ki zama matsoraciya mana. Mun yi shiru duka mu biyu muna sauraron bugun zuciyar juna. Kafin can naji lebensa na lalubar nawa tuni dama lantern ta mutu, hakan nan zuciya da shedan suka rude ni nima na mika masa nawa. Wani sabon yanayi muka tsinci kanmu wanda ya tuno mana da wani lokaci gare ni dai kam dukkan soyayyar shi dake danqare a raina ya taso. Wani yanayi nake ji mai wuyar fassarawa shima gaba daya ya rikice wata kila ma mun mance mu din su waye...........
   Ihu da kukan mu da muka ji ne yasa mu sakin juna da kyar don gaba daya muna wani yanayi take kuma aka kawo wuta ta haske dakin gaba daya. Rahama ce tsaye goye da yar ta, shi ya jinginar dani jikin bango don ba zan iya tsayawa da kafa ta ba. Ya kai hannunsa ya taba ta cikin zafin nama ta tire shi tana masifa cikin yaren su da kyar yake iya mata magana. Bata saurare shi ta kunce yar bayanta sannan ta juya da gudu tana kuka shima ya take mata baya, ko baa fada ba nasan kishi take yi can sai gashi ya dawo, ina hawaye nace ta tafi ko? Dama na sani Sulaiman mun bi son zuciyar mu abinda muka yi sam bai dace ba abinda ba muyi da yarinta ba shi zamu yi da girman mu? Yace ki bar zancen nan please abinda ya faru ya riga da ya faru.
  Satin mu daya aka sallame mu yace na tafi dasu Amatullahi na bar masa Amaturrahim nace ya kawo ta yace A'a kuje dasu kawai akwai abinda nake hange ne nace to shike nan. Tare muka fito amma sai da ya ga tafiyar mu sannan ya wuce shima. Ana sallar azahar na isa gida don haka sallah muka fara yi na fada wanka.

Yana komawa gida bai tadda ta ba kamar yadda yayi tsammani. Bedroom dinta ya nufa nan bata nan sai dai wardrobe din ta a bude an fiddo kaya a kasa sai kuma akwatuna a kasa babu ta tsakiya hakan ya bashi tabbacin da cewar yaji tayi. Bai damu ba yasan duk inda take kam dole zata dawo gare shi. Amaturrahim ya dauka ya kaita dakin shi, kan gado ya aje yayi shirin wanka sai da ya fito kana ya canja ta ya kuma bata abinci. Sai da tayi barci ya shiga tunanin duniya, bai wani damu da tafiyar Rahama ba amma maganar Aisha na damun sa a rai bai san kuma ta ina zai fara ba, ta gurin Inna ko kuma ta gurin Baban ta?. Kansa ya kulle sosai amma wata kila zai yi kokari ya samu Usman acan kasuwa suyi magana dashi, ya kuma yanke gobe zai je.
Da safe ya dau Amaturrahim ya kaita gurin Aunty Maijidda. Daga nan ya wuce kwari dama ya san shagon don haka ba wahala ya wuce can. Bai fi minti uku ba sai ga Usman din ya karaso don yaran shagon kawai ya samu.  Da mamaki ya tare shi yana fadin malam Sulaiman, kai ne haka? Yace wallahi yace to shigo daga ciki mana kana waje.
Ciki inda suke kirge da kuma ajiyar kudi ya kai shi suka zauna kan tabarma kamar ya san dama magana yazo. Sai da suka sake gaisawa sannan ne ya ware masa duk abinda yake ransa ya kuma qara da cewa.
  Kaina ya kulle ban san yaya zan yi ba? Ina kuma kunyar tunkarar Baba da wannan maganar Yaya yace ai Sulaiman abinda ya zama dole ta fa wajibi ne ayi shi ka fahimta? Kai da ita duka babu wani abokin zama da ya dace da dan uwansa face ku. Amma wani hanzari ba gudu ba yaya matasalar dangin ka? Bana so wannan Karon ma a sake samun matsala kamar da yace tabbas matsala bata yayewa gaba daya cikin rayuwar mutum akwai jarabawa akwai kuma kaddara. Amma ina mai tabbatar maka cewar kaso sittin cikin dari ya kau Usman yace to inin haka ne abun yazo da sauki amma ni yanzu shawara ta shine gobe insha Allah Baba zai dawo daga Taraba zuwa jibi in ya dawo sai kaje kuyi magana dashi ina jin insha Allah babu matsala a gani na. Sun dau lokaci suna tattaunawa kafin ya tafi. Usman ya dau atampa ya bashi yace ya kai ma Amarya.

Shatuuu ♥️

WADATAWhere stories live. Discover now