FIVE

2.6K 324 4
                                    

*WADATA*
    _FIVE_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad: Vote, comment, Recommend..... Ilysm

*My people of SHATUUU's KINGDOM both groups.... Thank you so much so take this as a token of appreciation*

 
   
   An rage saura sati biyu bikina kowa nata shiri. Baba ya samu gudunmawa sosai maman Kaduna ta dau nauyin yi min kayan daki. Yan Kaugama sun aikowa da Baba kayan abinci da dubu goma yan jahun ma sun aiko da nasu gudunmawar bikin da wannan Baba ya hada da kudin gurinsa ya bayar don a qaro min sayayya
An raka ni Kaugama don yo masu sallama. Na zaga dangi har naje gidan wata yar yayan Baba da aka mata aure kwanan nan. Yadda na ganta ya firgita ni sosai samira jaruma ce sam bata da raki. Amma da muka je duk wani mai hankali zai gane mai ya faru da ita. Don hatta lafiyar ta canja idanunta duk sun kumbura haka dai muka gaisa tana ce man amarya kin sha qamshi nace aa tukun wannan kirarin naki ne ai tace kaiya amarci ko wahala ban san saada nace! mata da wuya ko? Dariya tayi tace aa ba wani wuya.
Ko da na dawo gida gaba daya duk na tsorace samira jaruma ma tana jin jiki bare ni raguwa. Na kuma tabbata Sulaiman ba zai raga min ba don qarara yake nuna min shifa ya matsu na tare a gidansa hakan ba karamin tayar min da hankali yake ba.
  Da yamma Yaya yazo yake ce dani Aunty Naima na son ganina gobe na amsa da to
  Da hantsi na shirya sai kabuga Yaya sambo ya sauke ni shi kuma ya wuce makaranta. Zuwa na bata qarasa aiyukanta ba don haka na taya ta muka qarasa. A motar Yaya da ya bari ta jani har unguwar gwammaja gidan wata mata muka je da ganinta kaga yar Maiduguri tana kiranta da Yana mun gaisa Aunty Naima ke fada mata gani tace to amarya sannu nace yauwa ina zaune suka yi lissafi Aunty Naima ta bata 30k ina tunanin ta kudin aikinta ne. Nan ko ta tashi ta fara hada kayan gyara ta fara aikinta har laasar.
   Ta qunso wani abu taba Aunty Naima tana min gargadin kar na sake na shiga rana na amsa da to insha Allah. A gida Aunty Naima na ta man bayani magunguna da tsimi ko me ne ta kira su? Oho mata, Na marairaice nace

" Don Allah Aunty ki bar su ni wallahi bana so"

tace

"Hmm lallai baki da hankali kuwa. Yadda mutumin nan ya matsu da auren nan kice kuma baki gyara jikin ki to wata qila tashin farko ko zama sai ya gagare ki"

nace

"Da wahala ko Aunty?"

  Zaunar dani tayi ganin duk na rikice ta yi qasa qasa da muryar ta tace

"Ba wani wahala, da ace da wuya duk ba mu zama gidajan mu ba, abinda nake so da ke kawai ki sha don qwatowa kanki martaba a gurin miji yadda yake ta rawar kannan ai dole a fita kunyar shi. Ki nutsu ki tsaida hankalinki guri guda kina ji na ko? Da wannan ake riqe miji in kin qiya matan banza su riqe maki shi"

Nasiharta ta shige ni amma duk da haka dai raina akwai tsoro da fargaba, a lokacin na yadda shi ke rike aure amma bayan na shiga gidan se Naga abin ba Haka yake ba, auren is not all about pleasures it's a treasure and thorns, na fahimci wannan armashi yake Kara mishi amma real deal din WADATA ce ta zuci.... Hakuri shi ne aure, shi ne mukai lacking Yanzun shiyasa auren ke wahalar damu saboda Yanzun tunaninmu da kayi aure dukkan damuwar duniyar nan ta Kare amma ba Haka bane mata!

