SIXTEEN

2.3K 316 32
                                    

*WADATA*
_Sixteen_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad

*Lovely Ammashiekh, sweetest Farida Maina, Beloved Fatima Zarewa, Dearest Surayya, Sweet Ya Ummah, Sister Abida, A'isha Major, A'isha kaagu, Maman Zahra,  Hijja, Maman heeshma, Oum Ifhan, A'isha jajere, Aisha Imam shehu,  Fatima idris, Amina Jamil, Ramlexxxx, Fatin zuly, Jiyology, Anty Ummin Danbatta, A'isha Akko, Reemah, Zeedee, Falt, Umm~Jaafar......I can't get to call all your names but be rest assured that I love you and thank you for 💕*

A kwana a tashi babu wuya gurin Allah Har na kuma samun wani Cikin, gashi me azabar  laulayi yasha banbam da cikin Amatullahi, Sulaiman ya damu kwarai da irin yanayin da nake ciki wani sa'in gyaran gida shi yake yi don ni ba qarfin yi. Wannan kam ba irin na Amatullahi bane.
    Ina zaune parlour yau ma kamar kullum bakina ne ba dadi gaba daya banda Appetite, Amatullahi na home work a gefe na ina rike da hannunta tana tracing. Sulaiman kuma yana kitchen yana soya man sauce din attaruhu da albasa wata kila idan naci zan ji sauki a bakina. Abinda ban taba koda tunani ba shi naji, Sallamar Inna da Fadimatu wadda tasa na dago kaina da sauri ban san sa'adda na mike ba a razane, ina fadin

"Sannun ku da zuwa Inna."

Fadimatu ce ta amsa da cewa

"Yauwa Aishatuuu Sannu da gida"

Inna kam cewa tayi

"Ina yake?"

bakina na rawa Ina stammering nace

"Yana... Ciki..."

Kamar kam an ce ta leka ta leka kitchen din ta hango danta na girki. Salati ta saki

"Innalillahi Wainna ilaihirrajuun! Ashe da gaske ne kam tabbas asiri aka yi maka sulemanu, ban taba yarda ba yanzu da kanka kake girki? Bayan duk namijin arziki yana can gurin aiki?....."

Shi ya katse ta da fadin

"Inna, ba haka bane bata da lafiya ne baki ga duk ta rame ba?"

Tace

"Haka zaka ce mana tunda ta shanye ka. Guri ta samu ta zauna"

Ni kuwa dana kame a tsaye tunda suka shigo sai sannan na samu na motsa naje na dauko masu ruwa da lemo na kawo masu. Fadimatu ke mata magana amma ban san me take cewa ba tunda ba hausa suke ba, Inna ta dube ni a wulakance tace

" Kwashe kayan ki kafin muma ki shanye mu. Yadda kika shanye man yaro kin hana shi zuwa gurina da yan uwansa sai dai kullum yana dawainiya dake da iyayen ki, to bani lamunta kinji ko? Na kuma roke ki ki sakar man yaro na haka abin ya isa Haka"

  Kuka nake sosai saboda I hate it idan akace Suleiman na dawainiya da iyayena, nace

"Wallahi Inna ba abinda nayi masa kuma ba wata dawainiya da yake yi dani ba, Allah tun farkon aurenmu da kika hana baya ga hakkin aure baya man wani abu ki tambaye shi mana"

Na fada hawaye na min zarya tace

"Ai baya cikin hankalinsa yanzu sai dai har gidan naku zani na gargadi iyayen naki"

Sai a sannan Fadimatu tasa baki tace

"Inna ki bar zancen nan don Allah ni da na san haka zaki yi Allah ban rako ki"

Sulaiman kam ba abinda yake sai bata hakuri. Ganin ina kuka yasa Amatullahi itama ta fara kuka tazo ta rungume ni. Daukar ta nayi na tafi daki na. Gado na fada nayi ta rasgar kuka Wanda ni kaina ban san dalili ba na yin kukan ba sede inajin gaba daya tamkar everything has crumble down, like the world is tumbling down. Akalla nafi awa uku ina kukan idanuna da Kaina Kamar zasu fado, kafin Sulaiman ya shigo ya dade kaina a tsaye kafin yace

WADATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora