*WADATA*
_Thirty six_✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
💥Shatuuu095@wattpad
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
Kainuwa fans group from 1 to 12.....this page is for every member that's together with us on this journey
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*WADATA*..... _The story of A'isha and Suleiman... The fated lovers_
Kwana uku na kira Dr Mukhtar nace yazo ina so muyi magana dashi yace
"Gida?"
Nace
" A'a"
" Asibiti kike so mu hadu? "
Nanma Kaina na girgiza nace
"A'a muje dai can wani park"
Yace to. Kafin a tashi na silale muka je, bayan mun gaisa dashi nace
" Ina so na san wasu abubuwa game da Kai ne"
Babu bata lokaci ya Fara da
"Suna na Mukhtar ni dan asalin garin Takai ne ta jihar Kano yawancin mu maza ne a gidanmu, babbar yayar mu ce mace amma ta rasu sai kuma autar mu. Mahaifina ya rasu sai mahaifiya ta kawai wadda ta tsufa yanzu. Nayi karatu na a nan kasar specialization ne kawai naje Russia nayi akan pediatric.
Ina da mata ta daya Bilkisu sai yara uku babbar 'Yata Ni'ima tana nan BUK tana medicine level 2 sai kuma mai bi mata Safiyya Mummy na tana SS1 sai kuma Ammar yana primary 4 amma dai daga shi bamu sake haihuwa ba sai wata kila in kin shigo ki haifa mana naki kyawawa.....ya fada da dariya
Bilkisu na aiki a asibitin Malam, tana bangaren mata wato gynecology. Zama na da ita Alhamdulillah ba matsala zan aure ki ba don ta gaza ba A'a sai don kawai ke ma ina son ki."Ban katse shi ba har ya kammala nace
"Allah Ya raya su mummy, amma zan sake tunani akai"
Yace
" Ba damuwa hakan ma na gode sosai."
Na koma gida zuciya ta cike da tunani iri iri. Message ne ya shigo min, kamar na san number din amma na mance. Na karanta hakan ya tabbatar min da Sa'adatu ce
Na turo miki sakon nan ne don ki fita harkar miji na. Idan kika kuskura kika sake dawowa rayuwar mu nayi miki alqawari sai na saka ki a qunci na har abada sai kin ji gara wancan zaman da wannan, ina baki shawara ki nemi wani mijin amma ba nawa. In kunne yaji.... ….. Mai kashe........ Ki kuma sani tsunstun da ya ya ja ruwa....... Kamar nayi mata reply amma sai na share ta kawai babu amfani kuma dama kofa take nema ko yanzu kam ai na sha gaban ta nayi mata nisa.
Bikin yar Zinatu ya tashi sai shiri suke ba kama hannun yaro, biki ne da suke ji dashi sosai don Zinatu ta dan fi su dama dama a budin miji. Da suka zo Kano sayayya ne suka biyo ta gidan Sulaiman. Ba laifi Rahama ta karbe su anan suka fada mata makasudin zuwan su na don Allah gwal din da aka saka mata lefe zata arawa Zinatu domin ta kece raini ranar auren yar ta kar yan uwan mijin ta su zo su raina ta. Da kyar ta ara masu akan bayan biki zata dawo mata da abinta da kuma kudin aro duk suka yarda a haka a kuma matsayin sirri aka yi abun, ba kuma sa son ko da Sulaiman yaji labari tace ba matsala.
Shi bai san sun yi haka ba sam! Tunda kwana biyu baya zama gida ayyuka sun rikice masa na makaranta da kuma harkokin sa saboda haka baya zama gaba daya yanzu gidan na hannun Rahama itama tana can nata gantalin da bata fasa ba. Yunwa kam yara na shan ta ba su Amaturrahman ba har ma da tata yar mai shekara tunda gaba daya Sulaiman ya saba masu da kayan madara tunda ita girki sai tayi ra'ayin in ma anyi bata wuce jallof da gara ma a kira ta dafa duka. Shi dai yakan kokarta ci ba don son ranshi ba sai don ba yadda zai yi amma yara sam basu ci ita kuma tace ba ta iyawa da wannan iyayin. Hakan yasa har Amaturrahim ma tabi sahun yan uwanta in ka ganta gurin Rahama to nono ne zata sha in ta ga dama.
Yau ma da mai adaidaita sahun su ya dawo dasu wanda ke dauko su in Baban su baya nan ya kawo su. Kamar ko yaushe bata nan don haka sun saba makota zasu shiga su amso makullin gida har ta da Amaturrahim ta bar ta don haka Amaturrahman ta amso ta suka tafi. Kitchen suka kai kwanukan su kana suka wuce daki. Da kyar Amatullahi ke abubuwa don tun safe take ciwon ciki ga Baffa baya nan. Da kyar tayi sallah ta kwanta yunwa na cin ta, Amaturrahman ce ta hado mata cereal da kyar ta sha sannan ta rufa barci mai nauhi ya dauke ta. Haka ita kam tayi ta jele da Amaturrahim har tayi barci kana tayi nata home work din ba zata iya yin na Amatullahi ba don haka ta bar shi. Kayan su ta saka cikin laundry basket ta dauko masu wanda zasu saka gobe.
Sai tara saura Rahama ta shigo gida lokacin sai Amaturrahman kawai tana dakon dawowar Sulaiman ta shaida masa ciwon Amatullahi amma Rahama ta shaida mata sai gobe zai dawo yana can FUD a Dutse yana wani aiki kuma yayi dare don haka sai washe gari tace
KAMU SEDANG MEMBACA
WADATA
AcakThe story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk Wanda Yayi hakuri bazai Taba tabewa ba, labarin A'isha da Suleiman masoyan gaske Wanda kaddara ta d...