Sai dare Yaya yazo ya tafi dani muka koma gida. An shigo satin biki hidima nata qaruwa Amina bello da Husna suke rabon Kati a gidajen qawayen mu don da gaske tilas su biki xasu yi sosai. Ga ni kam you can't believe it na sha gyara sosai in and out ita kanta Mama ta gyara ni duk da bata fito tace min ga amfanin abinda take bani ba. Randa na hadu da Sulaiman ji yayi kamar ya tafi dani sai dai ba hali. A bangaren xamantakewar aure Umma ce ta cire kunya ta yi min bayanin abubuwa sannan tayi man fada sosai hade da nasihu. Yaya Rabi ma ta min nata gwargwado yadda zan rika kula da mijina.
A satin biki aka kawo lefe akwati shida kaya ne bana wasa ba Sulaiman yayi bajimta kowa ya gani sai sam barka yake an basu tukwuici dai dai da qarfinmu.
   Dangi sun fara hallara gidanmu ya fara cika. Yaya da Yaya sani sun hadu sun yi mana sabon fenti mai kyau. Duk kayan da nasan zan bukata na kwashe su na Kai gidan Maman Shahid wata makwafciyar mu. Gidan ba laifi kato ne kuma yaran ta biyu, mijinta soja ne din haka bai cika zama a gida ba.
Ranar laraba Yana tazo ta mana kunshi ni da sauran kawaye na dama Amina ma ta dawo guri wai har yanxu fushi take yi da yan gidansu. Husna ce da sauran masu zuwa su tafi. A ranar kuma aka je yi min Jere can gidana dake nan BUK quarters a nan new site tunda shi Sulaiman a nan yake.
  Ranar jumaa ta Kama xaa yi kamu a nan Mumbayya house. Da qarfe hudu na yamma, tun azahar muke ta shiri abinmu musamman Amina kawaye nata tururuwar zuwa kan dan lokaci gida ya cika taf! Maman Shahid ke ta dawainiyar abinci dasu don komi ita na bar wa. Mai kwalliya guda Aunty Naima ta dauko ashe ma cousin dinta ce itace ta tsaya akanta aka yi kwalliya aka gama a cikin kawaye ma masu so duk an masu. Gaskiya sun yi man kara anko suka fitar na wata atampa mai kyau kuma kowa yayi ta. Ni kam lafaya ce jikina fara tas sai aka hada min Dan kunne, takalmi, duk golden colour jamaa kar kuso kuga kyau dai an yi shi. Tun uku muka tafi saboda akwai tazara tsakanin mu da gurin bikin. Anan ma an sha hotuna sosai, qarfe uku da arbain da biyar ango yazo da tashi tawagar. Shi ya fara zama cikin tashi kwalliyar shi ta shadda Fara tas, Yayi kyau Har Ya gaji Don da kyar na daina kallonshi, kana ni kuma qawayena suka rako ni nan fa kowa ya saita camera sai hotuna ake.
An yi abubuwa su kidan qwarya dasu koroso mata sun taka rawa sosai daga nan kuma sai Kama amarya. Wata mata aka ba turaren da nake zaton yar uwar Sulaiman ce don na ganta kar! Kamar shi tana sanye da wani material maroon colour sai tayi ado da milk colour abin dai sai Wanda ya gani. Itace ta feshe ni da turare guri ya dau buda da hargowa, ta kuma bude fuska ta a cikin mayafi na. Nan kam na sha hotuna ni daq angona.
Sai shida aka tashi anyi rabon mahuci na kaba mai sunan mu jiki sai maburgi na miya da lalle sai goruba da magarya.
Taro kam yayi albarka ba Wanda zai ce baa kyauta masa ba.
   Gidan maman Shahid muka yada zango, alwala muka yi don sallar magriba dama mun yi sallar laasar kan mu tafi saboda gaskiya bana son haden sallah kuma ina so aure na yayi albarka.
  Yau asabar tun safe nake jina sukuku haka nan jikina duk ba qwari kawai dai ina daurewa ne. Haka kawai gaba na ke yawaita faduwa ban kuma san dalili ba duk jikina ya mutu ko wanka ma na kasa yi. Ba yadda su Amina basu yi ba amma naki yarda nayo wanka, sai da aka kira Mama tazo tayi ta lallami na kana nayo wanka. Shadda ce yau zan saka ina kwalliya wayar Sulaiman ta shigo min nayi kamar ban ji ba. Amina ce ta miko min tace ango yana kira na amsa gami da karawa a kunne na nayi masa sallama ya amsa da cewa

" Wife"

Har raina naji Kalmar sai kawai nace umm yace

"Ga mu nan kan hanya yanxu aka gama daurin aure "

nace hmm yace

"Lafiya kuwa? Ko tun yanxu xaa fara ja min aji ne "

Kasa furta komai nayi Se wani bakon yanayi da Ya shigeni, seriously ni A'isha na zama matar aure? na girgiza Kai kamar yana kallo na yace

"Alright bara na bar ki kawai sai an jima ko?"

Nace Uhmmm

yace yauwa around 2 xaa zo daukar ku don ayi komi in time. Bance komi ba na kashe wayar, shiryawa na qarasa yi. Su Amina ma duk sun shirya na shiga gida ana ta gaisawa dani. Abokan wasa nata tsokana ta ni ban iya ba sai dai nayi ta murmushi kawai. Ina son kebewa da Mama amma tana cikin sabga Yaya Rabi ma da Aunty Naima are all occupied. Dole na hakura na share kawai. Wajen daya muka tafi sallah gidan maman Shahid anan aka kawo min abinci nace na koshi don cikina a cike nake jinsa.
Maman Kaduna ma tazo da iyalanta sun yi kara don sun kawo gudunmawa mai yawa don kusan duk ita aka raba
Rukayya ce ta shigo tace Yaya Mami wai kizo inji Mama dangin Yaya Sulaiman sun zo da maman Yaya Amina nace to gani nan zuwa tace to. Ruwa na kuma watsawa na shirya cikin wani Lace riga da Zan!ne blue colour.
A parlour din Baba na same su mata ne guda hudu uku kana ganinsu kaga hutu don yadda jikin su ya muna sai dayar dai itama tana tsananin Kama da Sulaiman hakan yasa nace wata kil yar uwarsa ce. Har qasa na sunkuya na gaida su, har Mummy ta Amina bello dayar ce tace Masha Allah, amarya tayi dama na sani dan gidana sai yayi zabe wannan jinkirin ba a banza ba kowa yayi magana har wannan yar uwar Sulaiman din anan na sake tabbatarwa don daga yadda take magana zai tabbatar maka bafullatana ce. Aunty Naima ce ta shigo ta kawo masu abinci fried rice ce sai dambu da kunun aya. Tare muka fice ta kaini da gaida yan gidansu da yan gidansu Yaya Sadiya matar Yaya Sani,
   Karfe biyu Yaya Rabi tazo tace na shirya yan daukar amarya sun taho. Nace Yaya Ravi don Allah a bari sai gobe tace aa ba ruwana umarni daga Baba!

To fa aure dai gashi an daura.... Me kuke gani? Ya tafiyar zata kasance tsakanin A'isha da Suleiman?

It's always Shatuuu♥️

WADATAWhere stories live. Discover now