TWENTY ONE

2.5K 287 16
                                    

*WADATA*
_Twenty one_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad


Da safe kam da kyar ya lallaba ta tayi sallar da yake ta fama da ita tun asuba. Tabbas kam tayi kokari ta kawo masa budurcin ta ta kuma isa mace gurin mijinta, ya jinjina ma kokarin ta saboda bata da lafiya. Yanzu haka zazzabi ne a jikinta sosai, don haka bayan ta idar da sallah ta kwanta kitchen yaje ya hado mata tea sai bredi ya kawo mata. Kadan taci ta sha magani sai barci.
Shi ya gyara gidan ya dauko forms din ta ya cika gaba daya. Girki ya dora ba wani abu mai nauhi ba indomie ce ya dafa yaci abinsa sai tea.
Ita kam hakimar sai sha biyu ta tashi a barci, jikin kam ya ware sosai dama ciwon jiki ke dan damunta dazun amma yanzu taji alhamdulillah da sauki sosai. Toilet ta fada tayi wanka abinta. Ta fito ta shirya cikin cikin wata shadda riga da zani. Ba laifi tayi kyau don ita kam akwai kyau. Bata kai ga fitowa ba ya shigo yau din kam baki daya ma kunyar shi take ji.  Hannun ta ya kama tare da zaunar da ita bakin gado, yayi mata godiyar daren jiya tare kuma da sa albarka.
Cikin kwana ashirin Sulaiman ya more sadakin sa. Ya kuma dan saba da matar sa to dama a irin zaman nan ne halin kowa na ainahi yake fitowa in kuwa baa yi dace ba sai rigima shike nan sai zama ya tabarbare.
Yau yaje ya gama mata komai ranar asabar ta sama zata fara zuwa makaranta ta islamiya. Ita kuma boko da jamb duk wannan Monday din ne don sun fara lesson. Jamb lesson kam Thursday and Friday shi kuma makarantar Monday to Wednesday ne daga shida na safe zuwa uku na yamma.
Sai da yayi submitting ya dawo dauke da uniform dinta da kuma kayan karatu. Tana hada masa abinci ne tayi kwalliya abinta ba laifi, nan doguwar kujera ya zauna yayi mata! Magana tazo ta zauna yayi mata bayani dallah dallah. Tsaki taja tare da fadin

"Wannan fa wulakanci ne kamata zaka maida Secondary? Saboda me to?"

Yace

"Kinga it's not something hard, kinga kano is unlike Adamawa kina bukatar good grades kafin ki shiga makaranta saboda there's a lot of competition, ki gane mana"

Da masifa tace

"Allah ba inda zani wannan ai raini ne yaya zaka min haka ni ilimi na ya wadace ni ita waccar matar taka ai ba haka kayi mata ba tunda ita son ta kake yi."

Tana fadin haka ta mike tayi ciki. Gwaggonta ta kira tana kuka ta fada mata komai. Tace

"To meye ciki don kin koma makaranta ai karatu da dadi"

Tace

"Gwaggo fa..."

Tace

"To yanzu yaya zan yi miki? daga aure sai matsala? Nifa kinga kiyi hakuri kawai ina ce shi din ba malamin jami'a bane? To yaya zai zauna dake baki yi karatu ba?"

Tace

"Nifa Gwaggo in jami'a ce zan yarda amma fa wai baya zai maida ni?."

Ganin ba goyon baya yasa ta kashe wayar ta kira Inna ta gaya mata karya da gaskiya tace to ko ta sha kuruminta ba inda zata ita ma jibi zata zo kano zata yi ma tufkar hanci.
Ilai ko sai gata Sulaiman ya sha fada yadda baya zato a gurin Inna akan ya rabu da ita.

"Waccan matar kam ai baka mata haka ba? Sai don yanzu nasa ka auri wannan shine kake yi min haka ko?"

Sulaiman yace

"Ni fa gaskiya Inna ba zan zauna da macen da bata yi karatu ba saboda ina gudun tarbiyar da zata yi ma yarana."

Ita kanta ta sha mamakin kalaman sa saboda bai taba mata musu ba ko rana ce indai tace dare ne to fa ya zauna a dare ne. Amma sai taci gaba

"Nida banyi bokon ba wace tarbiyar ce ban maku ba? "

Kanshi Ya girgiza Yace

"Inna, da fa da yanzu ba daya bane ada kam kana iya zama ba ilimi amma yanzu lokaci fa ya canja. Ni tunda kince baki so shi kenan ya wuce amma fa ko diploma ce zan samo mata dole dai sai tayi karatu."

WADATADove le storie prendono vita. Scoprilo ora