*WADATA*
_Twenty three_✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
💥Shatuuu095@wattpad
⚠️Biko just read at your own risk, I'm too lazy to edit, Afuwan, any question just DM me I'm gonna reply ASAP
OMG..... Yesterday I forgot writing title and page number, Ayya lovelies Kai ya dau zafi, though Naga Kun fahimceni. Thank you and the page is wholly dedicated to Ghost readers, no comment, no votes..... Hhhhhhhh.... I still appreciate bcoz I'm one of them, I feel a heavy load commenting on novel..... Ilysm I swear!
Jiki na wuce na shiga bandaki na watsa ruwa, dama ba sallah zan yi ba don haka na malele kan gado abuna. Zuciyata ce ke yi min suya sosai Wanda ban san dalili ba na kuwa tabbatar hakan bai da nasaba da ganin matar Sulaiman, ni din kam ko mahaukaciya ce to yau kam na tabbatar Sulaiman na son matar shi don ko ga karamin ciki nan na lura jikin ta wanda ita kanta ba lallai bane in ta san dashi. Na share hawayen da suka zubo min ni kuma haka tawa jarabawar rayuwar take, ina son Sulaiman sosai ina kuma kishin shi sosai a raina......
Sallamar Baba da na jiyo a parlour ce ta katse ni, na mike da sauri na dauki dankwali na na fito. Yana tsaye bakin kofa nace sannu da zuwa Baba yace yauwa yar uwata ya hanya? Nace alhamdulillah yace sannu da zuwa ya wajen su Yaya A'i din? Nace duk suna lafiya tana gaishe ka ma yace ina amsawa.... Bara naje daki ko? Nace to.
Ciki na koma na dau wayata na kunna suratul bakara ko na ji sanyi cikin zuciyata. A haka har barci ya kwashe ni.Yau kam Yaya Sadiya na qudurce zuwa ina son sanin wasu abubuwa game da Barrister tunda har ita tasan shi. Karfe goma har na gama shiri muka fito ni da Rukayya. Tare muka tafi aka sauke ta makaranta ni kuma na wuce.
Ita daya na samu a gida sai Afaf da take goyo yanzu, tana wanke wanke a bakin famfo na kitchen. Na dau Afaf gami da shiga tana gani na sai murmushi tana fadin wata sabon gani, Hajiyar Allah yau kece gidana? Nace kai! Yaya Sadiya in banda mu biyu ne ai sai naji kunya ayi zaton bana zuwa tace zuwa kike? Nace to ayi hakuri tace to mu shiga nace A'a bara na taya ki tace Allah ki shiga gani nan zuwa nace to.
TV na kunna amma sam Afaf taki zama nace to tafi gurin maman ki.
Minti ashirin sai gata da kayan tea a hannu nace sannu auntyna tace yauwa. Aje min tayi a gabana, muka gaisa tace mu karya ko?. Sai da muka gama take ce min ashe Ya Bashir zaki aura? Nace wallahi fa rannan ai yake ce min ai yasan Baba tace eh wallahi da kakanmu da kakansa na wurin uba Sune suke uwa daya uba daya kinga kenan mu second cousins ne nace eh shine ma zancen da nazo ji ina so kiyi min bayani akan shi sosai. Tace to.
Barrister Bashir dai da mu gaba daya yan asalin garin Maigana ne ta Kaduna zama ya maida su Kaduna kamar yadda mu ma ya kawo kano sanadiyar aikin iyayen mu. Matar shi Sa'adatu ina tunani yar nan Kaduna ce tun yana degree suka yi aure ita din yar masu kudi ce sosai kuma tayi karatu cikin wayayyu. To tunda ga nan suke zaman su.
Ni dai gaskiya ba zan boye maki tunda ba wani zama muke sosai da Bashir sai dai ko in abu ya faru mun je Maigana ko su suka zo ko kuma mu munje wurin su. Halayen sa ba kushe illa shi mutum ne mai sabga irin mutum ne shi da zaki ga kamar ba abinda ya dame su so careless. Kinga kuma ko wace mace ba zata so haka ba. Nace to tare da jan numfashi nace to misali cikin gidan shi fa? Tace eh to kinga dai na ce maki ni ba zuwa gidansa sosai nake ba na dai fada maki matar sa wayayya ce in tana da matsala ba baka ganewa da wuri mu dai gaskiya zuwan da muke gidan ba ta da matsala nace to.
Mun dan tattauna sosai da ita na kuma gamsu da batun ta a raina. Da nayi sallar laasar rana tayi sanyi sai na tafi gida.
Washe gari da safe sai gasu Amatullahi baban su ya kawo su. Mama har da ce min Sulaiman duk zuwa sai ya tambaye ni na fita mu gaisa nace ba inda zani Mama yaje can ya qarata shi da yan uwansa. Tace to, da murnar su suka zo gurina nima ina kewar su sosai a raina. Na lura da dan sauyi tattare dasu sai dai bana so na tambaye su don kar na binciki abinda zai sani a damuwa. Sulaiman ya aiko min da set na kayan cosmetic na st.Ives sai manyan lace guda biyu. Mama har da ce min tunda kin kasa fita shi gashi yazo ai har da sako nace kai Mama. Da kaina na yanke masu farce na ce su zo mu fita. Can saloon muka je aka wanke musu kai. Muka biya ta Shop at Sheshe nace kowa ya dau abinda yake so, sosai naga suna murna sai naga da kamar ina shiga hakkin su tunda na baro gidan na daina jan su jiki. Kafin mu koma gida na biya dasu ta oasis na unguwar mu na saya masu yoghurt da ice cream har da yaran gidan mu.
Da muka dawo gida ana ta sallar laasar don haka sallah muka yi suka sha ice cream dinsu nayi masu kizo kalba ta twisting mai kyau, ina jinsu suna ta yaren su a raina nace ashe an kowa maku? Umma ce mai cewa kuyi mana shiru gwarawa.
Cikin kayan da na siyo masu na saka masu daya. Na hade masu saurin saboda da dare baban su zai zo su tafi nima banda aiki ya ma bashir yawa da yau zan koma. Na tambaye su performance dinsu a makaranta sun yi min bayani na kuma ji dadi sosai. Na dade rabo na da nayi farin ciki irin na yau ko da muka yi waya da Barrister sai da fuskanta na kuma fada masa yace na basu waya su gaisa. Sun jima suna hira musamman Amaturrahman mai baki sai dai ba sosai hausar ta ke fita ba.
Ana sallar isha kam sai ga Sulaiman yazo daukar su, Amaturrahman har da kukan ta na taho mu tafi gida nace zan zo wata rana su dai su tafi. Da na dawo har da kwalla ta.
Da safe kam shida ina tasha Yaya sambo ya raka ni na hau mota don asibiti nake so na wuce direct.
BINABASA MO ANG
WADATA
RandomThe story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk Wanda Yayi hakuri bazai Taba tabewa ba, labarin A'isha da Suleiman masoyan gaske Wanda kaddara ta d...